Categories
Kanun Labarai

Atiku Abubakar ne kaɗai zai iya cin galaba kan Buhari a zaɓen 2019 – Abbati Bako

An bayyana tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da ya yiwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP kome, cewar shi ne kadai mutumin da zai iya samun galaba kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari idan aka shiga zaben 2019.

“Gazawar wannan Gwamnatin ta Shugaba Buhari wajen cika alkawuran da ta daukarwa ‘yan Najeriya, ya sanya mutane da yawa suka dawo daga rakiyar ta. Dan haka, wannan ne ke kara tabbatar da damar da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar yake da ita ta samun nasara”

“Idan Atiku ABubakar ya tsaya yayi shiri sosai akan wannan zaben, ba ni da wata shakkar cewar zai kayar da Shugaba Buhari a zaben 2019 dake tafe. Babu wani mutum a PDP da zai iya karawa da Buhari kuma yayi nasara in ba Atiku Abubakar ba” Inji Abbati Bako.

Abbati Bako, ya kara da cewar, irin wannan yunkuri da mutane irinsu Atiku Abubakar suke yi na kalubalantar jam’iyya mai mulki a zaben 2019,shi ne zai sanya su farga domin su an cewar Annabi ya faku.

Da yake maida jawabi kan kalaman Gwamnan jihar kaduna, Malam Nasiru el-Rufai, Abbati Bako ya bayyana cewar abinda gwamnan yayi mummunar katobara ce da bai kamata mutum irinsa yayi ba.

“Ba zai taba yuwuwa ba, ka kalli mutum kamar Atiku Abubakar kace ya tafi Allah ya raka taki gona. Abin kaico ne Gwamna ya bayyana hakan. Siyasa batu ne na tattaunawa da sahalewa juna, a lokacin da aka tattauna, aka barwa Atiku Abubakar, a wannan lokacin kuma su el-Rufai zasu ji bakar kunya sosai”

Abbati Bako kwararren dan sisaya ne, da yake fashin bakin kan siyasar najeriya da ma sauran duniya baki daya.

 

Categories
Labarai

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin dawo da ‘yan Najeriya gida daga Libiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin mayar da dukkan ‘yan najeriya da suke a kasar Libiya da ma sauran ‘yan Najeriya dake halin galabaita a kasashen duniya.

Shugaban ya bayar da umarnin ne daga birnin Abidjan na kasar Kwadebuwa, a wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa ya fitar a ranar laraba.

Shugaba Buhari ya yi jawabin ne a lokacin da yake tattaunawa da kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasar ta Kwadebuwa, a babban birnin wato Abidjan, inda yake halartar wani muhimmin taro.

Shugaba Buhari ya sha alwashin rage yawan adadin ‘yan najeriya dake yunkurin tudada zuwa kasashen Turai ta kowacce hanya. Musamman hanyoyi masu hadari da suka hada da Hamadar Sahara da kuma Tekun meditereniya.

Samar da abubuwan more rayuwa da suka hada da Ilimi da lafiya da inganta aikin noma wanda zai baiwa dubban jama’a aikinyi da kuma samar da abinci ga dumbin al’ummar Najeriya, a cewar Garba Shehu.

Duk wasu hanyoyi da suka dace ana kokarin binsu domin ganin an dakile kwarar ‘yan Najeriya zuwa kasashen Turai ta barauniyar hanya domin neman ingantacciyar rayuwa a can kasashen Turai din.

Abu ne mai wahalar gaske, a iya gano ainihin garuruwan mutanan da suka mutu a yunkurinsu na tafiya kasashen Turai a kasar Libiya da tekun Meditereniya, kasancewar duk masu tafiyar babu wasu cikakkun bayanai da suke nuna inda suka fito.

