Categories
Raayi

2019: Bajekolin makaman yakin neman zaben APC

Daga Ashafa Murnai Barkiya
1. Gamna Ganduje ya zubar da mutuncin Shugaba Muhammadu Buhari. Duk da kururuwar da Gwamnatin APC ke yi cewa za a samu canjin tafiyar siyasar kasar nan, hakan ya nuna ba gaskiya ba ne.
2. Gwamna Ganduje bai dauki Fadar Shugaban Kasa da daraja ba, domin ta kira shi, kuma ta kira Kwankwaso domin a samu zaman lafiya a Kano. Gwajin Makaman da Ganduje ya yi, ya tabbatar da gaskiyar zargin da Kwankwaso ya yi cewa an yi shirin afka musu idan sun kai ziyara a Kano.
3. Kimar Kwamishinan ‘Yansandan Kano ta ragu sosai a idon jama’a, idan ma ba ta zube ba. Wanda ya nemi hana Kwankwaso taro, sai ga shi gwamnatin jihar ta shirya ‘gwajin makamai’ a gaban sa. Ni ma na goyi bayan cewa ba adali ba ne, a dauke shi daga Kano.
4. Sufeto Janar na ‘Yansanda ya kyale Kwankwaso ya yi na shi taron, tunda dai har Ganduje ya yi na shi bajekolin, kuma a ranar da ya kamata Kwankwaso ya yi taron sa.
5. Jam’iyyar APC ta ba talakawa kunya da har ta daure wa Ganduje gindin gudanar da irin wannan mahaukacin taro. Duk wanda ya tuna alkawurran da ku ka yi wa jama’a na gyara kasar nan, ya san cewa kun yi ta aibata PDP ku na nuna hotunan magoya bayan su dauke da makamai, ku na cewa za ku canja.
6. Duk wanda ya dauko mana irin wannan haukan ya nemi ya saka mana shi a cikin ajandojin sa na 2019, to mu ma za mu ci gaba da yakar sa a kafafen sadarwa, ko wane ne shi, za mu ci gaba da nuna wa jama’a illar sake zaben sa.
7. Yanzu kuma da wane bakin magana magoya bayan APC za su ci gaba da aibata wasu? Canjin da mu ka yi ta fafutikar kawowa a 2015 kenan?
8. Akwai babbar matsala ga Shugaba Buhari a kamfen din 2019, tunda har ya yi likimon da ya bari ‘yan-takifen siyasa su ka shiga gaban sa, su ka canja wa APC sabon launin tambarin jam’iyya, su ka maye gurbin wanda aka sani da takubba, sanduna, adduna, gariyo, barandami da duk wani makamin tayar da hankulan jama’ar da aka yi wa romon-kunne a 2014, aka ce za a samu canji.
9. Shekara uku cur mu ka yi, mu na rubuce-rubucen kawo canji. Amma wasu ‘yan takife na neman maida wahalar da mu ka yi ta zama wahalar banza. Sun kimshe na su ‘ya’yan a gida da cikin manyan makarantu, sun bar talakawa dauke da takubba da barandami.
Wannan ra’ayi na ne, amma duk wanda ya tsargu, to da shi na ke!
Categories
Labarai

Miyagun ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane 38 sun shiga hannu a Kaduna

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, ta ci nasarar cafke ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane su 38 wadan da suka addabi hanyoyi a Kaduna, an kame ‘yan fashin daga ranar 20 ga watan Oktoban 2017 zuwa 25 ga watan Janairun 2018.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Mista Austin Iwar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba.

Yace a cikin mutum 38 din da aka kama, 21 an kama su ne da kokarin yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da ayyukan ta’addanci, 17 kuma an kama su ne da laifin sace sace na cikin unguwa da kuma ayyukan sara suka.

Yace, irin miyagun makaman da aka samu a wajensu, sun hada da Alburusai 41 da manyan motoci guda uku, sannan kuma rundunar ‘yan sanda ta ci nasarar tarwatsa wata maboyar ‘yan fashin a cikin daji.

Kwamishinan ‘yan sandan yace, abin farinciki a wannan kame da aka yi shi ne, an kama ‘yan fashin da suka addabi hanyar Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano.

“Wasu daga cikin wadan da aka kama din, suna yin garkuwa da mutane a yankin Lere da Fambeguwa a yankin Kubau da Zaria”

Sannan kuma, yace, wadan da aka kama masu sace sace da sara suka an kama su ne a Rigasa da Tudun wada da Kawo da Unguwar Rimi duk a cikin birnin Kaduna.

