Categories
Labarai

Gwamnatin Bauchi ta raba butocin alwala 10,000 ga Masallatai a fadin jihar

Gwamnatin jihar Bauchi ta hannu Mai tallafawa Gwamnan Bauchi M A Abubakar akan kungiyoyin da bana Gwamnati ba da abokan kawo cigaba Alh Mansur Manu Soro ya bada sadakar butocin alwala har guda dubu goma (10,000) ga masallatai a fadin jihar Bauchi.
Mai tallafawa Gwamna ya mika butocin ga babban limamin masallacin Juma’a na Kofar Gombe kuma Shugaban Hukumar Gudanarwa na Kwalejin Sharia da Musulunci dake Misau Sheikh Dr. zubairu Madaki domin rarrabasu ga masallatai.
Da yake karbar butocin, Sheikh Zubairu Madaki yayi addu’ar Allah Ya saka masa da alkhairi ya kuma yi alkawarin raba butocin ga masallatai daban-daban.
Categories
Kanun Labarai

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Togo a jihar Katsina

Shugaban kasa Muhammadu BUhari a masaukinsa dake gidan Gwamnatin jihar Katsina, inda yake karbar bakuncin Shugaban kasar Togo Faure Gnasinbe Iyadema.

SHugaban na kasar Togo na yin wata ziyara ne a Najeriya, ina yazo daidai da ziyarar da Shugaba Buhari ya kai jiharsa ta Katsina.

Shugaba Buharin ya karbi shugaban na kasar Togo ne a jihar ta Katsina maimakon birnin tarayya Abuja.

Categories
Raayi

Allah ɗaya gari bamban

Daga Mansur Sokoto
Yau na yi Sallar jum’ah a Masjidus Salam babban Masallacin garin Yamousokrou ta kasar Cote d’Ivoire wanda shugaban kasarsu na farko Felix Houphouet ya gina masu tare da babbar Coci wadda ita ce ta farko ga girma a duniya bayan ta Fafaroma.
Abin mamaki na farko da na gani shi ne yadda aka rako limamin Sheikh Aboubacar Fufana cikin kwambar jama’a suna rera wasu wakoki kamar ana karatun Alkur’ani.
Da shigowar sa ladanin kofar yamma ya fara kiran Sallah shi kuma liman ya dale kan minbari. Yana kammalawa sai ladanin kofar kudu shi ma ya fara nasa kiran Sallar. Da kammalawarsa ladanin kofar arewa ya rera nasa. Hakika da a radio na ji kiran Sallarsu da ba zan gane shi ba domin wata irin waka ce kawai kake ji ana rerawa. Sai an zo karshe sai ka ji Masallacin ya dauka da Sallallahu alaihi wasallam.
Daga nan liman ya hau minbari. Ni ban sani ba da yaren kasarsu ne yake hudubar ko da Faransanci? (Suna da yaren: Abron da Agni da Cabaara Sanufo dss). Amma dai na gane “wattaqullaha” da kuma “kasratuz zunub”… da wasu kalmomi kadan na larabci da ya rika jefawa ko wasu nassoshi da ya kafa hujja da su. A jima kadan kuma sai in ji ana ta ce masa Amin, ni ma sai in ce Amin don kada a bar ni a baya.
Yanzu idan a Najeriya wani limami kuma babba irin wannan ya yi huduba ba da larabci ba za a kwashi rikici wanda sai shekara ta zagayo ba a kare ba kamar dai ita ma huduba irin Alkur’ani ce da ake neman tabarruki da lafazinsa.
Kada ka ce limamin ba ya jin larabci domin yana cikin taron limamai da muke yi kuma na sa shi ya yi larabci mai tsawo kuma mai kyau sosai. Haka ma karatun sallarsa lafiya kalau.
Da ya kare huduba sai ladan ya yi wata hargowa “Safa! Safa!” Sannan aka ta da Sallah aka gama aka yi addu’a.
Masallacin dai kam ya lashi manyan kudi duk da yake an dauki shekaru masu yawa da yin sa amma an zane bangayensa da ginshikansa da wani irin ado mai ban sha’awa irin wanda yake cikin tsohon Masallacin Madina. Abin ban mamaki ace ba Musulmi ne ya gina shi ba.
Asali dai ni na zo halartar taron limamai na Afrika ne da yake gudana yanzu haka a wannan garin wanda ISESSCO ta shirya. Amma na fahimci Allah ne ya hukunta zuwa na domin in karu da albarkar tafiya saboda duk kasashen da aka gayyato masu jin Faransanci ne kawai, kuma sanya ma’aikatar ilimi ta kasar a cikin shirin ya sa aka juya akalar shirin gaba daya zuwa Faransanci.
Amma daga bisani na samu canja yanayin bayan lurar cewa duk limamai ne masu jin larabci kuma aka samu gyara muka koma tattaunawa da harshenmu na Musulunci da ya hada mu.
Fa’ida ta biyu samun haduwa da yan uwa Hausawa da na yi wadanda suka kira ni har unguwarsu na gabatar masu da karatu a daren jiya duk da ruwan sama da ake yi. Yan uwanmu Hausawa na Abidjan tuni sun samu labarin zuwa na tun sauka ta a Airport kuma suna dakon ko zan isa da wuri yau bayan rufe taro domin su ma mu gaisa da su.
Bisa gaskiyar magana, Musulmi yan Najeriya wajibi ne mu gode ma Allah bisa karfin addinin Musulunci da watsuwar karatun Sunnah a cikin mu. Mun wuce wadannan kasashe na faranshi ba kadan ba. Malamai kuma kalubale ne babba a gurguso nan a isar da Da’awa. Allah ya yi muna dace.
Categories
Labarai

