Categories
Taska

Yadda wani maigadi a kwalejin ‘yan mata ke karbar cin hanci don fitar da dalibai zuwa lalata da maza

 Daga Habu Dan Sarki
Wani binciken kwakwaf da jaridar TheCable ta gudanar ya bankado yadda wani maigadi a Kwalejin Tarayya ta ‘Yan Mata (FGGC) dake garin Langtang a jihar Filato yake karbar cin hancin naira dubu 5 domin kulla alakar lalata tsakanin dalibai mata da ke karatu a kwalejin, don su je su kwana da maza a waje.
Wannan maigadi da rahotanni suka nuna cewa, a baya yana aiki ne bangaren dafa abinci amma aka canza masa wajen aiki zuwa bakin kofar shiga makarantar bayan an kama shi da laifin yi wa wata daliba ciki, ya shiga wannan harka ne sakamakon alakar da ke tsakanin sa da wasu ‘yan mata a makarantar, inda yake karbar cin hanci da bai wa daliban kudin mota zuwa inda ake jiransu.
Binciken ya gano cewa ban da wannan maigadi da ke hada baki da bakin maza a waje yana fitar da ‘yan mata, akwai kuma wasu malamai a makarantar wadanda su ma ake zargi da amfani da ‘yam matan ta hanyar da ba ta dace ba.
Dan jaridar TheCable da ya gudanar da wannan bincike ya ji ta bakin wasu daliban makarantar da suka koka da irin halayyar banza da wasu malamai da aka sakaya sunayen su, suke  nuna musu, musamman idan sun shiga ofisoshin su ki kuma sun aike su gidajensu.
Binciken ya gano makarantar  ta FGGC Langtang na fama da matsaloli na rashin katanga mai tsayi da za ta kebe daliban daga dakunan kwanan su, da samar da kyakkyawan tsaro, ta yadda za a kare kimar wannan makaranta da mutuncin wadannan ‘yan mata.
Kokarin da aka yi na ankarar da mahukunta a makarantar da hukumomin ma’aikatar ilimi ta tarayya ya ci tura, yayin da suka nemi a aika musu da koke a rubuce dauke da hujjoji  gamsassu game da abubuwan da ake zargi.
Menene ra’ayin ku game da muhimmancin samar da tsaro a makarantun kwana da daukar mutane nagari aiki, don kula da amanar yaran da ake tura wa karatu nesa da iyayensu.
Categories
Kanun Labarai

Shugaba Buhari ya yi nadamar rashin yin wasu naɗe naɗe a hukumomin Gwamnati

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana nadamarsa kan rashin yin wasu muhimman naɗe naɗe a wasu hukumomin Gwamnati. Shugaban yayi wannan nadamar ne a ranar Talata, ya kuma sha alwashin cike duk wani giɓi a hukumomin Gwamnati nan da ɗan lokaci ƙanƙani.

Shugaban ya bayyana haka ne, a babban taron masu ruwa da tsaki da kuma shugabannin zartarwa na jam’iyyar APC da aka gudnar a fadar Gwamnati dake Abuja.

Shugaban a cikin jawabinsa ya tabo batutuwa da dama da suka shafi tafiyar Gwamnatinsa da kuma irin yadda mutane ke korafe korafe kan salon shugabancinsa, na rashin yin abubuwa da yawa cikin gaggawa.

Daga ciki ya fada cewar, “A shekarar da ta gabata, na shaida muku cewar, zamu yi naɗe naɗe a wasu hukumomin gwamnati da bamu yi ba tunda muka zo, sai dai kai gashi har yau bamu yi ba, sabida wasu dalilai, a wannan gabar, nake bayyanar muku da nadamata kan rashin yin wadancan naɗe naɗe na hukumomin Gwamnati”

“Wannan kuma ya faru ne, sakamakon sakaci da aka samu na kwamitin da na kafa wanda zasu duba wadan da suka dace dazamu naɗa a hukumomi daban daban, domin tafiya tare ba tare da nuna fifiko ga wani bangare ba”

“Ina sane da cewar, magoya bayanmu sun zaƙu da wadannan nade nade da suke jiran mu aiwatar da su,a sabida haka, ina mai tabbatar musu da cewar, zamu yi wadannan naɗe naɗe ba da jimawa ba, musamman yanzu da tattalin arziki ya farfado, muna da isassun kudade a hannu”

Sannan kuma, shugaban yayi godiya ga shugabannin jam’iyyar Musamman Cif John-Odigie Oyegun, da kuma jagoran jam’iyyar na kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu, sannan kuma, shugaban yayi godiya ga majalisun dokoki na kasaa, musamman shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Doga akan irin gudunmawar da suke bashi.