Yace dukkan mutanan da aka ci nasarar kamawa suna nan a hannun ‘yan sanda suna bayar da bayanai, ‘yan sanda kuma na cigaba da gudanar da bincike, daga zarar an kammala bincike za’a gabatar da su gaban kotu don fuskantar hukunci.

“Muna son mu tabbatarwa da al’umma cewar, rundunar ‘yan sanda tana aiki babu dare babu rana wajen ganin ta kamo masu laifi a duk inda suke, da karya lagon dukkan wani aikin batagari” A cewarsa.

Sannan yayi kira ga al’umma da su baiwa rundunar ‘yan sanda hadin kai musamman wajen bayar da bayanan da zasu kai ga samun nasarar cin lagon miyagunmutane a ko ina suke.

 

Categories
Labarai

Ɗan sanda ya kashe abokin aikinsa sakamakon taƙaddama a Adamawa

Wani dan sanda mai suna Bala Adamu a ranar talata ya kashe har lahira wani abokin aikinsa, Emmanueel Timothy, wanda yake aiki karkashin runduna ta musamman a karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.
A lokacin da yake tabbatar da faruwar wannan al’amari a gaban ‘yan jarida, Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Adamawa, Othman Abubakar, ya bayyana cewar, lamari ya auku ne, bayan wata gajeruwar takaddama ta shiga tsakanin ‘yan sandan biyu da misalin karfe 10:45 na safe, a caji ofis na Madagali.

 

“Mamamcin, Timothy mai mukamin Saja, wanda ya samu hora daga runduna ta 13 a Mukurdi na daga cikin wadan da aka turosu jihar Adamawa domin yin aiki na musamman” A cewar Othman Abubakar.
Otthman bai bayar da cikakken dalilin wannan hatsaniya da ta kaure tsakanin ‘yan sandan biyu ba, sai dai ya tabbatar da cewar dan sandan da yayi kisan Adamu tuni aka tsare shi a sashin masu manyan laifuka, inda yace tuni aka tura batun zuwa sashin bincike na rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

 

NAN

Categories
Kanun Labarai

Majalisar Dattawa: Ba zamu tattauna batun Kwankwaso da Ganduje ba, matsalarsu ce ta cikin gida

Bayan wata zazzafar muhawara a zauren majalisar dattawa a ranar laraba, majalisar tace ba zata tattauna batun rikici tsakanin Kwankwaso da Ganduje ba, domin a cewar majalisar rikicin batu ne na cikin gida tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

Sanatocin sunce duk wani abu da ya faru tsakanin Kwankwaso da Ganduje batu ne na cikin gida, sannan majalisar ta bukaci Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya da ya baiwa Sanata Kwankwaso cikakken tsaro a duk ranar da ya sanya zai shiga jihar Kano.

Da yake bayyana jawabi kan wannan batu, Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, yace ya saurari dukkan bangarorin da suke adawa da junatsakanin Kwankwaso da Ganduje, kuma yace al’amarin batu ne na cikin gida.

Saraki yace, a dukkan jihohin fadin tarayyar Najeriya, akwai sabani tsakanin tsohon Gwamna da sabon Gwamna, yace wannan sabani na Kwankwaso da Ganduje ba wani sabon abu bane, a sabida haka ba wani abu bane da majalisar dattawa zata mayar da hankali akansa domin tattaunawa ba.

Haka nan kuma, Mista Saraki, ya bukaci kwamaitin majalisar dattawa dake lura da sha’anin ‘yan sanda da ya gayyaci Sufeto janar na ‘yan sanda na kasa domin yayi musu bayanin yadda akai ya kasa baiwa Sanata Kwankwaso cikakkun jami’an tsaro a taron da ya shirya yi 30 ga watan da ya gabata.

Tun farko dai, Sanata Isah Hamma Misau daga jihar Bauchi ne, ya kawo batun gaban zauren majalisar dattawa inda yace akwai munanan hotuna dauke da muggan makamai, da aka dinga yadawa a shafukan sada zumunta na intanet, wanda aka ce an dauke su ne a Kano.

Sanata Misau yace, idan har za’a iya hana dan majalisar dattawa zuwa mazabarsa domin ganawa da al’ummar da yake wakilta, to lallai akwai matsala a kasarnan.

Yace,idan hotunan da muke gani suna yawo a shafukan sada zumunta na intanet game da kano gaskiya ne, to lallai rayuwar al’umma tana cikin hadari kwarai da gaske.