“Lokacin da aka bayar da sanarwar, mutuwar mutum 26 ‘yan Najeriya a tekun Meditereniya, kafin a tabbatar da cewar mutanan ‘yan Najeriya ne ko ba ‘yan Najeriya bane, tuni aka binne su a wajen”

“Amma a bisa bayanan da na samu daga mai bani shawara kan ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen waje, mutum uku daga cikin ashin da shidan da aka ce ‘yan najeriya ne suka mutu, uku ne kacal bayanai suka tabbatar da cewar ‘yan Najeriya ne”

“Amma ba zan yi mamaki ba, idana aka ce dukkan mutanan ‘yan Najeriya ne. Mutanan su dinga yin wannan tafiya mai cike da hadai suna hawa kwale kwale a cikin teku, zamu yi abin da zamu iya wajen ganin mutanan sun zauna a gida Najeriya”

“Duk wani mutum da zai mutu a cikin sahara ko a tekun Meditereniya, matukar babu wasu cikakkun bayanai da suka nuna cewar dan Najeriya ne, to babu wani abu da zamu iya yi a gwamnatance domin babu hanyar da zamu gane namu ne”

“Abin takaici ne da kaduwa kwarai da gaske, muga hoton bidiyon da ake sayar da ‘yan Najeriya kamar awaki a matsayin bayin da aka yi garkuwa da su, akan kudin da bai taka kara ya karya ba, a kasar Libiya”

Shugaba kuma, ya tabbatar da ‘yan najeriya dake zaune a kasar ta Kwadebuwa cewar, akwai abubuwa masu dadi dangane da Najeriya, domin ana samun ingantuwar tsaro da sha’anin tattalin arziki da aikin gona da sauran.

Categories
Kanun Labarai

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na ranar Laraba

Mataimakin Shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo shi ne ya jagoranci zaman majalisar zartawar na mako-mako da ake gudanarwa a wannan Larabar a fadar Shugaban kasa dake birnin tarayya Abuja.

An fara zaman ne da misalin karfe 10:55 na safiyar Laraba. Zaman dai ya samu halartar Ministoci kamar su Lai Mohammed Minsitan yada labarai da al’adu, Minsitan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu.

Sauran su ne, Minsitan ciniki da masana’antu da zuba jari, Okechukwu Enalema; Harkokin Noma, Audu Ogbe; Ministar Mata, Jummai Alhassan da kuma karamar ministar harkokin kasashen waje, Khadija Abba-Ibrahim.

Ragowar su ne, ministar kudi, Kemi Adeosun; da karamin ministan zirga zirgar jiragen sama, Hadi Sirika, wadannan da ma wasu, sune wadan da suka samu damar halartar zaman majalisar na yau laraba a fadar Shugaban kasa.

Haka kuma, daga cikin wadan da suka halarci zaman akwai Magatakardar Gwamnatin tarayya Boss Gida Mustapha, Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa Alhaji Abba Kyari da sauransu.

Categories
Kanun Labarai

An rantsar da Uhuru Kenyatta a matsayin Shugaban Kenya karo na biyu

A ranar talata 28 ga watan Nuwamba aka rantsar da Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto a matsayin Shugaban kasa da mataimakinsa karo na biyu. A lokacin d yake jawabi bayan ya sha rantsuwar kama aiki, Mista Kenyatta yace zai yi Gwamnati a bude wadda zata kunshi ‘yan hamayya da suke fatan cigaban kasar Kenya.

Shugaba Kenyatta da mataimakinsa William Ruto, zasu sake yin wa’adi na biyu kuma na karshe na tsawon Shekaru biyar a matsayin Shugaban kasa da mataimakinsa. A jawaban da ya gabatar dai bai yi bayanin ko Gwamnati tasa zata kunshi Jagoran ‘yan Adawar kasar, Riyila Odinga ba.

Sai dai a jawaban da ya gabatar masu ratsa jiki, ya bayyana cewar, shi Shugaban kasar Kenya ne wadda ta kunshi kowa da kowa ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, dan haka yake kira ga mutanan Kenya da su bashi hadin kai domin cin ribar ayyukan raya kasa da zai shimfidawa kasar ta Kenya.

