Categories
Kanun Labarai

‘Yan Boko Haram sun kashe ɗan sanda da ’yar gudun hijira

Daga Jaafar Jaafar

A wata fafatawa da aka yi tsakanin sojojin Nigeria masu yaƙi da ta’addaci a arewa maso gabashin ƙasar da ‘yan ƙungiyar Boko Haram, wani ɗan sanda da wata ‘yar gudun hijira sun rasa rayukansu.

Kakakin Runduna ta Bakwai K.M. Samuel ya ce ranar Juma’ar nan da misalin ƙarfe shida na yamma sojojin su ka yi wa maharan kwanton ɓauna yayin da su ke tsallaka ƙauyen Bocobs da ke ƙaramar hukumar Bama a Jihar Borno.

A cewarsa, nan take sojojin su ka fara yi musu luguden wuta har su ka kashe guda cikinsu kuma su ka raunata da dama.

Bayan sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addar, sojin sun ƙwato kekuna guda uku da jarkoki guda biyar da buhunan masara guda biyu.

Sai dai kuma a wannan rana da misalin ƙarfe bakwai na dare sojojin sun sake artabu da maharan yayin da su ka far ma wani ƙaramin sansanin soji a garin na Bama.

A wannan hari ne aka kashe dan sanda guda daya, kuma harsashi ya samu wata ‘yar gudun hijira ita ma ta mutu.

Kwamandan Birged ta 21 ya ziyarci filin dagar a yau, kuma daga bisani ya zarce a ka yi jana’zar ‘yar gudun hijirar da ta rasu.

Categories
Wasanni

Giroud ya ci ƙwallaye ɗari a Arsenal

Daga Abba Wada Gwale

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Arsenal, Olivier Giroud, ya zura ƙwallonsa ta ɗari a tarihin zamansa ƙungiyar bayan da ya zura ƙwallo ɗaya a wasan da Arsenal din ta lallasa Bate Borrisov da ci 4-2 a gasar Europa da su ka fafata a ranar Alhamis.

Giroud, ɗan shekara 30 wanda ya koma Arsenal daga ƙungiyar Montpellier ta ƙasar Faransa, ya bi sahun ɗan wasa Thiery Henry da Ian Wright da Cliff Bastin a sahun wadanda su ka zura ƙwallaye 100 a ƙungiyar.

Ɗan wasan wanda ɗan asalin ƙasar faransa ne, ya kusa barin Arsenal a kasuwar siye da siyarwa ta watan Agusta bayan da ƙungiyar ta siyo Alexandre Lacazatte shi ma daga ƙungiyar Lyon ta Faransa inda kungiyar Westham ta ingila ta yi zawarcin sa.

A wasan da Arsenal ta buga Theo Walcott ne ya zura ƙwallo biyu a raga.

Bisa ga dukkan alamu ƙungiyar farfado daga yanayin da ta shiga na rashin kataɓus, inda ta yi sa’ar doke Bate Boristov a wasan Europa.

Wasan da suka tashi 4-2, ranar Laraba, ya kasance na biyu da Arsenal ta ci a rukuninsu na takwas (Group H) na gasar kofin Turai ta Europa.

Walcott ya fara zura wallo a raga ne a minti na tara da shiga fili, sannan ya ƙara ta biyu a minti na 22.

Rob Holding ya ci wa Arsenal kwallonsa ta farko a minti na 25, wadda ta kasance ta uku ga kungiyar, kafin kuma Giroud shi ma ya ci tasa a minti na 49 da bugun fanareti, kwallon da ta kasance ta 100 da ya ci wa ƙungiyar.

Bate ta samu ƙwallayenta ne ta hannun Ivanic a minti na 28 da shiga fili, yayin da a minti na 67 Gordeychuk ya ci musu ta biyu.

Arsenal ce ƙungiya ta farko da ta doke Bate a gida a wata cikin gasar kofin Turai, tun bayan da Barcelona ta ci ta a wasan rukuni na kofin zakarun Turai a 2015- a wasa bakwai kenan.

Arsenal ce ta ɗaya yanzu a rukunin da maki shida, yayin da Red Star Belgrade ta ke zaman ta biyu da maki hudu, bayan da ta ci Cologne, wadda ta sha kashi a wasanninta biyu, da ɗaya mai ban haushi.