Yace a matsayina na Sanatan da ya fito daga Bauchi, wadda muka yi iyaka da jihar Kano, yace wannan shi ne dalilin da ya ja hankalinsa cewar, lallai abinda yaci doma baya barin Awe.

Daga nan Sanata Misau ya bukaci Sanatoci da su yi Allah wadai da abinda ya faru a Kano na kokarin dawo da siyasar daba da yawo da makamai.

Bayan da Sanata Misau ya gama jawabinsa, Sanata Kabiru Gaya daga Kano, yace ya caccaki Misau, inda yace duk irin abubuwan da suka gudanar a jihar babu inda aka tayar da rikici koo hatsaniya.

Yace duk wani sabani tsakanin Kwankwaso da Ganduje batu ne na cikin gida kuma za’a warware shi cikin sauki.

A nasa bangaren, Sanata Barau Jibrin, daga jihar Kano, yayi mamakin ya zai Sanatan da yake bauchi ya kawo batun da ya shafi jihar Kano a zauren majalisar dattawa, bayan kuma kowannen Sanatoci suna da matsaloli da gwamnonin jihohinsu.

 

Categories
Labarai

Hukumar kare haƙƙin Ɗan-adam ta ƙasa ta samu ƙorafe ƙorafe 583 a shekarar bara

Hukumar lura da hakkin Da-Adam ta kasa, NHRC, shiyyar Arewa maso yamma, a babban ofoshinta dake Kano, ta bayyana cewar a shekarar bara ta samu korafe korafe kusan 583, sannan kuma taci nasarar horas da ‘yan sanda 50 kan yadda zasu kare ‘yancin al’umma.

Babban kodinetan hukumar shiyyar Arewa maso yamma, Hajiya Hauwau Salihu ce ta bayyana haka a Kano, inda tace a cikin kararraki 583 da hukumar ta karba, 256 an bibiyesu kuma an kai karshensu, sauran 327 sune har yanzu ake bibiya.

Ta bayyana cewar, mafiya yawancin koken da hukumar take samu, batu ne da ya shafi mutanen a gidajensu da unguwanninsu. Da kuma batun ciyarwa bayan miji ya rabu da matarsa ga yaran da suka haifa.

Hajiya Hauwa ta cigaba da cewa, sauran korafe korafen sun hada da, batun gado, tsare mutane ba da hakki ba, cin zali, tursasawa, da kuma azabtar da yara ba are da wani hakki ba.

Kodinetan hukumar, ta bayyana cewar galibin kararrakin da ke wajensu, suna bukatar sasantawa ne da kuma tattaunawa domin gano bakin zarensu.

Sannan kuma tace, wasu korafe korafen suna mika su ne zuwa kotuna domin samun maslaha a can domin gudanar da zuzzurfan bincike kan wasu matsalolin.

Haka kuma, ta kara da cewar hukumar ta kammala duk wasu shirye shirye na baiwa wasu karin ‘yan sanda guda 50 horo a wannan shekarar ta 2018.

 

Categories
Labarai

Shugaba mai tsoron Allah ba zai iya yaki da cin hanci ba a Najeriya – Bishop Kukah

Babban Bishop na Sakkwato, Rabaran Matthew Hassan Kukah, a ranar laraba, ya bayyana cewar, yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, wani babban al’amari ne da yake bukatar ba wai kawai mutum mai tsoron Allah ba.

Mista Kukah yana bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da wani littafi mai suna “The Shadow List” wanda cibiyar yada bayanai da harkar jarida ta Afurka ta shirya a babban birnin tarayya Abuja.

“Kawar da cin hanci da rashawa, tare da gina sabuwar al’umma da ba tada sofane na cin hanci, ba batu bane kawai na muna fata. Wannan batu ne da yake bukatar jajirtaccen Shugaba ba wai kawai mai tsoron Allah ba”

“Na sha nanata cewar, Najeriya baata bukatar Shugaba mai tsoron Allah, domin mai tsoron Allah sau da dama yakan zama uzuri. Idan kana bukatar tsoron Allah to kana iya zama mai tsoron Allah in kaso”

Mista Kukah, yaga baiken masu mulki inda yace sun zama tamkar wani gungugu na masu laifi, domin kowa ka daga shi sai ka tarar da kwance yake cikin dukiyar haram.

Kukah yace, idan muka tsaya muka fahimci zahirin abinda yake damun kasarmu, to mun taimaki kanmu.