Haka kuma, shugaban ya yi godiya ga dukkan ;ya ‘yan jam’iyyar ta APC bisa irin gudunmawar da suke baiwa jam’iyyar da kuma irin yadda suke baiwa jam’iyyar goyon baya.

 

 

Categories
Tarihi

Tarihi da baiwar Sarkin Zazzau Alu Ɗan Sidi (1903-1920)

Daga Dandalin Tarihin Magabata

Sarkin Zazzau Aliyu Dan Sidi shahararren basarake ne a Arewacin Najeriya. Ya yi fice saboda irin fasaharsa da illiminsa, kuma shine sarkin Zazzau na farko da Turawa suka nada.

Turawanne kuma suka sauke shi, bayan sun samu sabanin ra’ayi akan wasu sauye-sauyen zamani. Ya zama sarki yana da shekaru 64. Ya yi sarautar Zazzau daga shekarar 1903 zuwa 1920.

Jikan Sarkin Zazzau Musa ne, Bamalli. Wani abin sha’awa game da da tarihinsa shi ne, shi dai bai taso a gidan Sarautar Zazzau ba, ya taso a gidan malanta ne, a hannun malaminsa Limamin Durum wato Malam Abubakar.

Ya taba samun sabani da Sarkin Zazzau Kwasau (Mai kogin Jini dan Sambo), wanda hakan ya sanya ya bar Kasar Zazzau, ya shiga yawace-yawace, inda har ya zauna a kasar Kwantagora a zamanin Sarkin Kwantagora Ibrahim Nagwamatse.

Ya wallafa wakoki da dama, cikinsu kuwa akwai Tabarkoko, Saudul Kulubi, Wakar Diga da kuma wakar Birnin Kano.

An ce wakar Birnin Kano ya yita ne, yayin wata dabar bankwana da sarakunan Arewacin Najeriya su ka shiryawa Gwamna Arewacin na Zamanin Turawa wato Sir Hugh Clifford, a Birnin na Kano a cikin shekara 1914. A zamaninsa akan masa kirari da “Aliyu na Awwa mai iya Sarki”.

Sarkin Zazzau Aliyu dan Sidi Batijjane ne na kwarai, kuma ya yiwa shehin Darikar ta Tijjaniya wato Shehu Ahmadu Tijjani waka.

