Categories
Taska

Abubawa 12 da rashin samun wadataccen barci ke haifarwa

Daga Hassan Y.A.Malik

Kowannenmu na sane da yadda ya kan kasance idan bai samu isashen barcin dare daya ba kawai. Mu kan ji gajiya, bacin rai, mu kuma kasa nutsuwa. Amma da yawa a cikinmu na tunani a nan kawai al’amarin ya tsaya.

Rashin isasshen barci na wani tsahon lokaci na haifar da muggan matsaloli ga lafiyar jiki, wanda ba su magantuwa har sai an rama shi.

A duk lokacin da muka dau bashin barci, jikin mu bai iya yafewa. Ko dai mu rama, ko kuma mu fuskanci matsalolin da hakan ke haifarwa:

Ga wasu daga cikinsu kamar yadda masana su ka zayyana:

1. Mantuwa da rashin fahimta

2. Dakushewar kwakwalwa

3. Rashin karfin jiki

4. Bacin rai

5. Hawan jini

6. Matsalolin zuciya

7. Ramar jiki

8. Kunburin Idanu

9. Tsufa da wuri

10. Karyewar garkuwar jiki

11. Raguwar Sha’awa

12. Kara yiwuwar hadura

Categories
Labarai

Matashin da ya kashe dan yayarsa don yin tsafi ya shiga hannu

Daga Hassan Y.A. Malik

Wani matashi dan damfarar yanar gizo (Yahoo Boy a turance) ya shiga hannun hukuma, bayan da ya kashe dan yarsa mai shekaru 7 domin ya yi tsafin kudi da ita.

Matashin mai suna Tunde Owolabi wanda ake wa lakani da “Money Talk” wato kudi na magana ya aikata wannan abu ne a yankin Ikoyi da ke jahar Lagos.

Rahotanni sun bayyana cewa yaron da ya yi yunkurin yin tsafin da shi ba wani ba ce illa dan yarsa.

Wani ma’abocin amfani da shafin Facebook, Odueke Olumide, shi ya watsa wannan labari a shafinsa.

Ya ce Owolabi da kafar shi ya kai jami’an tsaro inda ya yasar da gawar yaron.

Yanzu haka jami’an tsaron na ci gaba da bincike akan shi kafin a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Categories
Labarai

Hadiman Gwamna Ganduje biyu na rigima akan mallakar ofis

Daga Hassan Y.A. Malik

Mai bawa gwamnan jihar Kano shawara na musamman akan harkokin sabbin kafafen yade labarai, Salihu Tanko Yakasai ya fadawa jaridar Vanguard a jiya cewa sakarci ne ya bar ofishinsa ga Darakta janar na yada labarai, Aminu Yassar wanda ya ke kasa da shi.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnan, Dakta Abdulahi Umar Ganduje ya karawa Yakasai girma daga mukamin darakta janar zuwa na mai bada shawara na musamman, yayin da aka maye gurbinsa da babban sakataren yada labarai na gwamnatin, Yassar.

Tun bayan da aka kara masu girma ne Yassar da tsohon maigidansa, Yakasai, ke hargitsi game da wanda zai rike ofishin darakta janar.

A cewar Yakasai, a tsarin mukaman gwamnati, mukamin hadimi shi ne mafi girma domin kuwa daidai ya ke da na kwamishina, yayin da darakta janar ya ke daidai da babban sakatare.

Ya ce “Gwamnati za ta iya baiwa kowane jami’i ofishin da ta ga dama, kuma ni wannan ofishi aka ba ni. Ba da karfi na kwata ba”

Ya ci gaba da cewa “Ba gidan ubana ba ne. A yau idan aka ce na bar ofishin, kafin ku ce Vanguard, na fita daga nan.”

Yakasai ya kara da cewa tun da ya fara aiki a gwamnatin Ganduje shekaru 2 da suka gabata, ya yi kokarin mutunta wadanda suke aiki tare kuma za su ci gaba wayar da kan jama’a game da ayyukan gwamnatin.

Categories
Labarai

Rikici ya barke tsakanin manoma da Fulani a Ebonyi

A jiya Talata ne rikici ya barke tsakani Fulani makiyaya da manoma a jahar Ebonyi, lamarin da ya haddasa jikkatar mutane 4.

Yayin da Fulani 3 suka samu raunika a kawunan su, daya daga cikin manoman ya samu yanka a gurare daban daban a sassan jikin shi.

Yanzu haka manomin na samun kulawa a asibitin gwamnatin tarayya da ke Abakaliki, babban birnin jahar, yayin da Fulanin ke asibitin Awgu da ke jahar Enugu.

Tuni dai mazauna yankin suka tsere daga gidajensu gudun kar Fulanin su kai masu harin ramuwar gayya.

Rahotanni sun bayyana yadda Fulani daga garin Mpu a jahar Enugu suka afkawa wata gona a yankin Akaeze da ke jahar Ebonyi inda suka yi kaca-kaca da gonar, lamarin da ya hassala manomin har ta gai ga ya yi magana, inda daga nan ne rikicin ya fara bayan da fulanin suka afkawa manomin da sara da suka.

