Categories
Labarai

Wasu matasa sun yi takakkiya akan keke don jaddada goyon bayansu ga Takai

Daga Muhammad Bashir Amin

Wasu Matasa masu kaunar Dan takarar gwamna jihar Kano karkashin inuwar tutar Jam’iyyar PDP Mal. Salihu Sagir Takai Sun Tuko keke daga Kauyen Kachako Cikin Karamar hukumar Takai don jaddada goyan bayansu ga takarar Takai 2019.

Da Muke zantawa da Shugaban tawagar Mahaya Kekunan Nazifi Nagge Kachako, ya bayyana cewa sun tawo su uku akan Keke tun daga kauyensu Na Kachako kuma zasu koma akan Kake kamar yadda suka tawo, kuma sun ci Alwashin ci gaba da kawo irin wannan Ziyarar akan Kekunansu duk ranar Juma’a har sai an bayyana Takai a matsayin gwamnan jihar Kano a Zaben 2019, ya kuma ci gaba da cewa ba iya su kadai ba ne Kungiya ce da su guda, yanzu su Shugabannin ne suka fara bude kofa a yau Juma’a 31/08/2018.

Garin Kachako dai gari ne mai Nisan gaske zuwa cikin Birnin Kano wanda Akalla zaka iya kwashe tafiyar awa daya da minti Arba’in a mota.

 

Categories
Labarai

Shugaba Buhari tare da matarsa Aisha da ‘yarsa sun tafi kasar Sin

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da kai dakinsa Aisha Buhari da ‘yarsa Hanan Buhari sun bar Abuja zuwa birnin Beijing na kasar Sin don halartar taron kasashen Afurka da kasar ya Sin.

Categories
Raayi

Jan hankali: Hattara dai matasa

Daga Hafizu Murtala

Kowa zai yarda dani cewa a ýan watannin da suka shude Siyasar Nigeria kamar yadda aka saba ta fara daukar zafi, wannan ya hada da rikicin majalisun tarayya da kuma sauye sauyen sheka da shugabannin siyasa suke yi daga wata jamíyya zuwa wata saboda muna dab da zaben 2019.

Wannan ya saka magoya bayan wadannan Jagororin suna ta musayar yawu a fagen kafofin sada zumunta. Masu suka nayi, Masu yabo nayi, Masu Zagi nayi da sauransu.

Sabo da takaici nace wa kaina, bazan kara Maganar siyasa da kowa ba a kafar sada zumunta ko a wajen ta, zan rike raáyi na na siyasa a zuciya, ranar zabe idan da hali na zabi abinda raina yake so. Amma bayan Nazari da bibiyar mutane masu hangen nesa ta tabbata cewa idan mutum zai kiyaye cin mutuncin dan uwansa, babu laifi don ka baiyana raáyinsa aka akan wani abu da alúmma take tattaunawa akai. Amma akwai wanda yace dani ai ita Siyasa, babu wani amana ko mutunci a cikinta. Wannan zancen ba gaskia bane.

A Khudubarsa ta yau, Limamin Masallacin Jumaá na Area 10 dake Abuja As-Sheikh Al-Yolawiy yayi nasiha akan musulmi suyi duba akan makasudin zamantakewa da ýanuwantaka ta musulunci, su guji gaba, aibatawa, kiyayayya da sauransu saboda raáyi na Siyasa. Ya kawo Ayoyi da dama a Al-Qurani mai tsarki ta yadda Allah yake umartarmu damu zama Alumma daya, masu son juna da

Wannan Khudubah ta sosa min wajen da ke min kaikayi, bisa nazarin da nayi akan yadda alúmma suka hasala suna ta jifan juna da maganganu na rashin dacewa saboda raáyi na siyasa. Raáyin da na lura yana da matsala a rayuwarmu. Dalilin fadin hakan kuwa shina, yawancin mutanen mu za kaga suna son Jagororin su kawai saboda su biya bukatar zuciyar su, da kona zuciyar abokan adawar su, amma ba wai don su samu wani abu a wajen wadannan Jagororin ba, ko su amfana dasu ta wata hanyar. Domin idan don aikin da Shugaba ya keyi kake son sa, to ka sani wannan aikin da yayi ba kai kadai zai amfana ba, duk wani mai rayuwa a wajen da aka yi aikin zai amfana dashi.