Wakar Birnin Kano ta Malam Alu dan Sidi

Muna gode Allah da yayi nufi

Yasa muka taru a kofar Kano

Muna yin Salati bisa ga Muhammad

Dalilinsa anka yi mu akayi Kano

Mu kara salati bisa ga sahabbai

Mu sami dalilinsu komi anu

Zama hali ma nahnu shi muka zance

Da niy yi shiri zani birnin Kano

Diya min Muharram ga ran Lahadi

Na hau bisa jirgi zuwa na Kano

Ga Chalawa ni kwana guda muka tashi

Muna gaisuwa da dawakan Kano

Dawaki na baki kaza yan gari

Fa har muka sadu da Sarkin Kano

Da fa muka gaisa ya juya na bishi

Dada har ya kaini masauki Kano

Ina gaida masu zuwa daga nesa

Da shaihu na Kukawa ga shi Kano

Da Mahoni Laraba Gaidan Kano

Kaza Lamido Adamawa a birnin Kano

Katagum, Hadejia, kaza duk da Gombe

Misau Jama’are a birnin Kano

Da Zazzau da Bauchi, kaza Katsina

Da Daura, Gumel gasu birnin Kano

Kazaure da kau Sakkwato har da Gwandu

Kabawa da Argungu birnin Kano

Mutan Gwadabawa da Kwanni da Yabo

Gamuwa da Anka a birnin Kano

Da Meri da Augi mutanen Yamma

Mutan Jega ga su a birnin Kano

Mutan Wukari, mutanen Ibi

Da Loko da Lokoja a birnin Kano

Da Yawuri har Kwantagora Rijau

Mutan Wushishi da Bussa a Birnin Kano

Kushurki da Kunguna har Kuriga

da Gwari na Waki a taron Kano

Mutanen Maginga mtan Kanbuwa

Na Sulame gasu a birnin Kano

Illori, Nufawa, Lafai, Agaye

Fa hatta Abuja a birnin Kano

Fa har Tunkiya gata ga Damisa

Mashayansu dai sunyi kiwo Kano

Kutawa mutanen Kafi, Lafiya

Da jam’an ta Baroro a birnin Kano

Da Mahmudu Ningi da Sarkin Bura

Da Sarkin na Bassa a birnin Kano

Ina gaida Sarkin Kano Yayi Aiki

da anka yi taro garinsa Kano

Gidaje na sabka dada har liyafa

Da taryan sarakai su sabka Kano

Da sabkan farare da sabkan bakake

da birni da kauye a birnin Kano

dalili gareni in san yayi aiki

Zama nayi ko da nika je Kano

Da shi da ya sabkar da su masu sabka

Ta’ala shi bamu sawaba Kano

Fa naje da yare iri da yawa

Da busa da ganga a taron Kano

Fitawa da doki dako Feluwa

Da sayi suna sukuwa nan Kano

Mutane da doki da niz zo dasu

jimillansu hamsa zuwana Kano

Kurama, Katab har da Cawai duka

Fa duk sunyi wasa a taron Kano

Da Jaba da Gwari mutan Rumaya

Kadara fa na kai su taron Kano

Ga babban suka na dawakan saraki

Na Zazzau fa sun ka ci taron Kano

Da anka yi wasa fage ya hadu

Muhudanmu sun yi ado nan Kano

Ka rarra, ka Kabra, ku san tumkiya

Bata iya kabra ba Kano

Da tauri da tsauri idan anka goga

Guda sai shi yanke guda a Kano

Ba’an gwada karfe ba, sai inda karfe

Duwatsu fashewa su kai a Kano

Ka zaga Kano har kasan dan Kano

Na birnin Kano wanda yasan Kano

Ka kau tambaye shi tsakani da Allah

Ya bayyana maka taron Kano

Na yawata Kano gani ga dan Kano

Dada har nasan anguwa a Kano

akwai anguwan madawkin Kano

Da sunanta Yola a birnin Kano

Daneji, da Soron dinki akwai su

akwai Lungunawa da Sheshe Kano

Da Marmara duk unguwa ce duka

da Kunduke Kwankwaso duk a Kano

Akwai Wudilawa akwai Na’ibawa

Da Ibadi Fasa-keya a birnin Kano.

Caranci, Gudundi, akkwai Jarkasa

Makankari, Garko duk a Kano

Kusura, Kudancin Kano da Wazirci

Da Siradi akwai ta Kano

Karofi na Wanka da Shuni akwaisu

Madatai da Daushi akwai su Kano

Karofi na Sudawa, Zangon Ciki

Da Dandago, Diso akwai su Kano

Akwai unguwar Durunmin Kaigama

Da Bulbulas, Guntu akwai su Kano

Da Yalwa da Dala, Madaboo duka

Suna nan Arewa da Kurmin Kano

Akwai wata ko unguwa Masaka

Da Sarari da Sagagi Birnin Kano

Awai unguwa Waitaka a Kano

Akwai Durumin Dakata min Kano

Mahanga, Kutumbawa duk unguwa ce

Da Damtsenka Tsage a Birnin Kano

Akwai Cediya ta Kuda unguwa ce

Akwai Kalaman Dusu duk a Kano

Da Lallokin Lemu, da kau Makwarari

Makwalla fa duk unguwa ce Kano

Dabinon Awansu da Mandawari

Da Alfindiki Kwalwa duk a Kano

Tsaya in gajarta guda don kau yawaita

In kawo wurinta da niyyi Kano

Fa har muka kare naje Nasarawa

Garin makarantan su Sambon Kano

Akwai makaranta karatun Bature

Acan Nasarawa ta kofar Kano

akwai yara masu Karatu na allo

Akwai masallaci ginanne Kano

AKwai Makaranta ta al Kur’ani

Da litattafanmu a birnin Kano

Akwai wani dakin zaman masu ciwo

Akwai matsarinsu a kofan Kano

Masaka, madunka, da mai Sassaka

Gidansu guda makarantan Kano

Makera, Badukai da masu kudi

Cikin makaranta ta kofar Kano

Cikin shekara goma sha dai ga daula

Aliyu binu Sidi zuwanshi Kano

Ya wake ta yan baya domin su ji

Su san wakacin tafiyanshi Kano.

