Categories
Labarai

Yakin cacar baki ya kaure tsakanin Bukola Saraki da Sanata Abdullahi Adamu

AN shiga yakin cacar-baki tsakanin Shugaban majalisardattawa Bukola Saraki da Sanata Abdullahi Adamu tsohon Gwamnan jihar Nassarawa.

Ana musayar yawu ne tsakanin manyan Sanatocin biyu, sakamakon zargin da Abdullahi Adamu yayi na cewar Saraki na magana a bayan idon Dino Melaye, inda Saraki ya maida martani da cewar Abdullahi Adamu makaryaci ne.

Daga isani kuma Abdullahi Adamu yayi ikirarin cewar Sanata Bukola Saraki na yin zagon kasa ga Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Inda ya nemi Saraki da ya nemi afuwar Shugaba Buhari akan yadda ya dinga kwasar zunubbansa yayin da Buharin ke kwance a asibiti a kasar Burtaniya.

 

Categories
Labarai

Ibeto jakadan Najeriya a Afurka Ta-Kudu yayi murabus, ya koma PDP

Ahmed Musa Ibeto wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin jakadan Najeriya a kasar Afurka Ta-kudu yayi murabus daga mukaminsa, sannan ya sauya sheka zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP.

Ibeto dai shi ne tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Neja, inda ya sauka tare da Gwamna Muazu Babangida Aliyu Talban Minna a shekarar 2015. Kafin dai karewar  Gwamnatinsu ne dai Ibeto ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Inda Shugaba Buhari ya zabe shi a matsayin Minista daga jihar Neja,kafin daga bisani a maye shi da Bawa Bwari daga jihar ta Neja. Daga baya ne kuma bayan da aka janye sunansa daga matsayin Minisa, aka bashi mukamin jakadan Najeriya a kasar Afurka ta-kudu.

Wata majiya mai tsuhe ta tabbatar da cewar, Ahmed Ibeto zai tsaya neman takarar Gwamnan jihar Neja a karkashin tutar jam’iyyar PDP, inda ake sa ran zai yanki tikitin shiga jam’iyyar ta PDP a mazabarsa dake Ibeto a karamar hukumar Magama ta jihar Neja.

Categories
Kanun Labarai

An hadu tsakanin Kwankwaso da Ganduje ba tare da anyi magana ba

Yau Talata aka yi wata haduwa ta bazata tsakanin Kwankwaso da Ganduje a gidan Janar Aliyu Mohammed Gusai mai ritaya yayin da aka yi jana’izar mai dakinsa da ta rasu a kwanakin baya.

An hadu ne tsakanin Kwankwaso da Ganduje a makabarta yayin da aka je binne matar a makabarta. Sai dai kuma har aka watse babu wanda ya yiwa wani magana tsakanin manyan ‘yan siyasar biyu.

Categories
Labarai

Sauya sheka daga APC zuwa PDP ko a jikina – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar saya shekar da ake yi daga APC zuwa jam’iyyar PDP ko a jikinsa, yace sam abin bai dadara shi da kasa ba, Shugaban ya bayyana hakan ne a dare jiya Lahadi.

Shugaba Buhari yayi wannanjawabi ne a lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan Najeriya dake kasar Togo lokacin da ya kai ziyara ofishin jakandancin Najeriya dake birnin Lome a kasar Togo din.

Garba Shehu kakakin fadar Shugaban kasa, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ruwaito Shugaba Buhari yana mai cewar, ‘yan Najeriya da yawa na yabawa kokarin Gwamnatinsa tare kuma da nuna gamsuwa da ita.

 

 

Categories
Labarai

Sai da na haye bishiya domin gujewa masu yunkurin garkuwa da ni – Dino Melaye

Dan majalisar dattawa ta jihar Kogi Sanata Dino Melaye, ya bayyana yadda aka so yin garuwa da shi a yankin Gwagwalada dake babban birnin tarayya Abuja akan hanyarsa ta zuwa Lakwaja domin halartar kiran da kotu ta yi masa a ranar Alhamis.

Dino Melaye wanda dan majalisar dattawa ne, ya bayyanawa manema labarai a Abuja cewar, sai da ya fita a guje ya shige daji, sannan ya haye bishiya domin tsirar da rayuwarsa daga wadannan miyagun mutane.

Yace ranar Alhamis da sassafe ya bar Abuja domin zuwa Lakwaja don amsa kiran kotu, amma a hanyarsa ta tafiya ya lura da wata mota Toyota kirar Siyana tana biya da shi a baya, daga bisani kuma mutanan suka budewa motarsa wuta, inda suka yi yunkurin yin garkuwa da shi.