Amnesty: Mutum 1,800 aka kashe a Najeriya a wata shida

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana damuwa game da yawan kashe-kashen jama’a a Najeriya, inda ta ce an kashe fiye da mutane 1,800 a bana kawai.

Ta ce ba ta jin dadin yadda ake samun asarar rayuka sanadiyyar rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, da na kabilanci, da hare-haren ‘yan fashi, da kuma rikicin Boko Haram.

Sai dai kungiyar ta dora alhakin yawaitar hare-haren da kuma mayar da ramuwar gayyar kan gazawar hukumomin tsaron kasar.

Wata sanarwar, wadda mai magana da yawun kungiyar a Najeriya, Isa Sanusi, ya sa wa hannu, ta ce akalla mutum 1,800 ne aka halaka daga watan Janairun da ya gabata zuwa Yuni a jihohi 17 na kasar.

Kuma adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya zuwa yanzu, “ya nunka na gaba dayan shekarar da ta gabata, wanda aka kiyasta cewa ya haura 800,” a cewarsa.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce duk da kalubalen tsaron da ake fuskanta gwamnatinsa ta “cimma muhimman nasarori” a fannin.

Har ila yau kungiyar ta ce a al’amari na baya-bayan nan da ya auku a jihar Filato, ‘yan bindiga sun kai wa kauyuka 11 hari a ranar Asabar da ta gabata, suka kwashe tsawon sa’o’i bakwai suna ta’adi, inda suka kashe mutane akalla 200 a kauyukan.

“Kuma jama’ar wuraren ba su samu wani dauki daga jami’an tsaro ba.” Al’amarin da kungiyar ta bukaci a gudanar da bincike a kansa.

Duk da cewa an tura rundunonin tsaro, ciki har da sojoji, a jihohi fiye da 30, karuwar wadannan hare-hare suna nuni ne da cewa, duk wani mataki da hukumomin Najeriya ke dauka ba ya yin tasiri, a cewar kungiyar.

Daga nan, kungiyar ta jaddada bukatar gwamnatin Muhammadu Buhari ta gaggauta daukar matakin hukunta mutanen da ke da alhakin wannan ta’adi da aka yi a jihar Filato.

BBCHAUSA.COM

Categories
Labarai

‘Na gayawa Kwankwaso zai kwashi kashinsa a hannun Ganduje – Kawu Sumaila

Hon Kawu Sumaila ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa shi da kan sa ya gaya wa tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso cewa kada ya yi karfa-karfa wajen dora dan takara ba tare da an bi yadda doka ta gindaya ba amma akayi watsi da wannan shawara tasa, gwamnan ya dora wanda yake so.