 

Allah Ya Gafarta Masa

Categories
Duniyan Labarai Wasanni

ISIS na barazana ga Messi da Neymar

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Kungiyar ISIS tayiwa yan wasan kwallon kafa guda biyu barazana da rayuwarsu sakamakon wani hoton yan wasan data wallafa a shafin twitter.

An bayyana hoton ne wanda aka nuna dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Neymar yana kuka a zaune an daure hannayensa sannan kuma ga mayakan qungiyar ta ISIS  gaban har ila yau kuma ga tutar kungiyar a bayansa.

Wata kungiya wadda take goyon bayan ISIS dince ta wallafa hoton a shafin na twitter sannan aka turashi zuwa wani sashin wallafa labarai na kasar Iran mai suna YJC sannan akayi rubutu kamar haka “Hoton kumgiya ISIS  na maraba da fasar cin kofin duniya a kasar Russia, bayan Messi yanzu kuma sai Neymar”.

Barazanar dai da kungiyar ta ISIS takeyi yana saka shakku akan magoya bayan kwallon wadanda zasuje kallon wasan cin kofin duniya da za’ayi a jihohi 11 na kasar Russia.

Wannan hoto na Neymar yazo kwanaki kadan bayan kungiyar ta wallafa hoton Messi yana kuka agaban mayakan kungiyar.

A kwanakin baya ma kungiyar ta saka hoton mai koyar da tawagar yan wasan kasar faransa Didier Deschamp wanda shima suka saka hotonsa suna masa barazanar zasu kasha shi.

Categories
Kanun Labarai

PDP bata gamsu da matakin Gwamnati na korar Babachir da Oke kaɗai ba

Jam’iyyar PDP mai hamayya, ta bayyana rashin gamsuwarta da matakin da Gwamnatin Buhari ta dauka na korar su Babachir da Oke daga aiki ba tare da bayyanawa al’ummar Najeriya rahoton kwamitin binciken da ta kafa a kansu ba. Jam’iyyar ta bayyana cewar, wannan dodo rido ne ake yiwa ‘yan najeriya game da wannan batu.

PDP ta bayyana hakan ne ta bakin kakakin kwamitin riko na jam’iyyar karkashin jagorancin Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, wata Yarima Dayo Adeyeye, a ranar litinin a harabar sakatariyar jam’iyyar dake babban birnin tarayya Abuja.

Idan ba’a manta ba, a litinin dinnane Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayar da sanarwar korar dakataccen sakataren Gwamnatin tarayya Babachir David Lawal daga aaiki tare da shugaban hukumar NIA Ayo Oke.

PDP ta bayyana cewar, korarsu ba tare da bayyana ainihin rahoton kwamitin da Shugaban ƙasa ya kafa karkashin jagorancin mataimakinsa Yemi Osibanjo ba, kamar shiga ɗaka da kare ne. Kuma wannan ba abin yadda bane.

‘Yan Najeriya sun jima suna dakon irin matakin da Shugaban kasa zai ɗauka kan wannan badakala da ta shafi manya manyan makusantansa ta fuskar aiki.

“Sam sam bamu yarda da wannan mataki da shugaban kasa ya dauka a dukunkune ba, tilas a fito a yiwa ‘yan Najeriya bayanin, kuma a bar shariah tayi aikinta akan mutanan da aka kama da laifi, ba wai kawai a sallame su ayi shiru ba”.

“dan haka, tilas a tura wadannan mutane zuwa gaban hukumar EFCC domin cigaba da bincikarsu, tunda Shugaban kasa yaki bayyanawa al’umma asalin llaifin da aka same su da shi”.

Rahoton kwamitin Yemi Osibanjo ya kamata ya zama a bayyane, ‘yan najeriya su gani su karanta, dan su san ainihin laifin da mutanan da aka kora suka yi.