Categories
Siyasa

Zan cigaba da kasancewa sanata har karshen rayuwa ta, inji Bukar Abba

Tsohon Gwamnan jihar Yobe karo uku, kuma sanata mai wakilatar gabashin jihar a majalisar dattawa ta kasa, ya bayyana cewar, zai cigaba da zama a majalisar kasa a matsayin sanata har karshen rayuwarsa.

Tsohon Gwamnan wanda aka zabe shi a matsin sanata tun 2007, inda aka kuma sake zabarsa a shekarun 2011 da kuma 2015.

Alhaji Bukar Abba Ibrahim shi ne shugaban kwamatin kula da zaizayar kasa da sauyin yanayi na majalisar dattawa ta kasa.

Bugu da kari matarsa, Khadija Bukar an zabeta a matsayim ‘yar majalisar wakilai ta kasa har karo uku kafin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabe ta a matsayin karamar ministar harkokin kasashen waje a 2015.

Bai dai bayyana ko zuwa ga wa yayi wannan bayanin ba. Amma dai Gwamnan jihar Yobe me ci Ibrahim Geidam zai kammala wa’adinsa a shekarar 2019 yayin da ake ganin zai nemi kujerar dan majalisar dattawa, wadda suka fito mazaba daya da tsohon gwamna Bukar Abba Ibrahim.

Sanata Bukar Abba a bayyana hakan ne a yayim da yake zantawa da manema labarai a yayin da ake shirin bikin cikar Nigeria shekaru 57 d samun mulkin kai.

Me kuke ganin zai faru tsakanin tsohon gwamna Bukar Ibrahim da Gwamna Ibrahim Geidam a 2019?

Categories
Kanun Labarai

‘Yar gidan Gwamna Ganduje ta tubure sai ta auri wani Bayerabe

Daga Mustapha Usman

‘Yar gwamnan Kano Adbullahi Umar Ganduje, wato Fatima Ganduje, ta kafe tsayin daka sai ta auri dan gidan gwamnan Jihar Oyo mai suna Idris Abiola Ajimobi.

Fatima wacce ta gama karatun ta na digiri a Jami’ar ABTI da ke Yola, ta yi nisa cikin soyayya da wannan saurayi, duk da cewa auren bai gamsar da iyayenta ba.

A cewar wani makusancin gidan Gwamna Ganduje, “an sha kwace wayoyinta a tsare ta a gida, amma duk da haka sai ta san yanda ta yi su ka yi magana ko su ka hadu.”

Shaukin soyayyar wannan saurayi da budurwarsa ya fito fili karara, yayin da ta sanya hotonsa a shanfinta na Instagram (fateeganduje) a ranar 19 ga Satumbar wannan shekarar ta na nuna wa duniya cewa Idi fa kyautar ubangiji ne a gareta.

Shi ma kuma Idris ya sanya hoton bidiyonsa tare da Fatima suna zantawa.

Categories
Taska

Matar Tsohon Najadu Hefner Ba Za Ta Samu Tumunin Takaba Ba

Daga Mustapha Usman

Mashahurin tsohon nan Hugh Hefner wanda ya yi shuhura wajen yaɗa batsa bai barwa matar da za ta yi masa takaba ko taro ba.

Hefner ya mutu ranar Talata bayan shafe shekaru 91 a duniya, kuma da shafe fiye da shekaru 50 yana fasadi a doron kasa.

Duk da cewa sun yi zaman aure na kimanin shekaru biyar da matar tasa mai suna Crystal Harris kafin mutuwarsa, sai dai a cikin wasiyyar da ya bari ya ce kada a bata ko taro cikin makudan kudin da ya bari.

An ƙiyasta dukiyar da ya bari kimanin dalar Amurka miliyan 110 ce, sai dai wata majiyar kuma ta ce bai kai hakan ba.

A cikin wasiyyar da ya bari, dukiyar tasa za’a raba ta ne tsakanin ‘yayansa hudu da ya bari da Jami’ar Kudancin California da kuma fannin taimakawa mabuƙata. Ita kuwa Crystal ya ce kawai a kula da dawainiyarta.

Sai dai rahotanni sun yi nuni da cewa kafar walan da Hefner ya yi Crystal ramuwar gayya ce saboda wahalar da ta bashi kafin a yi auren.

Me nene ra’ayinku a kan wannan ƙafar wala da ya yi mata?

Categories
Siyasa

Buba Galadima ya caccaki gwamnatin Buhari

A tattaunawar da yayi da sashen Hausa na BBC, Injiniya Buba Galadima yace gwamnatin tasu ta APC da suka yi uwa suka yi makarbiya domin ganin kafuwarta, bata tsinanawa al’ummar Nigeria komai ba ya zuwa yanzu.

