Kungiyar nan mai fafutikar kafa kasar Biyafara da aka fi sani da IPOB. ta kaddamar da wani sabon gidan Rediyo mai watsa shirye shiryensa da Hausa.

Mai magana da yawun ‘yan kungiyar mai suna Emma Powerful ne ya bayar da anarwar kafa sashen Hausa na gidan rediyon.

Ya ce, a ranar 6 ga watan Janurun 2018 din nan ne sashen Hausa na gidan Rediyon zai soma aiki, akan mita 15110 a gajeran zango da mialin karfe 7 na yamma.

“A kokarinmu na cika alkawuran da muka daukarwa kawukanmu, mun samar da sashen Haua na gidan Rediyin IPOB domin isar da sakon neman ‘yancinda muke yi zuwa ga kowa da kowa”

“Gidan Rediyon ba wai za’a kama shi ne kawai a Najeriya ba, za’a iya kama tashar a dukkan fadi Afurka, duk inda masu jin Haua suke a nahiyar Afurka zasu iya kama domin suji bukatunmu”

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ne ya ruwaito wannan labari.

NAN