PDP ta ci gaba da cewar, Gwamnati karkashin jam’iyyar APC na yin rufa rufa kan batun cin hanci da rashawa a Najeriya, musamman abinda ya shafi wasu manya daga cikin Gwamnatin.

Sun ce, tilas ne hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su binciki Babachir da Oke dan sanin hakikanin laifin da suka aikta, sannan su fuskanci kuliya.

Wannan babban laifi ne da ake zargin wadannan mutane da aikatawa, ba wai kawai korarsu Shugaban kasa zai yi yayi shiru ba, tilas ayi bayani, dan ba zamu zauna, muna tafawa shugaban kasa a irin wannan dukunkune da yayi ba.

Mun gamsu da tsarin demokaradiyya da kuma kundin tsarin mulki da ya baiwa kowanne dan kasa dama, sannan babu wani batun boye boye da za’a yiwa al’ummar Najeriya ba.

Wannan sam ba adalci bane, su Babachir da Ayo a kore su kawai ba tare da daukar wani mataki akansu, bayan kuma sauran mutane Gwamnati na mika su wajen hukumomin bincike dan gurfanar da su gaban shariah.

Kamfanin dillancin Labarai na Najeriya ne ya ruwaito wannan rahoto. Ko me zaku ce akansa?

Categories
Labarai

Gwamnatin Najeriya zata biya Inyamurai diyyar Naira biliyan 88 sabida yaƙin basasa

Gwamnatin Najeriya, ta amince ta biya diyyar Naira biliyan 88 ga mutanan da suka jikkata sanadiyar yakin basasar da aka gwabza a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Wannan biyan diyyar ya zo ne, bayan da kotun yankin kasashen Afurka ta yaamma, tayi hukunci cewar, laifin Gwamnatin Najeriya da ta kasa cire abubuwa masu fashe da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, daga burbushin makaman yakin basasa.

hakan ya biyo bayan, gamsuwar da bangarorin biyu sukaai na sasantawa a wajen kotu, don kawo karshen wannan shariah.

Ita dai wannan shar’ah ana yinta ne, sakamakon ƙarar da wani Vincent Agu da wasu mutum 19 suka shigar suna ƙalubalantar Gwamnatin Najeriya a shekarar 2012,kan sakacinta na ƙin ciccire irin ragowar abubuwa masu fashewa tun bayan kammala yakin basasa a shekarar 1970.

Mashu shigar da ƙarar sunce ragowar abubuwan da aka bubbune a ƙasa, sunyi hasarar rayukan al’ummarsu da basu san hawa ba, basu san sauka ba.

Baya ga haka kuma, ragowar irin baraguzan makaman yaƙin basasa ya sanya, tilas suka hakura da gonakinsu, sabida gudun tona wani abu da zai iya fashewa.

A yayin da yake gabatar da hukunci alƙalin kotun, Friday Nwoke a ranar litinin, ya bayyana cewar, za’a baiwa jihohi 11 da yakin basasa ya shafesu a yankin kudu maso gabas da maso yamma, da kuma wani sashe na yankin tsakiyar Najeriya naira biliyan 50.

Ana sa ran za’a biya wadannan kudi naira biliyan 50 ta asusun bankin gamayya Afurka (UBA) a asusun ajiya mai lamba 1018230076 mallakin wani wanda aka amince ya karbi kudin a madadin wadan da suka jikkata a yakin basasa mai suna, Noel Chukwukadibia.

Sauran naira biliyan 38 kuma za’a yi amfani da su wajen, kwashe tare da ciccire sauran makaman da aka bubbune a kasa tun zamanin yakin basasa a yankunan da abin ya shafa. haka kuma, za’a biya wadannan kudade ta hannun kamfani mai suna “Deminers Concept Nigeria Limite”, wanda alhakin ciccire wadannan abubuwa ya rataya a wuyansa.

Bayan haka kuma, Gwamnatin tarayya zata kafa cibiyar kula da kayayyakin da aka tono a garin Owerri na jihar Imo, da kuma lura da wadan da suka kamu da larurua a sakamakon fashewar wadannan ragowar makaman yakin basasa.

Ana kaddara cewar mutum 685 ne suka rayu bayan da hadin fashewar makaman ya rutsa da su, wannan kumaya faru ne, sakamakon binciken da aka sanya kwararru suka yi domin binciko ainihin wadan da suka samu raunuka yayin fashewar wadannan makamai.