Wannan yasa nake tunanin son da wasu suke yiwa Shugabanni yayi kama da abinda Bature yake cewa “addiction” ta yadda wani zai ci Goro, Ko busa Sigari, don samun kwanciyar hankali da nutsuwa. Iyakar kenan. Yawancin wadannan magoya bayan, basu damu dasu suyi musabiha da shugabansu ba, ko yasan dasu, ko su kai masa ziyara, amma fa kai da kuke faduwa ku tashi tare zai iya gaba da kai akan wannan Shugaban, kaga kuwa akwai matsala babba.

Na lura da yadda ake yada Karya, Kazafi, Sharri a kafar sadawarwar zamani, saboda biyan bukatar zuciya. Wasu za kaga suna da gwani, wanda akansa sai inda karfinsu ya kare, wasu kuma haka kawai suka dauki karan tsana suka dorawa wani shugaba, aikinsu kullum shine yada maganganu na batanci akan sa. To mu sani, Allah yace duka abinda ka fadi ko ka yada, akwai Malaïka da yake rubutuwa, kuma za kayi bayani a gaba.

Dan gane da ýan Siyasa kuwa, wannan hoton ya ishe mu misali, su kam babu abinda ya dame su, duk abinda zai kawo masu mafita a siyasar su, shi suke bi, kadan ne suke tuntubar magoya bayansu kafin su dauki wani mataki na siyasa. Yawancin wadanda muke kaunar ma, idan suka suka samu mukamin, ýaýansu da surukansu da makusantan su, sune suke morewa fiye damu da muke gaba da junan mu akan su.

Ga kuma yan siyasa wani lokacin akwai abun haushi duba da yadda kusan sama da mutane goma suka fito duka daga yanki daya a PDP suke neman kujerar shugaban kasar da wanda yake kai ma yake nema, kuma yana da magoya baya, da ýan sanda, da soja da sauransu.

Shi Mulkin nan dai Allah ke bada shi, yasan wanda zai bawa 2019, ko muso ko kada muso. Don haka idan muna sane da wannan menene na tada jijiyar wuya? Muna sane a tarihin kasar nan, akwai manyan mutanen da sun nemi mulkin nan kamar ransu zai fita, amma Allah bai ga dama ya basu ba. Haka da yawansu suka mutu ba tare da samun biyan bukar su ba.

A karshe mu sani, koma dai menene, mulkin Nigeria zai bar Arewa ya koma Kudu bayan zangon da zamu shiga ya kare, kuma shekara takwas za suyi suna yi, a wannan yarjejeniyar da Idan suka ga dama ma suna iya karya ta. A yanzu idan muka lura mutanen Kudu basu ma damu da maganar wani 2019 ba, tunda a wajen su, lokacin Arewa ne, Saboda haka muje muci kanmu.

Sannan mu sani, idan dai har dimokradiyya muke yi, to kowa ma yana da yancin ya fito ya nemi takara, don haka idan ka zage shi ko ka bata shi, to ka rage masa zunubi ka dorawa kanka. Idan baka sonsa, sai ka bari ranar zabe ka zabi Wani sa. Duniya ma dai kowa zai bar ta, balle wani mulki. Allah yasa mu dace.

HAFIZU MURTALA,
Abuja, Nigeria.

Categories
Kanun Labarai

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin waziriyar Jamus Angela Merkel a Abuja

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Yau Juma’a ya karbi bakuncin waziriyar Jamus Angela Merkel a babban birnin tarayya Abuja.

Categories
Siyasa

Kano 2019: Takai ya yanki takardun tsayawa takarar Gwamna

Malam Salihu Sagir Takai da ya yiwa jam’yun ANPP da PDP takarar Gwamna a zabukan 2011 da 2015 ya yanki takardar sake neman kujerar Gwamnan jihar Kano karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Wannan shi ne karo na uku da Malam Salihu Sagir Takai yake neman takarar Gwamnan jihar Kano. A baya yayi takara a 2011 inda Sanata Kwankwaso ya samu galaba a zaben da tazara ‘yar kadan.

Sai dai a zaben 2015 Malam Salihu Sagir Takai ya kuma shan Kaye a hannun Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

Haka kuma, masu sharhin Siyasa a jihar Kano na ganin cewar a wannan karon Malam Salihu Sagir Takai na Iya samun galaba akan Gwamna mai ci Ganduje, idan har PDP ta amince ya bashi takara.

A zaben bana dai za a samu gagarumin canji a jihar ta Kano, kasancewar tsaffin Gwamnonin jihar guda biyu Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na da dumbin magoya baya, kuma na tare da jam’iyyar ta PDP.