Galidima yace, sam bai gamsu da salon yadda ake tafiyar da gwamnatin Muhammadu Buhari ba. Sannan ya soki batun tsaro da yaki da rashawa. Ya kalubalanci jami’an tsaro cewar “ba zasu iya tuka daga Damaturu zuwa Damasak su kadai ba” yace sam batun da ake na tsaro rufar kura ne da fatar akuya.

Sannan Galadima, yace an yi watsi da wanda duk suka yi tallar Buhari tun farkon fitowarsa takara. Ya kara da cewa, “babu ko mutum daya da aka baiwa mukami a cikin mutanen da suka tallata Buhari tun farkon shigarsa al’amuran siyasa.

Da aka tambaye shi dangane da zaben 2019, Buba Galadima yace, ba zai ayyana wani mutum a matsayin wanda zai marawa baya a yanzu ba, a cewarsa akwai lokaci nan gaba da zai yi hakan. Da aka tambaye shi ko zai marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, yace indai ba a neme shi ba ba zai kai kansa ba. Ya kara da cewar, yafi karfin yaje a samu wani dan siyasa yace zai taimaka masa ko waye.

Me zaku ce kan wadannan bayanai na Buba Galadima da yayi a BBC?

Categories
Labarai

HAJJIN BANA: Jihar Kaduna ta kammala jigilar alhazanta zuwa gida

Daga Yasir Ramadan Gwale

A dazu ne jirgi ya sauka da rukuni na karshe na alhazan jihar kaduna a filin sauka da tashin jiragen saman kasa da kasa dake Kaduna, da alhazan jihar daga kasa mai tsarki, abinda ya kawo adadi na karshe da suka dawo gida Nigeria daga mahajjatan jihar da suka sauke farali a bana.

Babban jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da jin dadin alhazan jihar Kaduna Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana hakan ga manema labarai. Inda yace da misalin karfe 7:05am na safiyar alhamis jirgi na karshe ya sauka da rukunin karshe na alhazan jihar Kaduna, wanda jirgin Med-view ya yi jigilar wasu daga cikinsu.

Jirgin na karshe dai ya sauka ne da manya manyan jami’an hukumar aikin hajji ta jihar Kaduna da sauran manyan mutane da suka hidimtawa alhazan a kasa mai tsarki ciki har da Imam Hussaini Sulaiman Tsoho Ikara da sauran wadan da gwamnati ta wakilta domin aikin alhazai.

Jirage guda biyu ne Max Air da kuma Med-View suka yi jigilar Alhazan jihar Kaduna, jirgin Max ya kwashi kimanin mutane 2,173, yayinda Med-View ya yi jigilar mutane 4,542.

Rahotanni sun bayyana cewar kimanin mutane 6,713 ne suka sauke farali a kasa mai tsarki daga jihar Kaduna.

Jagoran Alhazan na jihar Kaduna yabawa gwamnatin jihar Kaduna a bisa gudunmawa da kuma dukkan kulawa da ta baiwa Alhazan jihar a cewar Imam Sulaiman Tsoho Ikara, karkashim jagorancin Sakataren Gwamnatin jihar Kaduna Alhaji Balarabe Abbas Lawal da dukkan sauran wadan da suka taimaka wajen yiwa alhazai hidima a kasa mai tsarki, a yayin aikin hajjin bana.

Categories
Taska

Mutumin da ya yi shuhura wajen yada batsa a duniya ya mutu

Shahararren Ba’amurken nan da ya yi fice a duniya wajen assasa zinace-zinace da yada batsa, wato Hugh Hefner, ya rasu.

Hefner, wanda shi ne mamallakin gidan kalankuwa na tsiraici wato Playboy Mansion, da kuma mujallar Playboy Magazine, ya rasu ya na da shekaru casa’in da daya.

Duk da cewar iyayensa mabiya darikar cocin Methodist ne, kuma su na da son addini, shi kam Hefner sai ya koyi saka a mugun zare.

Saboda tsabagen shakiyancin Hefner wato ko dan kamfai ba ya sawa, sai dai ko yaushe ka gan shi cikin kayan bacci.

Shi dai wannan dattijo, wanda ya cinye shekaru kimanin hamsin ya na wannan ta’annati, daga basani har kurumcewa ya yi saboda tsabagen shan dakan maza.

