Wani dan sanda mai suna Bala Adamu a ranar talata ya kashe har lahira wani abokin aikinsa, Emmanueel Timothy, wanda yake aiki karkashin runduna ta musamman a karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.
A lokacin da yake tabbatar da faruwar wannan al’amari a gaban ‘yan jarida, Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Adamawa, Othman Abubakar, ya bayyana cewar, lamari ya auku ne, bayan wata gajeruwar takaddama ta shiga tsakanin ‘yan sandan biyu da misalin karfe 10:45 na safe, a caji ofis na Madagali.

 

“Mamamcin, Timothy mai mukamin Saja, wanda ya samu hora daga runduna ta 13 a Mukurdi na daga cikin wadan da aka turosu jihar Adamawa domin yin aiki na musamman” A cewar Othman Abubakar.
Otthman bai bayar da cikakken dalilin wannan hatsaniya da ta kaure tsakanin ‘yan sandan biyu ba, sai dai ya tabbatar da cewar dan sandan da yayi kisan Adamu tuni aka tsare shi a sashin masu manyan laifuka, inda yace tuni aka tura batun zuwa sashin bincike na rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

 

NAN