“ Ina so in gaya muka ka sani, wannan magana na yi ta nanata shi. Lokacin da aka kafa APC na bada shawarar a tabbata an bi doka wajen dora shugabannin jam’iyya da zaben ‘yan takara. Amma maimakon abi wannan shawara sai aka koma aka ci gaba da yadda dama can ake yi a jam’iyyar PDP, jiya Iyau tun da dama can mun sani ba zai hafi da mai ido ba.

“ Haka akayi a lokacin zaben fidda dan takara, gwamnoni suka dora wadanda suke so, akayi watsi da yadda dokar jam’iyya tace abi ba.

” A lokacin na jawo hankalin gwamna Kwankwaso cewa ya bi doka, kada yace zai ba na kusa dashi amma ya ki ji na. Na ce masa idan ya dora na kusa dashi, ba za a sami dasawa ba.

” A wancan lokaci har Ina ba da misali da yadda ta kaya tsakanin wasu gwamnoni da suka yi irin haka amma ba a gama lafiya ba kamar Aliero da Dakingari, Ali Saadu Da Sule Lamido, Saminu Turaki Da Sule Lamido da dai sauran su. Dama mun yi wannan hasashen kuma hakan ya faru.

Hon Sumaila ya kara dacewa duk da wannan matsala da aka samu, shi yana tare da gwamman jihar Kano ne wato Abdullahi Ganduje ba Kwankwaso ba.

“ Yanzu kam Ina tare ne da Ganduje saboda yana tare da Buhari. Amma fa Buhari ne ya hada mu. Kaunar da yake wa Buhari shine yasa nima nake kaunar sa. Dama can tare ya zo ya same mu tun a lokacin da baya yin Buhari har yazo yana yin sa yanzu kaga dole muna tare kenanan.

Da yake amsa tambayar ko ficewar kwankwaso a APC zai iya yi wa jam’iyyar Illa, sai yace tabbas rasa dan siyasa a jam’iyya ya kan yi wa jam’iyya Illa tunda ita siyasa da yawanku ne kuke cin zabe, saboda haka kowa so yake ya samu karuwar mutane ba raguwa ba.

HAUSA.PREMIUMTIMESNG.COM

Categories
Tarihi

Tarihi: Labarin Malam Mudi Spikin da wani Ɓarawo

Daga Fatuhu Mustapha
Wata rana malam Mudi Spikin ya dawo gida kawai sai ya hangi kofar gidansa cike da mutane ana ta hayaniya.  Nan da nan ya karasa da sauri domin yaga me ke faruwa, isar sa ke da wuya , ya tambayi wani mutum dake wurin, “me ke faruwa ne!” Mutimin yace masa ai barawo aka  kama ya saci buhun hatsi a gidan nan. Malam Mudi yace “subhanalLahi!” A gidan nawa?! Jin cewa shine maigidan yasa aka bashi wuri. Mutane kowa rike da makami, wasu na a miko shi mu gama masa aiki, wasu na a bari a kirawo yandoka.
Malam Mudi na shiga soro, yace ina barawo, aka ce masa gashi. Sai ya kalli barawo, yace masa ( cikin fada), “kai yanzu haka mu kayi da kai? Na gaya maka nima buhu guda ne, ya rage min a gidan nan, kuma ina da iyali, kuma ma ai cewa nayi in kazo kayi sallama, kace a auna maka rabin buhu, sai kawai kazo ka sunkuci buhu guda!!” Nan kuwa malam Mudi bai taba ganin barawo ba.
Nan kuma jikin kowa yayi sanyi, wani makwabcinsa yace ma, malam Mudi, “dama kai ka aiko shi?” Wani kuma ya kalli barawo, yace masa “kai ai sai kayi bayani, amma da kayi shiru, ai da tuni min gama maka aiki”
Nan da nan malam Mudi ya saka aka kawo kwanon awo, ya farke buhun nan da ya rage masa, ya aunawa barawo kwana 2o. Ya kulle ya daurawa barawo aka, har zai wuce, sai ya sanya hannu a aljihu ya dauko anini biyu ya mika masa, yace masa ga wannan in kaje kayi cefane, kasan uwargida sai da dan abin masarufi.  (Sai kace ya taba saninsa).
Tun daga ranar barawon nan ya tuba da sata.
Kaico! Ko yau a Arewa zamu samu dattawa irinsu malam Mudi Spikin? Allah ya jikansa da gafara!!
Categories
Raayi

