Categories
Kanun Labarai

Shugaba Buhari ya gana da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Washington

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa fadar White Houe ta kasar Amurka, inda Shugaban Amurka Donald Trump ya marabce shi.

Yanzu haka Shugaba Buhari da Donald Trump suna wata ganawar sirri tsakaninsu.

Categories
Labarai

El-Rufai yayi Allah wadai da harin da ‘yan daba suka kaiwa Sanata Hunkuyi

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai yayi Allah wadai da harin da wasu ‘yan daba suka kaiwa Sanata Suleiman Hunkuyi,Sanata mai wakiltar Arewacin jihar kaduna a majalisar  dattawan Najeriya.

Gwamnan ya kuma gargadi dukkan ‘yan daban dake jihar da su sani cewar, Gwamnati ba zata lamunci irin wannan iskanci da keta mutuncin mutane da ‘yan daban suke yi ba.

A yayin da Sanata Hunukyi ke yin wani taron siyasa, ‘yan daba sun kutso kai cikin wajen taron inda suka dinga cewar “Sanata Sai Uba Sani’ wasu kuma na cewar ‘Kaduna Sai Malam’, haka dai matasan suka hargitsa wajen taron, inda suka farwa mutane da sara da suka.

A sanarwar da Gwamna el-Rufai ya bayar ta hannun kakakinsa, Samuel Aruwan, yayi Allah wadai da abinda aka yiwa Sanata Hunkuyi, ya kuma yi jajen abinda ya faru ga sanatan da tawagarsa.

Categories
Labarai

Dino ya dirgo daga motar ‘yan sanda ne saboda sun yi yunkurin halaka shi- Sanata Ben Bruce

Daga Hassan Y.A. Malik

Sanata mai wakiltar mazabar Bayelsa ta gabas, Sanata Ben Bruce a yau Litinin ya bayyana dalilin da ya sanya sanata Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya yi kuli-kulin kubura ya dirgo daga motar ‘yan sanda tana cikin tafiya a Abuja.

Melaye a makon da ya gabata ya tsirgo daga kan motar ‘yan sanda a sa’in tana cikin tafiya za ta kai shi jiharsa ta Kogi don amsa wasu tuhume-tuhume da ake yi masa na manyan laifuka.

 Lamarin ya yi sanadiyyar samun raunakan a jikin Dino dalilin da ya sanya aka kwantar da shi a sashen bayar da agajin lafiya na gaggawa na babban asibitin tarayya na Abuja.

Sanata Ben Bruce ya bayyana dalilin da ya sanya Melaye ya yi tsalle ya dirgo daga motar ‘yan sandan tana cikin tafiya.

“Sanata Melaye na fama da cutar asma, amma duk da haka bai sa ‘yan sanda sun ki fesa masa barkonon tsohuwa ba, wannan ya sanya dole ya tsirgo daga motar tasu don ya tserar da ransa.”

Sanata Ben Bruce ya bayyana ta shafinsa na twitter cewa dirowar da Melaye ya yi daga motar ‘yan sanda gudun ceton rai ne.

Ben Bruce ya rubuta: Yanzu na gana da @dino_melaye. Abin takaici ne jin abun da ya faru da shi. Dino na da cutar asma, amma sai ga shi ‘yan sanda sun fesa masa barkonon tsohuwa akan hanyarsu ta kai shi jihar Kogi, dalilin da ya sanya ya yi ta fama da numfashi. Da suka sake fesa masa barkonon sohuwar a karo na biyu ne ya sanya dole ya yi tsalle ya dirgo daga motar. Dino ya yi gudun tsirar da rayuwarsa ne daga hannun ‘yan sanda. Abin takaici!

 

 

Categories
Taska

Budurwa ta yanke mazakutar saurayinta, dan ya dauki bidiyonsu suna jima’i

Daga Hassan Abdulmalik

Wannan abun al’ajabin ya faru ne a kasar Argentina, inda aka gurfanar da matar mai Suna Brenda Barattin, bisa zargin datsewa al’aurar saurayinta saboda ya nunawa abokansa bidiyonsu da suka dauka a yayin da suke jima’i.