“Zan yi Gwamnati a bude, wadda ta kunshi kowa da kowa, burinmu yanzu shi ne samar da dabarun da zasu kawowa kasar Kenya cigaba mai dorewa ba tare da la’akari da yanki ko kabila ko addini ba, kasar Kenya ta dukka ‘yan Kenya ce, babu wani wanda yafi wani sabi da kabila ko yanki ko addininsa”

Dubunnan mutane ne, dai suka halarci babban filin wasa na birnin Nairobi da aka gudanar da bikin rantsuwar, inda aka yi ta kade kade da bushe bushe a wajen filin wasa, tare da rera taken kasar, sannan kuma a gefe guda, mutane na ta daga jajayen kyallaye, alamar jam’iyyar Shugaba Kenyata.

Shugaba Kenyatta dai yana kan zagon na biyu kuma na karshe a matsayin Shugaban Kenya. Yanzu dai duniya zata zuba masa ido dan ganin yadda zai gudanar da Gwamnatinsa, kamar yadda yace zata kunshi dukkan ‘yan Kenya ba tare da la’akari da addini ko yanki ko kabila ba. Abinda ba’a sani ba shi ne, ko Gwamnati zata kunshi jagoran ‘yan hamayyar kasar Rayila Odinga?

Categories
Labarai

Sanata Shehu Sani ya yi tur da Gwamna el-Rufai kan korar ma’aikatan kananan hukumomi

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, yayi tur da matakin da Gwamnatin el-Rufai ta ɗauka na korar ma’aikatan kananan hukumomi a faɗin jihar. Sanatan yayi wannan kamai ne a shafinsa na facebook a ranar talata. Inda ya bayyana abin da cewar rashin Imani ne da rashin tausayi na Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru el-Rufai.

“Wannan korar da suka yi wa ma’aikata ba komai ba ne, banda zalinci da mugunta da cin zarafi da wannan Gwamnan ya saba nunawa mutanen jihar Kaduna, tun daga lokacin da ya hau kan karagar mulkin jihar”

“Jihar Kaduna na samun isassun kuɗaɗe daga kason wata wata na asusun gwamnatin tarayya, domin biyan albashi, saboda haka babu wani dalili na korar ma’aikata da Gwamnati take yi”

“Gwamnan Kaduna yana gallazawa mutane ne, sabida yana ganin yafi karfin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, sannan kuma, yana ganin yafi karfin Shugabancin jam’iyyar APC, amma abinda bai sani ba, shi ne, bai fi karfin Allah ba”

Sannan kuma, sanata yayi kakkausar suka akan yadda aka zura ido Gwamna el-Rufai na cin mutunci da zarafin wanda yaga dama. Ya kuma tunasar da Gwamnan cewar, ya sani, shima akwai lokaci na zuwa da al’ummar jihar Kaduna zasu nuna mishi iyakarsa.

“Duk wanda yaci mutuncin mutane, da duk wanda ya goyi bayan cin mutuncin mutane azzalimi ne, bai cancanci a sake koyon bayansa ba, dan haka, kada jama’a su sake zaben wannan mutumin”

“Ya koreku a yau, lokaci yana zuwa da kuma zaku koreshi; ya rushe ku a yau, lokaci yana zuwa da kuma zaku rushe shi; ya kakkabeku a yau,lokaci yana zuwa da kuma zaku kakkabe shi,In sha Allah”

Bayan haka kuma, Sanatan ya ci alwashin cewar, zasu yi dukkan abinda zasu iya wajen ganin an mayar da duk wanda aka kora daga aiki ya koma bakin aikinsa, tun daga kan hakimai da malaman makaranta da su kansu ma’aikatan kananan hukumomi.

“Malaman makarantu da aka kora da hakimai da aka kora da kuma ma’aikatan kananan hukumomi da aka kora, ku yi hakuri zaku koma bakin aikinku, nan ba da jimawa ba, bayan wannan Gwamnatin da mukarrabanta sun kau”

A farkon wannan makon ne dai gwamna ya sa aka fara sallamar ma’aikatan kananan hukumomi daga ayyukansu, inda akai ta yayata abin a kafafen sada zumunta na intanet da aka fi sani da ‘Socialmedia’.