Shaye shaye tsakanin matasa na neman zama ruwan dare

Daga Ayeesh A. Sadeeq

ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Shaye-shaye ya zama ruwan dare a tsakanin matasan wannan zamanin, abin al’ajabi da mamaki bai wuce yanda gaba daya jinsin wato maza da mata ke tu’ammali da kayan maye.

Da yawan su hakan ya faro asali ne daga abokan da su ke mu’amala da su. Mafi yawancin iyaye da malamai na matukar kokari wajen ganin sun nuna ma matasa illar da ke tattare da shaye-shaye. Sai dai akan yi rashin sa’a da wasu iyayen da ke bada gudunmuwarsu wajen lalacewar yaransu.

A matsayinmu na matasa akwai buƙatar mu san wadanne abokai ya kamata mu yi hulda da su, kamar yadda bature ke cewa “Show me your friends and I’ll tell you who you are”. Wasu zasu taso da kyakkyawar tarbiyya, sai dai kash! Abokan da suke haduwa dasu kan gurbata wannan kyakkyawar tarbiyya.

Akwai matsalar nan ta da yawan iyaye basu damu da sanin abokanan ƴaƴansu ba, idan aka yi rashin sa’a sai yaran su hadu da abokanan banza, daga nan halayensu na kwarai kan canza.

Wasu daga cikin yaran kan iya bakin kokarinsu wajen ganin sun nusar da abokansu illar shaye-shaye da suke yi, sai ayi rashin sa’a abokan sun yi nisan da ba sa jin kira. Maimakon wadancan na kwaran su rinjayesu sai na banzan su rinjaye nagari, shi kenan sai su taru su zama daya.

Babu dalilin da zai sa ka yi mu’amala da mutumin banza, idan ya zama dole to ka nisance shi sai idan akan abin da ya zama dole ne, hira tsakaninku ta zama ragagga.

A matsayin ka na matashi babu amfanin ka sha abinda zau gusar ma da hankali, ya sa ka fita hayyacinka, dadin da za ka ji na kankanin lokaci ne, amma illar da hakan zai haifarma har karshen rayuwa ne. Ka zubar da mutuncin gidanku, da naka. Ka bata rayuwarka a banza a wofi, ka zama ja baya a cikin abokanan ka, watakila kuna aji daya dasu a dalilin shaye-shaye su wuce ka a karatu, wasu har su cimma burinsu, kai ba ka tsinana ma rayuwarka komi ba.

Sannan ita kanta gangar jikinka a cikin hadari take, gaba daya za ka canza lafiya za tai maka karanci, banda yiwuwar rasa hankalinka kacokam a kowane lokaci ba tare da notis ba.

Daga lokacin da ka fada shaye-shayen miyagun kwayoyi daga lokacin kayi maraba da miyagun halaye, kadan daga cikinsu akwai sace-sace saboda kudin da za ka yi amfani da su wajen siyen kayan maye.

A duk inda ka san za ka zauna ya zama cikin mutanen kwarai ka ke zaune, sannan ka sama zuciyar ka tsanar shaye-shayen miyagun kwayoyi, sannan ka san irin abokan da za ka yi hulda da su, ko da ka ji sha’awar yin hakan ka tabbatar ka kaurace ma hakan.

Sannan iyaye ku sa ido akan ƴaƴanku, su waye abokanan su, ina suke zuwa. Wasu iyayen na da matsalar ƙin yarda da ƙarar da ake kawowa na yaran su. Wasu zasu nuna cewa an yi ma yaransu sharri basa shaye-shaye, akwai wadanda ke daukar cewa yaransu ba shaye-shaye suke yi ba asari ake ma su, ko kuma aljanu ne ke shafarsu.