Tuni gwamnan jahar, David Umahi, ya haramta kiwo a karamar hukumar har sai an kammala bincike game da batun tare da kafa kwamiti mai kunshe da mutane 10.

Gwamnan ya kuma kira taro da sarakunan gargajiyan jahar da shugabannin fulani makiyaya, da shugabannin kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kan lamarin.

Umahi ya ce duk manomin da ya kashe shanun makiyaya zai tafi kurkuku haka zalika duk makiyayin da ya lalata gonar manomi zai tafi kurkuku shi ma.

Sai dai ya ce dole kowane Bafulatanin da zai shiga jahar ya bi ka’idar bi ta kan titina ba ta cikin jeji ba.

Categories
Kanun Labarai

Cutar zazzabin Lassa ta ɓulla a jihohi 18

Daga Hassan Y.A. Malik

Zazzabin Lassa na ci gaba da yaduwa a sassan kasar nan inda zuwa yanzu rohotanni ke nuna cewa akwai akalla mutane 1,081 da ke fama da cutar a fadin Nijeriya baya ga mutum 90 da suka rasa rayukansu a jihohi 18 da cutar ta bulla.

Wannan bayani na kunshe ne a wata sanarwa da Cibiyar Lura da Cututtuka ta Nijeriya, NCDC, ta fitar a jiya Talata, inda snarwar ke cewa, akalla mutum 54 suka kamu da cutar a cikin mako guda, inda cutar ta sake bulla a jihohi 8 da a da babu, haka kuma aka sake samun rahoton mutuwar mutum 10 a jihohi 5.

Sanarwa ta ci gaba da cewa dukkan mutane 1,081 da aka samu da cutar a baya-bayan nan sun dauki zazzabin daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa ranar 25 ga watan Fabrairun 2018, kuma mace-macen sun faru ne a jihohin: Edo, Ondo, Bauchi, Nassarawa, Ebonyi, Anambara, Binuwai, Kogi, Imo, Filato, Legas, Taraba, Delta, Osun, Ribas, Abuja, Gombe da jihar Ekiti

Kaso 43 daga cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar zazzabin Lassa daga jihar Edo suke, sai jiha mai bi ma ta ita ce jihar Ondo mai kaso 26 cikin 100 na adadin mutanen da ke dauke da cutar.

Ma’aikatan lafiya da wadanda ke kula da marasa lafiyar guda 14 sun kamu da cutar a jiho 6. Ma’aikatan lafiya 7 daga Ebonyi, 1 daga Nassarawa, 1 daga Kogi, 1 daga Binuwai, 1 daga Ondo, sai 3 daga Edo. Haka kuma mutane 4 ne daga ma’aikatan lafiyar suka rasu, 3 daga Ebonyi, 1 daga Kogi.

Categories
Labarai

An kama mutane 18 da ake zargi da hannu a rikicin addinin da ya barke a jihar Kaduna

Jami’an tsaro a jihar Kaduna sun kama mutane 18 da ake zargi da hannu wajen kitsa rikicin addini a jihar Kaduna ranar Litinin a kasuwar Magani dake yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

An bayyana hakan ne jim kadan bayan da dukkan sassan jami’an tsaro na jihar Kaduna suka ziyarci yankin da abin ya faru a kasuwar magani domin ganin irin dumbin barnar da rikicin ya haifar.

Tawagar wadda Shugaban Kwamnadan rundunar soji ta daya dake jihar Kaduna Manji Janar Mohammed Mohammed ya jagoranta, ta kunshi kwamishinan ‘yan sandan jihar Austin Iwar da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya Mohammed Wakil.

Sauran ‘yan tawagar su ne, Shugaban hukumar tsaro ta NSCDC AM Bunu damai baiwa Gwamnan jihar Kaduna shawara ta fuskar tsaro Kanar Yakubu Yusuf da kuma mai taimakawa Gwamnan Kaduna ta fuskar hulda da kafafen yada labarai Samuel Aruwan.

A jawabinsa yayin da suka ziyarci garin, Kwamandar rundunar soji ta Kaduna ya yi kira ga masu rike da sarautun gargajiya a yankin da su yi kira ga jama’arsu su zauna da juna lafiya.

Mista Mohammed ya roki al’ummar da su yi hakuri su zauna da juna lafiya su manta da duk wasu bambance bambance dake tsakaninsu, kuma su daina halaka dukiyoyin juna sabida sabanin ra’ayi.

ya kuma tabbatarwa da al’ummar yankin cewar jami’an tsaro suna nan zasu yi aiki babu dare babu rana wajen ganin an dawo da doka da oda a yankin.

A nasa jawabin, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Mista Austin Iwar, a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya tabbatar da kama mutane 18 da ake zargi da hannu wajen tayar da wannan rikici.

“Yanzu haka wadannan mutane suna hannunmu, kuma muna nan ana gudanar da bincike” A cewar kwamishinan.