Haduwar Shekarau da Kwankwaso a cikin inuwar jam’iyyar PDP babbar barazana ce ga sake komawar Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, kasancewar su duka tsaffin Gwamnonin na da dumbin magoya bayan da zasu iya kayar da Gwamna Ganduje.

Daman dai ba abin mamaki bane a jihar Kano a kayar da Gwamna kai ci a yukurinsa na sake komawa, domin ko a 2003 Malam Shekarau ya kayar da Gwamna mai ci Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da shima Malam Shekarau yana Gwamna Kwankwaso ya kayar da dantakararsa Malam Salihu Sagir Takai.

A wannan zaben na 2019, jihar Kano na databank cikin inda za a fafata sosai, inda tsaffin Gwamonin jihar biyu zasu kalubalanci Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje. Shin ko PDP zata samu Nasara a jihar Kano? Lokaci je zai tabbatar da hakan.

Categories
Siyasa

APC ta Amince da yin ‘yar tinke a zabukan fidda gwani na jam’iyyar

Uwar jam’iyya mai mulki ta kasa APC ta amince da yin kato bayan katon a yayin zabubbukan fidda gwani na jam’iyyar a dukkan fadin Najeriya.

Sai dai kuma Gwamnonin jam’iyyar tun kafin wannan lokaci suka nuna kin amincewa da zaben fidda gwani ta hanyar ‘yar tinke ko kato bayan kato.

Uwar jam’iyya ta APC tace za a yi kato bayan kato tun daga kan zaben Shugaban Kasa har zuwa kasa.

Categories
Labarai

Na yanke shawarar fitowa takarar Shugaban Kasa a PDP – Saraki

Shugaban majalisar dattawa na Kasa Abubakar Bukola Saraki ya bayyana aniyarsa ya tsayawa takarar Shugaban Kasa a karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Saraki ya bayyana hakan ne a shafukansa na sada zumunta Facebook da Twitter a ranar Alhamis.

Ya zuwa yanzu Saraki ya shiga cikin sahun masu neman jam’iyyar ta PDP ta amince musu yi mata takarar Shugaban Kasa a zaben 2019 dake tafe.

Categories
Kanun Labarai

Shugaba Buhari ya halarci taron masu ruwa da tsaki na APC

Shugabannin jam’iyyar APC na Kasa karkashin jagorancin Adams Oshiomhole na yin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a sakatariyar jam’iyyar dake babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Daga cikin mahalarta taron akwai Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo da Gwamnonin jam’iyyar da kuma ‘Yan majalisar dattawa da na wakilai.

Mana sa ran a yayin wannan taron ne uwar jam’iyyar zata bayyana matsaya ta karshe kan hanyar da zata bi wajen yin zabibbukan fidda Gwani a cikin jam’iyyar a dukkan matakai na shugabanci.

Categories
Labarai

Matsorata ne ke tsoron zaben ’yar tinke – Shehu Sani

Dan majalisar dattawa na jam’iyyar APC mai wakiltar jihar Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani ya soki lamirin gwamnonin APC dake tsoron ayi zaben fidda gwani a cikin jam’iyyar kato bayan kato.

Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan be a shafinsa na Facebook. Inda ya bayyana cewar “Mu bama tsoron salon zaben fidda gwani na kato bayan kato, domin kuwa jama’a je zasu yi ba wasu shafaffu da mai ba.”

Haka kuma Sanatan yayi gugar zana Gia Gwamnan jihar Kaduna Nasiru el-Rufai inda ya Kara da cewar “A baya an biya wasu tsiraru suyi zanga zanga don nuna kin jininsa amma yana nan gadagau a cewarsa.”

Categories
Labarai

Dan shekaru 52 ya tsira bayan da wani gida ya rufta masa a Kano

Lamarin dai ya faru ne da sanyin safiyar a Alhamis, idan Shugaban hukumar kwana kwana ta jihar Kano yace sun samu kiran gaggawa daga wani Mohammed Musa cewar gina ya rufta da wani magidanci a unguwar kofar Naisa.

Lamarin dai ya faru ne a tsakiyar unguwar kofar Naisa dake yankin karamar hukumar Gwale, inda gina ya ruguje akan wani magidanci mai suna Muhammad Zakiru, inda cikin ikon Allah aka kubutar da shi.

Haka kuma, shugaban hukumar ta kwana kwana ya yi kira ga Jama’a musamman wadan da ke zaune a gidajen kasa da su guji zama a cikin irin wadannan gidaje musamman a wannan lokaci na damina.