Categories
Nishaɗi

Munir Dan Iya ya lashe zaben fidda gwani na PDP a Sokoto

Tsohon kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Sakkwato Alhaji Munir Dan Iya shi ne ya lashe zaben fidda gwani na Gwamnan jihar Sakkwato karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Baturen zaben jihar Bashir Yuguda shi ne ya bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a yau, inda ya samu kuri’u 2,175.

An gudanar da wannan zaben ne karkashin kulawar tsohon Gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa da kuma Gwamna mai ci Aminu Waziri Tambuwal.

Categories
Labarai

Kabiru Gaya na yunkurin halakani – Kawu Sumaila

Mai baiwa Shugaban kasa shawara akan harkokin majalisar wakilai ta kasa Hon. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, kuma mai neman kujerar majalisar dattawa ta kudancin Kano ya koka akan yunkurin halaka shi da abokin takararsa Sanata Kabiru Gaya yake kokarin yi.

Kawu Sumaila ya bayyana hakan je a wata tattaunawa da yayi da manema labarai, inda ya bayyana cewar shi da kansa yaga mutanan da suke yunkurin halaka shi a lokacin da yake jawabi akan dandamali.

”Na hangosu kuma na tabbatar ba mutanan garin Sumaila bane, dan haka na sanya ‘Yan sanda suka kama su”

Kawu Sumaila ya bayyana cewar an samu mutanan da makamai bayan da aka kaisu wajen ‘Yan sanda a garin na Sumaila.

Sai dai Kawu ya dora alhakin wannan lamari akan Sanata Kabiru Gaya a yunkurinsa na ganin bayansa. Yabkara da cewar ya ankarar da jami’an tsaro akan yadda Kabiru Gaya yake yawo da ‘Yan daga da makamai.

Categories
Labarai

Tambuwal ya kada kuri’arsa a zaben dan takarar Gwamnan PDP a Sokoto

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya jefa kuriarsa a zaben fidda gwani na dan takarar Gwamnan jihar Sakkwato da ake yi a ranar Lahadi.

Categories
Kanun Labarai

Kungiyar kwadago ta janye yajin aikin da ta soma a duk fadin Najeriya

Kungiyar kwadago ta kasa ta janye yajin aikin da ta kira a makon jiya a duk fadin Najeriya.

Categories
Labarai

An gano motar Janar Alkali da aka kashe a wani kududdufi a jihar Filatu

Rundunar sojan Najeriya ya gano motar Janar Alkali da ‘Yan kabilar Birom suka kashe suka jefa motarsa a cikin wani kududdufi.

An dai dauki tsawon lokaci ana laluben gawar janar Alkali tun bayan da labarin kisansa ya bulla.

Categories
Kanun Labarai

Shugaba Buhari na kan hanyar dawowa Najeriya daga Amurka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kamo hanya zuwa Najeriya bayan da ya halarci taron majalisar dinkin duniya a birnin New York na kasar Amurka.

 

Categories
Labarai

Maman Taraba ta koma jam’iyyar UDP

Tsohuwar ministar harkokin mata da ta yi murabus a ranar Asabar, ta bayyana komawarta jam’iyyar UDP tare da yankar katin shiga jam’iyyar.

Categories
Labarai

Maman Taraba ta yi murabus daga mukaminta, ta fice daga APC

Ministar harkokin mata da iyali Hajiya Aisha Jummai Alhassan wadda aka fi Sani da Maman Taraba ta ajiye aikinta a matsayin ministar harkokin mata sannan kuma ta fice daga cikin jam’iyyar APC.

Ta bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ta aikewa Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar ta APC.

Categories
Labarai Raayi

Yajin aikin da NLC suke yi laifin Buhari ne – Mekara

Adamu Babale Makera mai taimakawa Gwamnan Gombe na musamman ya yi zargin cewar wannan yajin aikin da ma’aikata suke yi ba laifin kowa bane illa Shugaba Buhari. Makera ya wallafa kamar haka:

Tun kafin yajin aikin yayi nisa yana da kyau irinsu National Council of State, National Council of Traditional Rulers of Nigeria, Christian Association of Nigeria da kuma Jama’atu Nasril Islam su dauki matakan gaggawa na shigowa cikin lamarin don a kawo karshen sa saboda talakawan Najeriya zasu fuskanci matsananciyar wahala idan yajin aikin yayi tsawo. An shafe kwanaki kimanin 50 babu salari, ga kuma mugayen yan kasuwa da dillalai masu neman irin wannan dama don tsawwalawa talaka.