A ranar Talatar da ta gabata ne dan majalisar dattawa Dino Melaye ya koma jam’iyyar PDP mai adawa daga jam’iyyar APC, yana cikin jerin mutane 15 da Shugaban majalisar  dattawa Bukola Saraki ya bayyana komawarsu jam’iyyar PDP a zauren majalisar dattawa.

 

 

Categories
Labarai

Majalisar dokokin jihar Binuwai ta yi barazanar tsige Gwamna Ortom

‘Yan majalisu 8 cikin guda talatin na majalisar dokokin jihar Binuwai sun sanya hannu kan takardar tsige Gwamnan jihar Samuel Ortom.

Tuni dai ‘yan majalisar guda takwas suka karbe ikon majalisar dokokin jihar, inda yanzu haka suke samun kariya daga rundunar ‘yan sandan jihar,kamar yadda Tahev Agerzua kakakin Gwamnan jihar ya shaidawa jaridar Premium Times.

Zamu kawo cikakken bayani nan gaba kadan.

Categories
Kanun Labarai

An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Kano Abdullahi Ata

Da sanyin safiyar Litinin din nan ne ‘yan majalisar dokokin jihar Kano, suka tsige kakakin majalisar dokokin jihar Kano Alhaji Abdullahi Ata. Tuni kuma aka maye gurbinsa da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kabiru Alhassan Rurum, wanda aka tsige kwanakin baya.

 

Categories
Labarai

Ficewar Kwankwaso daga APC ba zata ragemu da komai ba – Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa ficewar tsohon gwamnan jihar Rabiu Kwankwaso ba t ta tada wa kowa hankali a jihar Kano ba, hasali ma mutane murna suka yi ta yi.

” Ficewar sa da sauran wadanda suka fice daga jam’iyyar APC ba bai dada mu da kasa ba, ina so in sanar wa mutane cewa su bude idanuwar su suga yadda za muyi da su a lokacin zabe.

Ganduje ya kwarmata wa a manema labarai haka ne a hira da yayi da su a Kano ranar Juma’a.

” Ina so ku zo Kano ku gani ko akwai wani abu da ake yi wai don Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar APC, kowa na ci gaba da hidimomin sa ne kawai kamar ma ba aji ba.

” Dama can Kwankwaso na so yayi takarar shgaban kasa ne amma da ya tabbatar hakan ba zai yiwu ba sai ya fice daga jam’iyyar sannan Ina so in tabbatar muku cewa jihar Kano za ta ba Buhari kuri’un da bata taba bashi ba a zaben 2019.

Idan ba a manta Sanatoci 15 ne suka yi fitar burtu suka tsallaka zuwa jam’iyyar PDP.

Hausa.Premiumtimesng.com

Categories
Labarai

Mata 30 suka haihu a sansanin ‘yan gudun hijira dake Sakkwato

A kalla mata 30 ne suka haihu a sansanin ‘yan gudun hijira dake Gandi a jihar Sakkwato, su dai wadannan ‘yan gudun hijira sun fito ne daga kauyen Tabanni dake yankin karamar hukumar Rabah a jihar ta Sakkwato.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Sakkwato Alhaji Ibrahim DIngyadi shi ne ya bayyana hakan ga mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Saad Abubakar na uku a lokacin da ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijirar.

“A kalla akwai ‘yan gudun hijira 4,996 da suka fito daga kusan kauyuka tara na jihar Sakkwato bayan da ‘yan ta’adda suka farma garuruwansu da hare haren ta’addanci”

Dingyadi ya bayyana kauyukan da ‘yan gudun hijirar suka fito kamar haka: Tabanni da Gidan-Kare da Kursa da Warwasa da Rumbun-Tsamiya da Tudun-Kwasa da Dutsu da Illilu da kuma ‘Yankusar-kilawa.

Categories
Labarai

Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara ya ja hankalin Gwamnatin tarayya kan batun tsaro

Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Sanusi Rikiji a ranar Asabar ya ja hankalin Gwamnatin tarayya kan batun sha’anin tsaro a jihar da ya tabarbare.

Sanusi Rikiji, wanda kuma shi ne Shugaban kwamitin bayar da agajin gaggawa na jihar, yayi wannan kiran ne a fadar mai martaba Sarkin Zurmi, lokacin da yake magana kan abinda ya faru na kashe sama da mutane 42 da kauyuka 18 dake yankin karamar hukumar mulkin Zurmi.