 

 

Categories
Labarai

Hukumar ‘yan sanda ta ƙasa ta tabbatar da garƙame ɗansandan da ya yiwa maryam fyaɗe

Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta tabbatar da cafke tare da gaskame dansandan da ya yiwa Maryam fyade, wata karamar yarinya ‘yar asalin jihar kano a jihar Delta. “yan sanda a jihar Anambara sun tabbatar d kame Barau Garba, dan sandan da ya yiwa maryan ‘yar shekaru 24 fyade.

Kwamashinan ‘yan sandan jihar Garba Umar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Awka a ranar Litinin. A cewarsa, dan sandan da ake zargi, ya yi garkuwa da yarinyar ne a unguwar Hausawa dake garin Asaba, inda ya ajiye ta a wani daki ya dinga tarawa da ita a okporo dake birnin anica.

Ya kara da cewar, dan sandan dai yana tare da rundunar tsaro da zasu yi aiki a yankin Sakkwato, kafin daga bisani a maido da shi jihar Anambara domin yin wani aiki na musamman.

Yanzu haka dai wannan shu’umin dan sanda yana tsare a hannun rundunar ‘yanda , domin fuskantar tuhumce tuhumce kan wannan batu da ya dauki hankalin mutane da yawa.

“Dan sandan dai ya tabbatar da cewar, ya gamu da yarinyar ne a hanyar Asaba inda ta kidime sakamon zubar da kudin da aka aike ta su da tayi. A lokacin dan sandan yayi amfani da damarsa, wajen jan hankalin yarinyar har ya kawar mata da budurcinta”.

“Muna tabbatar da da al’umma cewar, wannan dan sanda zai uskanci hukunci da zarar hukumomi sun kammala bincike za’a mika shi gaba kuliya don ya fuskanci hukuncin abinda ya aikata”.

Kwamashinan ‘yan sandan ya tabbatar da cewar, zasu yi dukkan mai yuwuwa wajen ganin anyi adalci kan wannan batu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ne ya ruwaito wannan labari.

Categories
Labarai

Waye Boss Mustapha da Buhari ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya?

Boss Gida Mustapha, shi ne mutumin da aka bayar da sanarwar naɗa shi a mukamin sabon sakataren Gwamnatin tarayya, bayan da aka bayar da sanarwar sallamar Babachir David Lawal daga aiki.

Shi dai mutumin da aka naɗa a matsayin sabon sakataren gwamnatin, kwararren lauya ne, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa.

Boss Gida Mustapha, ya taba rike mukamin mataimakin shugaban rusasshiyar jam’iyyar ACN, daya daga cikin jam’iyyun haɗakar da suka narke suka koma APC.

Kafin dai a bayar da sanarwar naɗa Babachir a matsayin sakataren Gwamnati tun farko wasu da dama sun yi tsammanin za’a naɗa Gida Mustapha ne tun farko, amma sai abin ya zzo da bazata.

Kafin naɗa Gida Mustapha a wannan sabon mukamin nasa, shi ne, Manajan daraktan hukumar NIWA mai lura da hanyoyin ruwa da na tsandauri na Najeriya.

Waye Boss Gida Mustapha?

An haifeshi a jihar Adamawa, ya halarci makarantar sakandire ta garin Hong dake jihar Adamawa, inda daga nan ya wuce zuwa makarantar share fagen shiga jam’ah ta yankin Arewa maso gabas dake garin Maiduguri, a jihar Borno a shekarar 1976.

Daga nan ya wuce zuwa jami’ar Ahamadu bello dake Zaria, inda ya samu takardar shaidar kammala digirin farko a fannin Lauya a shekarar 1979, inda ya shiga makarantar horon lauyoyi ta kasa a shekarar 1980.

daga shekarar 1980 zuwa 1981 Gida Mustapha yayi hidimar kasa, sannan daga bisani ya kama aiki da kamfanin “Sotesa Nigeria Limited”, wani kamfanin kwararruna turawan Italiya, a matsayin babban darakta mai lura da ayyukan gudanarwa na kamfanin, ya bar aiki da kamfanin a shekarar 1983, inda ya fara aiki da wata cibiyar Lauyoyi mai suna Messrs Onagoruwa a birnin Legas.

