Categories
Labarai

‘Yan Najeriya na caccakar hukumar EFCC kan batun Ramalan Yero

Mutane da yawa ne a shafukan sada zumunta na intanet suka ga baiken hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, kan yadda ta sanya hoton tsohon Gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero rike da wani allo da yake nuna shi mai laifi ne na cin kudade ba bisa ka’ida ba.

Mutane da dama ne suka caccaki hukumar ta EFCC akan abinda suka kira azarbabi da ta yi wajen kiran Ramalan Yero mai ‘laifi’ ba tare da kotu ta hukunta laifin da hukumar take zargin Ramalan Yero da aikatawa ba.

Har ya zuwa yanzu mutane na cigaba da caccakar hukumar EFCC kan batun inda da dama suka kira shi da tozartawa ga tsohon Gwamnan.

Categories
Kanun Labarai Labarai

Buhari ya sanya hannu a dokar baiwa matasa damar tsayawa zabe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya sanya hannu kan daftarin dokar da ta baiwa batasa damar tsayawa zabe.

Dokar dai ta tanadi rage adadin shekarun da dan takara ya kamata ya kai kafin ya tsaya zabubbuka a Najeriya.

Ko a lokacin da ya yi jawabin ranar Demokaradiyya ta Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya alkawarta sanya hannu a dokar nan ba da jimawa, alkawarin da ya cika shi yau Alhamis.

Dokar dai ta tanadi cewar an sauya shekarun tsayawa Shugaban kasa daga shekaru 40 zuwa 35, yayin da aka rage shekarun tsayawa takarar majalisar dattawa daga 35 zuwa 30.

Haka kuma, an rage shekarun tsayawa takarar Gwamna daga shekaru 35 zuwa 30, yayin da aka rage shekarun tsayawa takarar majalisun dokoki na jihohi da na tarayya daga shekaru 30 zuwa 25.

Categories
Labarai

Kotu ta bayar da umarnin tsare Ramalan Yero a kurkuku

Babbar kotun tarayya dake Kaduna a ranar Laraba ta bayar da umarnin cigabaa da tsare tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero a gidan kurkuku.

Ramalan Yero da wasu mutum uku suke tssare a hannun hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Alkalin kotun Mai Shari’ah Muhammad Shuaibu ya bayar da umarnin a cigaba da tsare mutanan har zuwa ranar shida ga watan Yuni.

Daga cikin mutanan da ake tsare da su akwai tsohon Minista Nuhu Wya da tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Kaduna, Hamza Danma’awuya da kuma tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Abubakar Haruna.

 

Categories
Kanun Labarai

Super eagles sun sha alwashin ciwo kofin duniya a Rasha 2018

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super eagles sun sha alwashin ciwo kofin duniya da za’a buga a Rasha 2018. Kungiyar ta bayyana hakan ne a lokacin da ta kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari caffa a fadarsa dake Abuja, yayin da suka je domin neman a sanya musu albarka kafin tafiyarsu zuwa kasar Rasha.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osbanjo ne suka tarbi tawagar ‘yan wasa, a yayin da suka kai ziyara fadar ta Shugaban kasa. Da yake jawabi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi musu fatan alheri da kuma fatan zasu ciwo wa najeriya kofin duniya a yayin gasar.

Suma a nasu jawabin,’yan wasan sun nuna jin dadinsu da kuma bayyana cewar zasu yi duk abinda zasu yi wajen ganin sun ciwowa Najeriya wannan gasa ta cin kofin duniya a kasar Rasha.

Categories
Labarai

‘Yan Kwankwasiyya na tururuwa zuwa Mundubawa domin jaje ga Malam Shekarau

A wani abu da ake gani ba safai ba, da kuma yake kara nuna dankon alakarsiyasa tsakanin Kwankwasiyya da Mundubawa, ‘yan Kwankwasiyya da dama ne suke tururuwa zuwa Mundubawa gidan Malam Ibrahim Shekrau Sardaunan Kano, domin yin jaje ga Sardaunan kan abinda suke cewar Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa na yiwa Malamin bita da kulli.

A makon da ya gabata ne dai hukumar ta EFCC tayi awon gaba da tsohon Ministan Ilimi Malam Ibrahim SHekarau kan batun kudaden da suke da alaka da zaben 2015, hukumar ta gurfanar da Malam Shekarau tare da Amb AMinu Wali da kuma Injinya Mansur Ahmed a gaban kotun tarayya dake Kano.

Dubban magoya bayan malam Shekarau da jam’iyyar PDP ne suka yi tururuwa a harabar kotun domin nuna goyo baya ga jagoran nasu Malam Ibrahim Shekarau, inda har sai da ta kai ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masuzanga zanagar nuna goyon baya a harabar kotun.

Bayan da aka bayar da belin Malam Ibrahim Shekarau ne, mutane da dama suke ta yin tururuwa zuwa gidan Malamin dake Mundubawa domin jajanta masa wannan abu da ya same shi, cikinmasu zuwa wannan ziyarar jaje har da ‘yan Kwankwasiyya magoya bayan tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ake ganin suna rungumar juna da Malam Shekarau.

Categories
Labarai

Sanata Marafa ya raba kayan taimakon jinkai a Zamfara

Dan majalisar dattawa mai wakiltar Zamfara ta tsakiya a majalisar  dattawan Najeriya, Kabiru Marafa ya rabawa iyalan wadan da aka kashe a hare haren da aka kai kananan hukumomin jihar Zamfara guda hudu kayan abinci da kudade.