Ma’aikatan gwamnati a NajeRita sun chanchanci a yi musu karin albashi tun kafin zuwan Buhari, to sai dai zuwan Buhari ya kara tilasta hakan saboda wassu dalilai da dama amma zan yi tsokaci ne kawai akan guda biyu.

(1). Kamar yadda ya saba yin alkawura irin na yaudarar siyasa da kuma rashin lissafi, Buhari ya yiwa ma’aikata alkawarin zai sanar da yi musu karin albashi a karshen wannan watan da muke ciki na September, abun tambaya shine izuwa yanzu ya sanar da karin albashin da yace zai yi? Idan bai sanar ba ashe kenan ma’aikata suna da gaskiya idan suka tsunduma yajin aiki.

Batun alkawari Baba Buhari ya sha yin su amma ba ya iya cikawa, shi dai burinsa yayi muku alkawura saboda kawai ku sake zabensa a karo na biyu; to wannan alkawarin dai ga abun da ya jawo mana kuma shine ba shi da gaskiya. Rashin lissafi kuma shine ai ma’aikatan gwamnatin tarayya basu da yawa idan aka kwatantan da ma’aikatan jihohi da na kananan hukumomi, yaushe aka zauna qeqe da qeqe da shugabanni a matakin jihohi da kananan hukumomi akayi matsaya da gwamnatin tarayya cewa ga mafi karancin albashin da aka amincewa wanda jihohi da kananan hukumomi zasu iya biya? Ko a yanzu jihohi da yawa ba sa iya biyan N18,000 kuma sun gaza biyan albashi na tsawon watanni barkatai, yaushe wani zai zo musu da batun karin albashi su amince?

(2). Mu dai ba Malamai bane, to amma dole a san a ina za a ajiye mu don kuwa mu ba jahilai bane balle wani yazo yace mana wai tsadan abinci da hauhawan farashin kayayyaki daga ALLAH ne, haka kawai farashin ya tashi ba tare da dalili ba? Buhari yayi ci da zuci wajen zuwa da wassu ka’idodi irin nasa wadanda sukayi sanadiyyar hauhawan farashin kayayyaki irin wanda bamu taba gani ba a Najeriya kuma an yi ta yin kira gare shi amma yayi kememe ya ki amincewa; don haka shi muke daurawa alhakin tashin farashin kayayyaki. Kudaden da ma’aikata ke yin cefenen abinci kafin zuwan Buhari a yanzu sai sun ninka kudin sau 3, kun ga kenan karin salari ya zama dole idan yana son ma’aikatan su cigaba da rayuwa.

Alkawarin da Buhari ya yiwa ma’aikata amma ya kasa cikawa da kuma hauhawan farashin da salon mulkin sa ya jawowa yan Najeriya ne suka iza wutar wannan yajin aikin dake gudana a yanzu haka, don haka kai tsaye shine da laifi. Da fatan ALLAH YA kawo mana karshen wannan yajin aikin.

Categories
Labarai

PDP ta amince da birnin Fatakwal a matsayin inda za a zabi dan takarar Shugaban kasa

  1. Uwar jam’iyyar PDP ta kasa ya amince da birnin Fatakwal a matsayin inda za a yi zaben fitar da gwani na ‘Yan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar da za a yi nan gaba kadan.

An samu rarrabuwar kai tun lokacin da aka ayyana birnin Fatakwal a matsayin inda za a yi zaben fidda dan takara, inda wasu suka nuna cewar matukar aka kai taron birnin Fatakwal su ba zasu halarta ba.

Yayin da a gefe guda, Gwamnan jihar Ribas Nyesome Wike yace muddin aka dauke taron daga birnin Fatakwal to kuwa za a fa ba daidai ba a cikin jam’iyyar.

A cewar Wike wasu ‘Yan takarar Shugaban kasa je suke son a dauke taron daga birnin Fatakwal a maida shi wani wajen domin biyan bukatar kansu.

Sai dai kuma, a Zaman da ta yi a ranar Juma’a Shugabannin jam’iyyar sun amince ayi babban taron jam’iyyar na kasa a birnin Fatakwal din.