Barattini mai shekaru 26 da haihuwa, ta aikata wannan aika-aika ne a yankin Nueva Cordoba da ke kasar  Argentina a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, wanda hakan ya sa saurayinta dan shekaru 30 ya rasa kashi 90% na mazakutarsa, sannan ta saka shi cikin wani mummunan hali.

Barattini, wacce ta ke garkame a gidan yari ba tare da beli ba kafin saurarar karan ta a kotu, ta ce sakar bidiyon  da saurayinta, Sergio Fernandez, yayi ya jawo ma a raunin tabin hankali.

“Na yanke masa al’aurarsa ne amma ba ga baki daya: Na dan ji masa rauni ne. Ba duka na cire ba: na ji masa rauni ne kawa,” Baratinni  ta ce.

A halin yanzu dai saurayin na kwance cikin wani hali, inji lauyarsa, a yayin da ya ke jiran likitoci su yi masa aiki.

A cewar kafafen yada labarai na Fox News, ma’aikatan kiwon lafiya sun kasa dinke al’aurar Fernandez da budurwar  tasa ta cire.

Irin wannan lamari dai Ya faru akan, Loren Bobbitt, matar da ta yankewa mijinta mazakutarsa a shekar 1993 a yayin da ya ke bacci.

Bobbit ta ce ta yi hakan ne saboda mijinta na yi ma ta fyade.

Categories
Labarai

‘Yan sanda sun gayyace ni, na amsa kiransu, sun kuma bani belin kaina’ – Shehu Sani

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani ya bayyana cewar rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kaduna ta gayyace shi domin amsa tambayoyi kan zarginsa da ake yi da hannu kan wani kisa.

Sanatan Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook da Twitter “Inda yace da misalin karfe 10:45 na safiyar yau ne ya amsa gayyatar rundunar’yan sandan jihar Kaduna kamar yadda suka umarci ya bayyana a gabansu a wannan lokaci, inda kuma ya cika kiran da aka yi masa” A cewar Shehu Sani.

Ya kara da cewar, “Yan sandan su bani belin kaina, a matsayi na na wanda aka sani kuma aka tabbatar ba zan tsere ba”

Categories
Labarai

Najeriya zata harbo kumbu guda biyu sararin samaniya – NIGCOMSAT

Hukumar kula da yanayin sararin samaniyar Najeriya ta kasa NIGCOMSAT ta bayyana cewar nan ba da jimawa bane, Najeriya zata sake harba kumbo zuwa sararin samaniya tare da hadin kan wan kamfanin asar Chana..

Wani babban darakta a hukumar shi ne ya shaidawa babban kamfanin dillancin labarai na Najeroya, NAN, yau hakan a babban birnin tarayya Abuja.

Categories
Labarai

Kiranyen Dino Melaye: Gwamna Yahaya Bello ya magantu

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya magantu kan batun yiwa dan majalisar dattawa Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma a majalisardattawan Najeriya, Sanata Dino Melaye.

Gwamna Bello yace “Na karanta a kafafan yada labarai kuma na gani a talabijin, inda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta gudanar da aikinta cikin halin zaman lafiya a mazabar majalisar dattawa ta Kogi ta yamma”

Gwamnan yaci gaba da cewa, mambobin jam’iyyar APC a jihar, sun amince su goyi bayan Shugaba Buhari dari bisa dari a kakar zabe mai zuwa, saboda sonsa da zaman lafiya.

Ga dai Kalaman Gwamna Yahaya Bello cikin wannan Bidiyo da yayi cikin harshen turanci

Categories
Labarai

Mutane 6 da suka addabi jihar Katsina da fashi da garkuwa da mutane sun shiga hannu

Wasu mutum shida da ake zargi da aikata fashi da makami da kuma yin garkuwa  da mutane a hanyar Kaliyawa zuwa Mahuta a jihar katsina sun shiga hannu, bayan da aka yi batakashi tsakaninsu da jami’an ‘yan sandan jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina DSP Gambo Isah ya tabbatar da cewar, da misalin 05:00 bayan da aka tseguntawa rundunar ‘yan sandan jihar, suka tasarwa ‘yan fashin a hanyar Kaliyawa, inda suka ci nasarar kama ‘yan fashin.