An haifi marigayin a ranar 9 ga watan Afrilun shekar 1926 ta Miladiyya.

Me za ku ce a kansa?

Categories
Bayani

BINCIKE: An bankado almundahana a sashen ilimi na kananan hukumin jihar Kano

Daga Yasir Ramadan Gwale

Hukumar karbar koke-koken danne hakki da yaki da almundahana da zambar kudade ta jihar Kano ta bankado wata almundahana da zambar kudade da ta shafi wasu daga cikin kananan hukumomin jihar Kano tare da hadin bakin wasu daga cikin shugabannin makarantun primary dake jihar Kano.

Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji ne ya bayyana haka, a lokacin da yake karbar rahoton binciken daga daraktan hukumar da ya jagkranci wannan bincike SA Gusau. Magaji ya bayyana cewa, laifukan da suka bankado sun sabawa dokokin da suka kafa hukumar a shekarar 2008.

Muhuyi magaji ya kara da cewar, hukumarsa ta kwato sama da Naira Miliyan 21 daga hannun wadan da ake zargi da yin almundahanar. A cewarsa wasu daga cikin mutanan da ake zargi sun baiwa hukumar hadinkai wajen gudanar da binciken don gurfanar da wadan da ake zargi da laifukan zambar kudaden.

A wani bayani kuma, da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Maimuna Saidu Bello ta sanyawa hannu, ya bayyana cewar tun kusan a shekarar bara ne, hukumar ta kaddamar da gudanar da binciken akan irin bayanan sirrin da suke samu kan badakalar da ake tafkawa a sashen ilimi na kananan hukumomin jihar Kano. Ta kara da cewar, hukumar ta yi bincike akan mutane sama da 50 wadan da ake zargi suna da hannu dumu dumu cikin almundahanar.

Categories
Kanun Labarai

Tambuwal ya gargadi ‘yan Shia kan yin zanga zanga a Sokoto

Gwamnatin jihar Sokoto a ranar laraba tayi gargadi ga ‘yan Shiah a jihar akan cewar ba zata lamunci duk wata zanga zanga a jiyar da sunan juyayi a Sokoto.

Kwamishinan Shariah na jihar kuma antoni janar, Sulaiman Usman, shi ya bayar da wannan gargadi a madadin gwamnatin jihar Sokoto a lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan wani zama na musamman kan batun tsaro a jihar.

Kwamishinan yace, wasu bayanan sirri da gwamnati da jami’an tsaro suka samu ya nuna ‘yan Shiah a jihar na nan na shirin yin wata zanga zanga da sunan wani juyayi wadda zata iya kawo yamutsi a jihar.

“Akwai bayanai da suke nuna wasu aikace aikacen ‘yan Shiah a jihar ba abinda zasu kawo sai zaman dar-dar da rikici.”

“A saboda haka, idan ba a yi hattara ba, zaman lafiyar da ake amfana da shi a jihar, na iya samun tasgaro idan aka zubawa ‘yan Shiah ido zasu lalata shirin zaman lafiya a jihar” a cewar antoni janar kuma kwamishinan Shariah a jihar ta Sokoto.

Ya kara da cewa, “muna masu haramta dukkan wani shiri na yin zanga zanga a ko ina a fadin jihar Sokoto, don haka duk wanda ya karya wannan doka kada ya zargi kowa ya zagi kansa”

A dan haka ana gargadin ‘yan Shiah da su kiyaye dokokin da hukumomin gwamnati suka gindaya domin samun dorewar zaman lafiya a jihar.

A dan haka, ina amfani da wannan dama a madadin gwamnatin Sokoto nayi kira ga al’umma da musamman ‘yan Shia su kiyaye bin doka da oda. A cewar Sulaiman Usman.

A nasa jawabin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Mohammed Abdulkadir yace a shirye hukumomin tsaro suke a dukkan fadin jihar domin ganin an kiyaye dokokin da gwamnatin jihar ta gindaya.

A sabida haka, kwamishinan ‘yan sanda na kira ga ‘yan Shia su kasance masu bin doka da oda don kaucewa fishin jami’an tsaro a jihar. A cewarsa, jami’ansa a shirye suke don bada kariya ga zaman lafiyar jihar.

Kamfanin dillancin labaru na kasa NAN ya ruwaito cewar an zauna domin tattaunawa a jihar, wanda bangarorin jami’an tsaro suka halarta da syka hada da ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya na SSS da NSCDC da kuma jami’an hukumar gidan yarin jihar.