Yace,ina mamakin yadda ‘yan Najeriya a koda yaushe suke murna idan an samu sabuwar Gwamnati, wanda daga baya sai ka samu sabuwar Gwamnatin ba ta da maraba da wadan da suka gabace ta.

“Babu wanda yayi zaton shekaru ukun nan da suka wuce, zamu kasance a yadda muke ciki yanzu”

A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa, tsohon Shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Malam Nuhu Ribadu, ya jinjinawa mawallafin littafin, a bisa yadda ya dauki lokaci yana bayanin akan Najeriya da kuma batun yaki da cin hanci da rashawa.

Ribadu ya bayyana gamsuwarsa da kaddamar da irin wadannan litattafai, domin a cewarsa zai taimakawa masu karantawa fahimtar yadda Najeriya ta sanya gaba kan batun yaki da cin hanci da rashawa.

Mahalarta taron da yawa da suka tofa albarkacin bakinsu sun jinjinawa mawallafin littafin a kokarin na bayyanawa ‘yan Najeriya halin da ake ciki kan batun yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Categories
Labarai

Dangote ya mallakawa BUK wani katafaren gini na biliyoyin kudi

A kokarinsa na taimakawa al’umma wajen ganin an koyawa mutane sana’o’i domin fita daga cikin halin kangin talauci, fitaccen attajirin nan Alhaji Aliko Dangote, ya mallakawa jami’ar Bayero dake Kano, wani katafaren gini da kimarsa takai naira biliyan 1.2, domin horar da mutane kan ilimin kasuwanci da sana’a.

Wannan katafaren gini da Alikoo Dangote yayi, za’a yi bikin mika shi zuwa ga jami’ar Bayero a wata mai zuwa, kuma a lokacin ne ake sa ran fara amfani da shi wajen koyarwa a fannin kasuwanci da kuma sana’a.

Wannan gini irinsa ne na farko a kafatanin jami’o’in dake Arewacin Najeriya. haka nan kuma, Alhaji Aliko Dangote na gia wani makekekn gini makamancin wannan, a jami’ar birnin Badun dake jihar Oyo a yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Gidauniyar Aliko Dangote ce dai ta dauki gabarar wannan ayyuka domin bayar da tasa gudunmawar wajen inganta rayuwar al’umma, ta hanyar tallafa musu wajen samun ilimin sana’a da kuma na kasuwanci domin tafiya daidai da zamani.

Binciken DAILY NIGERIAN ya tabbatar cewar, wannan kaafaren gini na BUK ya kunshi, babban dakin taro da dakunan daukar darasi da azujuwa da dakin karatu da ofisoshin Malamai da sauransu.

 

Categories
Kanun Labarai

An sake sanya zare tsakanin Hameed Ali da ‘yan Majalisar Dattawa

Sa-toka sa-katse tsakanin Shugaban hukumar Kwasttam ta kasa Kanar Hameed Ali mai ritaya da ‘yan majalisar dattawa, har yanzu bata kare ba. A ranar litinin din nan, akai musayar yawu sakanin Hameed Ali da ‘yan majalisar dattawan.

Wannan sabani ya biyo bayan wata ziyara da kwamitin musamman kan sharar masana’antu na majalisar dattawa ya kai shalkwatar hukumar kwastam ta kasa a birnin tarayya Abuja.

Shugaban kwamitin, Sanata Dino Melaye, mun yi tsammanin Shugaban hukumar kwastam din zai tsaya dan ya karbi tawagar Sanatacin a harabar hukumar, ba kawai muje mu jira shi a dakin taro na hukumar ba.

Yace wannan shi ne tsarin da ake bi,idan baki sun shigo Shugaban hukumar ya fito domin ya karbe su, a ko ina, yace amma abinda Hameed Alin yayiwa Kwamiin abu ne da sam bai dace ba, kuma ya karya tsari.

“Kaafin na karanta jawabin wannan kwamiti da yake gabana, bari nayi wata magana kan abinda akai mana yayin da muka shigo gidannan na karya tsari da ka’ida”

“Shugaban Kwastam, maimakon ka zo ka nan dakin taro ka same mu, ya kamata ace kaine da kanka ka fito harabar hukumar nan ka tarbemu ka yi mana barka da zuwa” A cewar Dino Melaye.