Daga nan kuma Boss Gida Mustapha yayi aiki da hukumomi da dama, ciki kuwa har da hukumar PTF wadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba shugabantar ta. Daga nan kuma, yana daga cikin mutanen da suka nuna hazaka lokacin da ya rike mukamin akawu a kungiyar Lauyoyi ta kasa reshen jihar Adamawa.

Daga bisani, kuma ya shiga cikin al’amuran siyasa, inda har ya zama mataimakin shugaban rusasshiyar jam’iyyar ACN ta kasa. Wadda ta rushe don kafa jam’iyyar APC mai mulki, ya kasance mamba a kwamtin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a shekarar 2015.

bugu da kari kuma, yana daya daga cikin ‘yan kwamitin mika ragamar mulki daga PDP zuwa hannun jam’iyyar APC wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada su. Baya ga haka kuma, yana daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na jam’iyyar APC.

Boss Gida Mustapha Allah ya albarkace shi da iyali da ‘ya ‘ya, mutum ne mai san wasan kwallon lambu, da son tafiye tafiye musamman a cikin ruwa, da kuma son mu’amala da mutane.

Categories
Kanun Labarai

TA FARU TA ƘARE: Buhari ya sallami Babachir daga aiki

A yau litinin, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar da sanarwa korar dakataccen Sakataren Gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal daga aikinsa. Shugaban ya bayar da sanarwar sallamar Babachir din ne tare da shugaban hukumar NIA, Ayo Oke.

Wannan kora da aka yi musu, ta biyo bayan wani zargin zambar kudade da aka yi musu, inda har takai shugaban kasa ya kafa wani kwamiti karkashin jagorancinmataimakinsa, Yemi Osibanji, domin bincikar lamarin.

A ranar 23 ga watan Agustan da ya gabataa ne, Mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo ya mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari rahoton aikin kwamitinsa, inda aka samu Babachir da laifin sama da fadi da kudaden yankan ciyawa a sansanin ‘yan gudun hijira dake jihar Borno.

Tuni dai mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adeshina, ya bayar da sanarwar nada sabon sakataren gwamnatin tarayya, inda aka bayyana sunan Boss Mustapha daga jihar Adamawa a matsayin sabon sakataren Gwamnatin tarayya.

Zamu zo muku da cikakken bayani nan gaba…

Categories
Wasanni

Gambo Muhammad ya bar Kano Pillars

Daga Abba ibrahim Wada Gwale

 

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Gambo Muhammad, ya bar ƙungiyar ta Kano Pillars zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Rivers United da ke garin Fatakwal.

Shekarar Gambo goma a Kano Pillars kuma ya taimakawa ƙungiyar ta lashe kofin Firimiya na ƙasa sau hudu sannan ƙungiyar ta je wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Africa.

“Nabar Kano Pillars bayan sama da shekaru goma da na yi a ƙungiyar kuma nabar kulob din ne saboda yanzu baya buƙatar wasa na kamar yadda suka sanar dani,” inji Gambo.

Dan wasan dai ya koma Kano Pillars ne daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Buffalo shekaru goma da suka gabata.

Ya ci gaba da cewa: “Kano garina ne, anan aka haifeni na girma kuma zanyi kewar magoya baya da kuma ƙungiyar da na zama kyaftin dinta shekaru biyu da suka gabata.”

Gambo ya ce abin farinciki ne bugawa Kano Pillars wasa kuma ya kasance wanda yafi kowanne dan wasa zura ƙwallo a tarihin ƙungiyar.

Sannan ya ce ya samu gayyata daga ƙungiyoyi daban daban ciki da wajen ƙasar nan amma abu mafi sauki shine komawa Rivers United domin ita ce zaɓinsa duk da cewa zai sha wahala komawa Jihar Rivers da zama, amma haka zai zauna kuma zai saba da yanayin garin.

Ya ƙara da cewa “Da hawaye a cikin idanuwana ina yiwa kowa a ƙungiyar fatan alheri da magoya baya da mutanen Jihar Kano gaba daya.”

Gambo Muhammad dai ya wakilci yan wasan Najeriya a kofin Confederation wanda akayi a ƙasar Brazil a shekara ta 2013, kuma ya buga wasan da Najeriya ta sha kashi a hannun ƙasar Sifaaniya da ci uku babu ko daya.