Ya kuma kara da cewar, an ci nasarar samun bindiga samfurin AK47 guda daya tare da albarushi guda 19 da sauran kayan aikata ta’addanci a tare da ‘yan fashin.

Mutanan da aka kama su ne, Muntari Jibrin 25 da Dabo Hassan 60 da Abdullahi Alhaji Samu 20 da Tukur Mamman 20 da Babangida Sa’idu 27 da kuma Isyaka Yusuf 20.

Kakakin rundunar yace, mutanan sun amsa laifin cewar sune suke yin fashi da makami da kuma yin garkuwa da mutane a hanyar Katsina zuwa Zaria zuwa Funtuwa da yankin karamar hukumar Sabuwa da Dandume duk a jihar Katsina.

Yace ana cigaba da gudanar da bincike kan mutana, inda daga zarar bincike ya kammala za’a mika su gaban kuliya domin su fuskanci Shari’ah.

Categories
Labarai

2019: Nafi kowa cancantar yiwa jam’iyyar PDP takarar Shugaban kasa – Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar Shugabancin Najeriya a zaben 2019 dake tafe a shekara mai  zuwa, a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Shekarau wanda tsohon Ministan Ilimi ne, ya bayyana a wata wasika da ya aike mana, inda yake bayyana mana aniyarsa ta neman kujerar Shugabancin Najeriya idan jam’iyyarsa ta PDP ta bashi damar zama dan takararta.

Kamar yadda ya bayyana a wasikar da ya aike mana “Ina fatan kuna sane da cewar, tun bayan zaben 2015 da ya gabata, akwai kiraye kiraye daga mutane da dama ciki da wajen kasarnan, inda suke bukatar na tsaya takarar Shugabancin Najeriya a zaben da ke tafe na 2019, domin ceto halin da al’ummar kasarnan suke ciki”

“Na san mutane da yawa suna wannan kiran na tsayawa ta takarar Shugaban kasa ne, saboda yarda da amincewa da suka yi da ni, da kuma burin da suke da shi na ganin ni zan iya cire musu suhe daga wuta”

“A saboda haka ne, na zagaya dukkan sassan kasarnan guda shida, inda na zauna da mutane da abokai domin neman shawarwari da kuma nazartar halin da za’a tunkara idan halin fitowar yayi”

“Bayan wannan zagaye da neman shawarwari da na yi a dukkan fadin Najeriya, na gamsu da kiraye kirayen mutane, na kuma aminta cewar abinda ake fatan na yi zan iya yinsa, don haka ne na amsa kiran da al’ummar Najeriya suke yi min na fitowa takarar Shugaban kasa a zaben 2019 dake tafe” A cewar Malam Ibrahim Shekarau

 

Dailytrust.com

 

Categories
Kanun Labarai

‘Yan sanda sun tabbatar da fashewar Bom a gidan Shugaban Ohaneze a Enugu

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta tabbatar da fashewar Bom a yankin Ukehe a gidan Nnia Nwodo, Shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo, kungiyar dake fafutikar kare ‘yan kabilar Igbo ta Inyamurai zalla da sanyin safiyar Lahadi.

A sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, Ebere Amaraizu ya ce, tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ziyarci yankin da fashewar Bom din ta aukua Ukehe dake yankin karamar hukumar Igboetiti a jihar Enugu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Dan Mallam Muhammad, ya sha alwashin sanya kafar wando daya da duk wadan da suke da hannu wajen tashi wannan bom din a jihar ta Enugu.

Ya kuma sha alwashin ganin an bibiya tare da kamo wadan da suke da hannu wajen tayar da wannan Bom a gidan Shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo, kungiyar dake fafutikar kare Inyamura zalla.