A lokacin da yake mayar da martani kan wannan korafi, Shugaban hukumar Kwastam ta kasa hameed Ali, ya shaidawa ‘yan majalisar cewar, hukumar Kwastam na da nata tsarin, sabanin wanda aka sani ana yi a gurare da ban daban, ba kuma dole ne sai Kwastam tayi koyi da abinda wasu ke yi ba.

“Muna da tsare tsare irin namu, na yaddamuke karbar baki kamarku. Babu bukatar sai na sauko daga ofishina a sama na zo kasa dan na karbe ku, kamar yadda babu wani sanata da ya taba saukowa daga ofishinsa domin ya karbemu idan mun je majalisar dattawa”

“Bari na sake tabbatar muku da cewar, mu a hukumar Kwastam, muna yiwa al’ummar kasa aiki ne. Mun aminta da tsarin kasarmu, muna aiki da juna domin ciyar da ita gaba ba tare da tunanin zamu sabawa wani ko baiwa wani haushi, ba mu fatanmu muyi abinda ya dace ko da wani bai ji dadi ba” Inji Hameed Ali.

NAN

Categories
Labarai

Gwamna Fayose na Ekiti yace Allah ne ya bashi umarni ya zabi mataimakinsa a matsayin wanda zai gaje shi

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose, a wajen wani gangami da jam’iyyar PDP ta shirya a Ado-Ekiti, ya bayyana cewar,Allah ne ya umarce shi da ya zabi mataimakinsa, Kolapo Olusola Eleka a matsayin wanda zai gajeshi.

“Olusola bai taba tunanin zai zama mataimakin Gwamna ba, Amma Allah ya umarce ni da na dauke shi ya zamar min matamaiki, na gaya masa idan wa’adinmu ya kare tare zamu sauka, amma saai Allah yace na zabe shi a matsayin wanda zai gaje ni” Fayose ya fada a gaban jama’a.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar, tsohon ministan ayyuka da gidaje, Dayo Adeyeye, da Sanata Biodun Olujimi da wani jakadan Najeriya a Kanada Dare Bajide duk sun nuna sha’awarsu ta neman tsayawa gwamnan jihar a jam’iyyar ta PDP a zaben da za’a yi 14 ga watan Yuli.

Sai dai wani Kwamishina a Gwamnatin ta fayose, Owoseeni Ajayi, yayi tutsu kan batun zabar Olusola a matsayin dan takarar jam’iyyaar ta PDP.Indaa ya bayyana hakan da cewar tsabar rashin adalci ne.

NAN
Categories
Labarai

Ja da baya ga Rago ba tsoro bane – Kwankwaso

Sanatan Kano ta tsakiya a majalisar dattawa ta Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya magantu tun bayan jingine batun zuwansa jihar Kano a gobe talata sabida dalilai na tsaro.

uni dai aka gayyaci tsohon Gwamnan fadar Shugaban kasa, domin yin tata tattaunawa ta musamman da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo.

A lokacin da yake magana da manema labarai a gidansa a ramar litinin, Kwankwaso yace, ya jingine batun zuwan nasa gida Kano ne, sabida kiraye kiraye da aka yi ta yi a gareshi, daga muhimman mutane daga kano da Abuja, wanda tilas ta sanya ya amsa musu.

“Ina son jama’a su sani ja da baya ga rago ba tsaro bane, kawai na ji kiran mutane ne a ciki da wajen kano domin samun zaman lafiya”

“Kusan shekara uku ban shiga jihar Kano ba, rabona da kano tun da na je ta’aziyar babar Ganude, dan haka na jima ban je kano ba”

Yace, wasu ‘yan Siyasa a jihar Kano sun hada kai da ‘yan sanda da wasu mutane anan Abuja domin hanani shiga kano.

“Yau ‘yan sanda sun mamaye cikin birnin Kano domin hana dan Kano shiga garinsa, wanda yana da ‘yanci”

“Ina cike da mamakin yadda ake yin neman kama karya a jihar Kano, ta hanyar kawo sojoji, kamar ana yin yaki” A cewar Kwankwaso.

Da aka tambayi Kwankwaso ko ya jingine batun zuwansa Kano ne sabida tsaro,yace yafi karfin jin tsoron wani mahaluki.

“Babu wani mahaluki da nake tsoro. Ni da nayi Ministan tsaron Najeriya, dukkan sojoji suke kirana da Yallabai, nine za’a kira matsoraci” A cewarsa.

Yace nan ba da jimawa ba, zamu sake sanya wata ranar da zamu je Kano, wannan lokacin kuma, sai yafi kowanne, domin zamu yi shirin da bamu yi ba a baya.