Categories
Taska

Za a kaɗa gwanjon wasu hotunan tsiraici na marigayi Tupac Shakur

An shirya yin wani kasaitaccen bikin baja kolin wasu hotunan tsiraici na shararren mawakin turancin nan dan kasar Amurka, Tupac Shakur, tare da takardar shaidar mutuwarsa. hotunan dai su ne irin na farko, wanda suke bayyanar da tsiraicin marigayi TuPac da za a kada musu gwanjo.

Ana sa ran kudin da za ayi Gwanjon hotunan zai fara daga $15,000 zuwa abinda ya sauka, kuma za ayi wannan kada gwanjo ne a wani dandali mai suna “Gotta Have Rock and Roll”.

Su dai wadannan hotunan, rohotanni sun ce, wata tsohuwar budurwar marigayi Tupac ce ta taba daukansu da kyamarar daukar hoto, kuma taki bayyanar da hotunan tun a lokacin da ta dauke su, sai a yanzu tace za’a kada musu gwanjo.

Budurar ta bayyana yadda aka yi ta dauki wadannan hotunainda tace “Na dauki wadannan hotunan na tsiraicin marigayi Tupac ne a shekarar 1990 a wani gidan rawa a unguwar Marin County. Ya kasance yana da wata dabi’a (Tupac) duk lokacin da yaje gidan rawa bayan an gama cashiya, yakan baiwa abokansa dariya, ta hanyar kwabe wandonsa na ciki (kamfai) inda yake nuna musu tsiraicinsa su kuma su bushe da dariya”

“A lokacin da abin ya faru, wani dare ne da ba zan manta shi ba, ina kokarin kashe kyamarata da nake daukar hoto a lokacin, sai ga Tupac Shakur ya shigo, kamar yadda ya saba, kawai ya kwabe wandonsa na ciki, ya tsaya zindir, ni kuma nace masa yayi sauri ya kauce ko na dauki hotonsa tsirara, kawai sai yayi min gwalo, ni kuma kawai na dauke shi hakan zigidir”

“Fitilar kyamarata a lokacin ta haska Tupac a lokacin da na dauke shi hoton, alamar da saninsa na dauki hoton amma kuma bai damu ba, ya nuna ko a jikinsa dan na dauki hotonsa tsirara. Hoton dai ya nuna zallar tsiraicin Tupac, daman kuma shi mutum ne mai al’adar cire riga a ko da yaushe”

“Tun a wancan lokaci, babu wanda na taba nunawa wadannan hotuna da na dauki Tupac Shakur zigidir, sai yanzu da nake son a kada musu gwanjo domin a saida su, ta kara da cewar, wadannan hotunan su ne irinsu na farko da za a kada musu gwanjo, domin duk duniya babu wani wanda yake da irin wannan hoto sai ni” a cewar tsohuwar budurwar Tupac wadda ta nemi a sakaya sunanta.

Bayan haka kuma, za a kadawa takardar shaidar mutuwar Tupac gwanjo, wadda a baya an sha yin takadda kan ainihin rasuwar Tupac, ta yadda suke ke musun cewar bai mutu ba. Takardar shaidar mutuwarsa dai an yi ta ne a shekarar 1996, sannan kuma za’a kada mata gwanjon daga $5,000 zuwa abinda ya sauwaka.

Ikon Allah, ko me zaku ce kan wannan batu?

Categories
Labarai

‘Yan sanda a jihar Taraba sun gargaɗi mutane kan yaɗa wani bidiyo na batsa

Rundunar ‘yan sanda a jihar taraba a ranar litinin ta gargaɗi al’ummar jihar kan yaɗa wani hoto bidiyo a shafukan sada zumunta na intanet da yake nuna mace da namiji mazauna birnin jalingo suna saduwa da juna.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, David Misal shi ne yai wannan gargadi a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar. Yace cigaba da yaɗa wannan bidiyo da ake yi a shafukan sada zumunta na intanet bai dace ba, kuma zai iya kawo yamutsi.