A nasa banganren, Samuel Aruwan, ya bayyana cewar Gwamnatin jihar Kaduna ta yi maraba da labarin kame mutane 18 da rundunar ‘yan sandan jihar ta yi, yace zasu tabbatar an gurfanar da wanda suke da laifi gaban kotu.

Mista Aruwan ya bukaci al’ummar yankin da su yi hakuri su zauna da juna lafiya ba tare da tashin hankali ba.

Categories
Labarai

Majalisar dattawa ta yi tur da rikicin addinin da ya faru a jihar Kaduna

Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi Allah wadai da abinda ya faru na rikicin addini tsakanin Musulmi da Kirista a kasuwar Magani a yankin karamar hukumar Kajuru dake jihar Kaduna.

Haka kuma, Majalisar ta yi kiran da a rungumi juna a zauna lafiya tsakanin kabilu da bangarorin Musulmi da Kirista.

Hakan ya biyo bayan maganar da Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya kawo gaban majalisar inda ya nemi majalisar ta ja hankali.

Sanata Shehu Sani ya bayyana kashe kashen da cewar abin tur da Allah wadai da rashin sanin ciwon kai.

Haka kuma, Sanatan ya nemi a zauna lafiya a yi hakuri da juna, yace bai kamata mutane su dinga kone dukiyoyinsu da suka sha wahalar tarawa ba.

Ya bayyana cewar, sabani tsakani Musulmi da Kirista abu ne da za’a iya warware shi akan tebur ba tare da tashin hankali ko hatsaniya ba.

“Ya zama dole mutane su koyi yadda zasu zauna da juna lafiya” A cewar Sanata Shehu Sani.

Mataimakin SHugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu yayi kira da a zauna lafiya da juna tsakanin ‘yan Najeriya”

 

Categories
Labarai

Jam’iyyar APC ta amince Oyegun ya cigaba da jan ragamar ta na shekara daya

Shugaban jam’iyyar APC na kasa,  ya samu karin wa’adin cigaba da Shugabancin jam’iyyar na tsawon shekara guda.

An cimma yarjejeniyar amincewa da karawa Oyegun cigaba da kasancewa Shugaban jam’iyyar a wani taron masu ruwa da tsaki jam’iyyar da Shugaba Muhammadu Buhari ya halarta.

taron dai shi ne irinsa karo na farko a wannan shekarar da jam’iyyar ta yi tare da kwamitin amintattun jam’iyyar suka yi, wanda Ministoci da Gwamnoni da jiga jigan jam’iyyar APC daga jihohi 36 da suka halarci zaman.

Haka kuma, Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki bai halarci wannan zaman taron ba, wanda kakakin majalisar dokoki Yakubu Dogara ya halarta tare da mambobin majalisar dokoki ta tarayya.

Daga cikin wadan da suka halarci wannan taron har da Gwamnan Benuwai Samuel Ortom wanda a baya ya nuna ba zai halarci taron ba, sabida batun rikicin manoma da makiyaya.

Categories
Kanun Labarai

Shugaba Buhari ya yi fatali da dokar ‘Peace Corps’

Shugaba Muhammadu Buhari ya ki yadda ya sanya hannu kan dokar da ta samar da hukumar ‘Peace Corps’ wanda majalisar tarayya ta sahalewa a shekarar 2017.

Shugaban kasa, a wata wasika da ya aikawa majalisar dokokin tarayyar Najeriya, wadda kakakin majalisa Yakubu Dogara ya karanta a ranar talata, ya bayyana cewar rashin kudi da matsalolin tsaro sune uammul haba’isn din dalilin da ya sanya yaki amincewa ya sanya hannu.

Kudurin wanda ‘yan Najeriya da yawa suka jima suna dakon sanya masa hannu. Wanda ake sa ran samarda hukumar ta Peace Corps zata taimaka wajen rage aikin yi.

Categories
Taska

Shan ruwan kwakwa na rage hadarin kamuwa da cutar hawan jini

Wani sabon bincike ya tabbatar da cewar shan ruwan kwakwa yana rage hadarin kamuwa da cutar hawan jini da rage kiba.

Mista Ochuko Erikainrue masanin sinadarai da kuma tsirrai, shi  ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi a Legas kwanakin baya.

Ya bayyana cewar, ruwan kwakwa yana da matukar alfanu ga lafiyar dan adam, sabida yana da sinadarin kanwa a ciki, kuma tana taimakawa matuka wajen rage kamuwa da cutar hawan jini.

“Bincike ya tabbatar da cewar, ruwan kwakwa na taimakawa lafiyar jikin dan adam, kasancewarsa wani ruwa da Allah ya zuba shi cikin kwakwa”

“Ruwan kwakwa yana da gardi sosai, sannan kuma yana da sinadarai masu yawa a cikinsa wadan da suka kunshi sinadarin amino da bitamin B da C da sauransu”

“Ruwan kwakwa yana kara kuzari da kuma sanyawa jiki ni’ima”

“Haka kuma, ruwan kwakwa yana rage adadin kitsen da yake jikin mutum wanda yake iya zama cuta ga jikin dan adam”