Da yake kaddamar da bayar da kayan tallafin a Yandoton Daji, Kabiru Marafa ya bayyana cewar bayar da wannan tallafi ya zama dole domin ragewa mutanan da aka kashe musu ‘yan uwansu aka kuma yi musu hasarar dukiya, domin rage musu radadin halin da suke ciki.

Sanatan dai ya samu wakilci wani hadinmsa, Abubakar Dakta a wajen wannan bayar da tallafi, inda ya bayyana cewar, kananan hukumomin Tsafe da Gusau da Bungudu da Maru zasu raba buhunhunan shinkafa guda 1000, sannan kuma zasu kasafta Naira miliyan guda.

 

Categories
Labarai

Ramadan: Sheikh Dahiru Bauchi zai yi sauka ta 3 cikin shekaru 39 da ake tafseer

Sheikh Dahiru Usman Bauchi fitaccen malamin darikar Tijjaniyya zai yi saukar karatun Tafsirin AlKurani mai girma da yake gabatarwa a jihar kaduna.

A wannan shekarar ne dai kafin karewar wannan wata ake sa ran shehun Malamin zai yi saukar karatun Tafsirin, wanda kuma ita ce karo na uku da za’a sauke karatun tafsiri tun kusan shekaru 39 da ya dauka yana gudanar da Tafsirin a Kaduna.

Bayanai sun bayyana cewar, za’a yi wannan saukar ne a bana, tun bayan wadda aka yi shekaru goma sha biyu (12) da suka gabata da aka yi.

Sheikh Dahiru Usman bauchi dai ya fara gabatar da Tafsirin Alkurani mai tsarki ne tun kusan shekarun 1951, kimanin shekaru 67 da suka wuce.

Categories
Labarai

Gwamnatin jihar Neja ta kashe naira biliyan 4.3 don yiwa makarantu 9 kwaskwarima

A ranar Larabar nan, Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya bayyana cewar, Gwamnatinsa ta kashe zunzurutun kudi Naira biliyan 4.3 domin yiwa makarantu guda 9 kwaskwarima a fadin jhar a wani shiri na inganta makarantun Gwamnati da gwamnatinsa ta bullo da shi.

Gwamnan ya shaidawa manema labarai cewar an kashe kudaden ne wajen gyara ajuzuwan da suka lalace da gyaran bandakuna da sanya kujeru a makarantun da kuma yi musu fenti.

Yakara da cewar Gwamnatin kuma ta samar da wasu kayayyakin aikin domin amfanin malaman makarantu da suka hadar da kayan lantarki da dangoginsu da kuma kujeru da tebura.

“Alokacin da muka shigo Gwamnati a 2015 mun tarar da komai kusan ya lalace,ko yana gab da durkushewa, muna da makarantun da kusan shekaru 40 basu taba ganin fenti ba, dan haka muka gyara irinsu”

“Mun tarar da wasumakarantun babu bandakuna, wasu ajujuwan sun rushe, awasu makarantun kwana kuwa, wasu babu dakunan dafa abinci da kuma inda yara zasu ci abinci, sannan dakunan kwanan duk sun lalace”

“Taya kuke zaton zamu iya samar da jagorori na gari a irin wadannan lalatattun makarantun da yara basa samun yanayin koyo mai kyau?”

 

 

Categories
Labarai

Wani dan majalisar wakilai ya kuma ficewa daga APC zuwa PDP

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kachia da Kagara a majalisar wakilai ta kasa, Adams Jagaba ya bayyana sauya shekarsa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP mai adawa.

Dan majalisarwanda ya fito daga jihar Kaduna, ya bayyanawa kakakin majalisar Rt. Hon. Yakubu Dogara a zauren majalisar cewar ya sauya sheka ne daga APC zuwa PDP saboda yaddaake rashin gaskiya da kuma yadda jam’iyyar take cigaba da dakatar da shi na daga cikin dalilansa na komawa PDP.

 

Categories
Kanun Labarai

Sanata Dino Melaye ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Sanata Dino Melaye dan majalisar dattawa mai wakitar jihar Kogi ta Yamma a majaisar dattawan najeriya ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyarsa ta APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

A cewar jaridar The Nation dan majalisar dattawan Dino Melaye ya bayyana ficewarsa ne daga jam’iyyar APC zuwa PDP a zauren majalisar dattawa a zamanta na ranar Laraba,inda ya bayyana cewar jam’iyyar ta PDP ta yi masa alkawarin kujerar dan majalisar dattawa.

Dino Melaye ya halarci majalisar a yau Laraa bayan da ya shafe kwanai bai halarci zaman majalisar ba, daga nan kuma yayi godiya ta musamman ga abokansa ‘yan majalisar da uma takwarorinsa dake majalisar wakilai a bisa yaddasuka nuna masa kauna lokacin da yake fuskantar kalubale.

Daga nan kuma, Dino Melaye yayi godiya ga shugabancin jam’iyyar PDP na kasa a bisa yadda suka nuna masa kauna da soyayya a lokacin da yake fuskantar kalubale.

Dagakarshe Dino Melaye ya roki Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da ya samar masa da kujera a cikin ‘yan adawa na majalisar domin komawa cikinsu.