Su dai mutanan da aka nuna suna saduwa da juna a bidiyon mazaunan birnin Jalingo ne, abinda yake sanya tsoron kada hakan ya harzuka mutane su tayar da hankali a jihar. Yace, wannan bidiyo ba ga mutanan kadai, yana iya zubar da mutuncin jihar ta taraba.

Lokacin da DALIY NIGERIAN ta tuntubi wani Malamin addinin Musulunci a jihar, Sheikh Aminu Abdullahi ya yi tur da wannan hoton bidiyo tare da yin Allahwadai da masu yaɗa shi, sannan kuma yayi kira ga ‘yan sanda da su takawa yaɗuwar abin birki.

“Ina kira ga dukkan hukumomi a jihar Taraba da su dakile yaɗuwar wannan bidiyo domin hakan bai dace ba a ddinin Musuunci ba da kuma zamantakewa irin ta mutanan Jalingo dama Jihar Taraba baki daya ba, sannan hakan, ya sabawa dokar kasa”

“Kasancewar mutanan da suka yi wannan bidiyo mutanan Jalingo ne, ya zama dole a gurfanar da su gaban kuliya domin a hukuntasu kan wannan batsa da suka aikata, domin hakan ya zama izna ga sauran al’umma”

“Ba zai yuwu ba hukumomi su zuba ido ana cigaba da yaɗa wannan bidiyo a wayoyin hannu, domin hakan na iya bata tarbiyyar yara manyan gobe, hakan kuma babbar illa ne idan aka yi sake yara kanana suka dinga ganin irin wannan bidiyo”

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ne ya ruwaito.

 

 

Categories
Kanun Labarai

Buhari ga Gwamnoni: Ku biya dukkan haƙƙoƙin ma’aikata kafin kirsimeti

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaman da yayi da gwamnnoni yau a fadar Gwamnati a Abuja, ya kalubalanciGwamnonin da su biya dukkan hakkokin ma’aikata da suke bin Gwamnonin bashi kafin bikin kirsimeti mai zuwa.

Ma’aikatan jihohi da dama ne suke bin gwamnatocin jihohinsu bashin albashi da alawus alawus na watanni da dama a Najeriya.

Categories
Labarai

Ficewar Atiku: Jam’iyyar APC ta yi wawar asara – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ficewar tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar a matsayin abin kaduwa kwarai da gaske. A ranar Juma’ar nan ne dai Atiku Abubakar ya aikewa da uwar jam’iyyar APC ta kasa wasikar ficewarsa daga jam’iyyar.

Shugaba Buhari ya jajantawa Shugaban jam’iyyar APC na kasa Cif John Oyegun bisa wawar asarar Atiku Abubakar da jam’iyyar ta yi. Buhari ya bayyana Atiku Abubakar da cewar mutum mai matukar muhimmanci a cikin jam’iyyar ta APC.

Shugaban ya bayyana haka ne, ranar litinin a Abuja yayin da yake kaddamar da kwamitin da zasu duba yiwuwar samar da mafi karancin albashi, tare da duba hali da yana yin da ma’aikata suke ciki.

A yayin wannan taron, lokacin da Shugaban ke mika gaisuwa zuwa ga mahalarta taron, da ya zo kan Shugaban APC na kasa, wanda yake wajen, Buhari ya jajanta masa bisa wawar asarar da jam’iyyar ta yi na hazikin mutum, dukda cewar Shugaba Buhari bai ambaci sunan Atiku Abubakar ba, amma dukkan alamu kalamansa na nuni da ficewar Atiku Abubakar daga jam’iyyar.

Categories
Kanun Labarai

Shugaba Buhari zai gana da Gwamnoni da misalin karfe 2 na ranar litinin

A yau Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da tawagar gwamnonin Najeriya a fadar Gwamnati dake Aso Rock Abuja.

Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, kuma Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar shi ne zai jagoranci gwamnonin zuwa fadar Shugaban kasa da ranar nan.

Har ya zuwa yanzu dai ba a san ko akan meye zasu tattauna ba. Zuwa jimawa zamu kawo muku cikakken rahoto.