Ya kamata iyaye su hankalta duk inda mutum daya, biyu, uku zai kawo ma shaidar danka ko yarka to ka bincika ks gano gaskiyar zancen ta hakan za ka daƙile abin. Amma daga zaran kayi kunnen uwar shegu da lamarin, daga lokacin ne yaran zasu yi kamari akan mummunan abun da suke yi har ya zamo ba za ka iya shawo kan abin ba.

 

Categories
Raayi

Kira zuwa ga Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

Daga Yasir Ramadan Gwale

A jiya Alhamis fadar Shugaban kasa ta sanar da cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kashe Naira biliyan goma don tallafawa iyalan wadan da suka rasa ‘yan uwansu a kashe kasugaban kasa hen da aka yi a jihar filato.
Anan nake amfani da wannan dama nayi kira ga Shugaban kasa da yaji tsoron Allah, ya sani zai kasance abin tuhuma a gaban Allah kan nauyin da aka dora masa na al’ummar Najeriya.
Shugaban kasa ya sani babu wani ran dan Najerya da yafi wani. An kashe mutane bila adadun a jihad Zamfara fiye da wannan da ya faru a jihad Fikato, an kashe a Birnin Gwari an kashe a Taraba an kashe a gurare da dama.
Amma duk wadancan kashe kashe da suka auku musamman na Zamfara ba su da kimar da Shugaban kasa zai taimakawa iyalansu da biliyan goma? Shugaban kasa kaji tsoron Allah, babu wanda yafi wani a wajenka a matsayinka na Shugaban kasa.
Bai kamata Shugaban da aka fi yi masa zaton kamanta gaskiya da adalci ya dinga nuna wqriya irin wannan ba, lallai muna kira ga Shugaban kasa yadda aka warewa mutanan jihar Filato biliyan goma suma na jihar Zamfara da aka yi musu kashe kashe a ware musu biliyan goma.
Ifan Shugaban kasa yayi haka ya tabbata shi mai son kamanta gaskiya ne da adalci, rashin yin haka kuwq, nuna fifikon wasu al’umma ne akan wasu, wanda bai kamaci Shugaban kasa yayi haka ba.
Sannan muna kuma kira da a dayki dukkan matakan da suka dace domin kare alfarmar rayukan ‘yan Najeriya a ko ina suke. Allah ya bamu lafiya da zama lafiya, ya baiwa Shugabanninmu ikon kqmanta adalci.
Categories
Kanun Labarai

Mutane 19 sun kone, motoci 50 sun kone a yayin da tankar mai ta kama wuta a Lagas

Akalla mutane 19 ne suka kone kurumus yayin da sama da motoci 50 suka kama da wuta a wani mummunar fashwa da wata motar dakon mai tayi a jihar Legas a ranar Alhamis akan gadar Otedola dake unguwar Alausa a jihar Legas.

Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas, Kahinde Adebayo ya tabbatar da faruwar wannan al’amari ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, inda ya  bayyana cewar mtane hudu sun samu munanan raunuka a sanadiyar wannan hadari.

Adebayo ya bayyana cewar motar dakon mai dake dauke da man fetur Lita dubu 33 ita ta fashe kuma ta kama da wuta, inda nan take motocin dake gefe sama da 50 suka kone kurmus da misalin karfe 5:23 na yammacin ranar Alhamis.

 

Categories
Labarai

Gwamnatin Katsina zata kashe M60 don taimakawa wanda iska ta yiwa barna

Gwamnatin jihar Katsina ta ware zunzurutun kudi Naira miliyan 60 domin taimakawa wadan da suka hadu da ibtila’in iska mai karfi tare da ruwan sama mai yawa da yayi mussu ambaliya ya lalata mus gidaje da muhalli a fadin jihar.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar SEMA, Aminu Waziri ne ya sanar da hakan ranar Alhamis ga manema labarai a Katsina.

Ya bayyana cewar za a sayi kayan tallafin ga wadan da abin ya shafa a garuruwan Chiranchi da Mashi da Katsina da kuma Musawa d Batagarawa domin tallafa musu rage radadin da suke ciki na asarar da suka yi.