Categories
Labarai

Majalisar dokokin jihar Kano ya gayyaci Ganduje kan bidiyon badakalar da yayi

Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa domin bincike kan bidiyon da jaridar Daily Nigerian ta wallafa kan badakalar da Gwamna Ganduje yake ta karbar kudade a hannun ‘Yan kwangila.

A ranar 14 da 15 ga watan Oktoba ne Daily Nigerian ta wallafa wasu fayafayen bidiyo guda biyu da aka hasko Gwamnan Kano Ganduje yana karbar dalar Amurka daga hannun ‘Yan kwangila yana zubawa a aljihun babbar riga.

Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa domin bincikar wannan kazamar cuwa cuwa da ake zargin Gwamnan danaikata yasa Kwamitin ya gayyaci mawallafin wannan jaridar Jaafar Jaafar domin bayar da bahasi.

Sai dai bayan da Jaafar Jaafar ya bayyana don bayar da hujjoji gaban kwamitin. Kwamitin ya nemi Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya bayyana a gaban kwamitin ranar Juma’a domin bayarvda bahasi kan bidiyon.

Wata majiya ta tseguntawa wannan jaridar cewar, Gwamnan yayi wata ganawa ta gaggawa cikin sirri da kakakin Majalisar dokokin jihar Alhassan Rurum domin ganin bai amsa wannan gayyatar ba.

Sai dai kakakin Majalisar bai gamsu da rokon na Gwamna Ganduje ba na kada a bari ya halarci gayyatar kwamitin. Sai dai Ganduje ba shi da wani zabi a yanzu ko dai ya amsa gayyatar kwamitin ko yasa a tsige kakakin Majalisar abinda zai yi masa matukar wahala.

Categories
Labarai

Jam’iyyar APC tayi babban kamu a jihar Jigawa

Jam’iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Jigawa. Tsohon Kwamishina a Gwamnatin Sule Lamido kuma babban Lauyan Sule Lamido wanda yake jagirantar Sharia da ake yi masa a a Abuja ya sallama jam’iyyar PDP inda ya koma APC.

Mana Iya cewar PDP tayi wawar asara a jihar Jigawa.

Categories
Kanun Labarai

Sojojin Najeriya sun gano gawar Marigayi janar Alkali

Rundunar sojan Najeriya dake binciken kisan da aka yiwa marigayi Janar Alkali a kauyen Du dake yankin karamar hukumar Jos ta kudu sun ci nasarar gano gawar marigayin sojan.

Categories
Raayi

Takai ne yafi dacewa da Kano a wannan lokaci – Ali Yakasai

An bayyana Malam Salihu Sagir Takai na jam’iyyar PRP a matsayin wanda yafi dacewa da ya zama Gwamnan jihar Kano na gaba. Mai sharhi kan al’amuran kasuwanci Alhaji Ali Sabo Yakasai ne ya bayyana hakan a wata mukala da ya aiko mana.

“Yanzu mun fahimci komai ingancin Shugaba, kuma komai nagartarsa idan bai samu wadanda zasu tallafa masa gudanar da mulki ba to akwai matsala, saboda yana tubkane baya na warwarewa. Yanzu kalli Shugabanmu, Babanmu abun alfaharinmu Muhammad Buhari irin kokarin da yake wajen inganta rayuwar talaka. Bawan Allan nan Muhammadu Buhari har rashin lafiya ta kusa halakashi amma dattijon nan ya tsaya tsayin daka dan ceto rayuwar talaka.

Amma a gefe guda munyi rashin saa na Gwamnoni a arewa yawancinsu ba talakawa ne a gabansu ba, babu kishi, da ka suke tafiya, babu manufa ta inganta rayuwar talaka. Don haka wajibi ne mu sake tunani wajen samar da Gwamnoni masu inganci wadanda suke da akida da tsayuwa irinta Baba Buhari, kuma ko baa jamiyyar APC suka fito ba su yakamata mu goyawa baya domin su mulke mu.

Jihar Kano tana fama da irin wannan matsalar. Kano ne garin da yafi baiwa Baba PMB yawan kuriu. Amma ayyukan jihar Kano sabanin ayyukan Gwamnatin Baba Buhari ne. Harkar noma, noman rani da kiwo tun zamanin tsohon Gwamna Audu Bako (Allah ya kai rahama cikin kabarinsa) an barshi. Sai kuma Gwamna Abubakar Rimi da ya bude KASCO da KNARDA domin inganta noma.

Hanyar kasuwanci da masanantu da hanyoyin da zaa bunkasasu ko kusa baa dauki hanyar su ba, Kuma anyi halin ko in kula dasu. Kuma a gefe guda shine manufofin Gwamnatin Baba Buhari don inganta noma, kasuwanci da masanaantu

Zabinmu ga Salihu Sagir Takai na jamiyyar PRP zai dace da tafiyar Baba Buhari ta wajen rikon amana da jajircewa da karban shawarwarin kwararru da kuma kafewa domin aiwatar da su.

Salihu Takai tested and trusted ne, yana kama da Baba Buhari sosai ta wajen manufa iri daya. Salihu Takai yayi Chairman na Takai local Government ya kuma rike Chairman da inganci da bin sharia ta adalci. Duk dan local Government na Takai zai fadi alherinsa na rashin son kai da babakere.

Salihu Takai shi ya rike commissioner na gidan ruwa inda yayi katafaren gidan ruwa mafi girma a Africa ta yamma a wanda bayan kammala aikin ne ya dawo da rarar kudi Naira Miliyan 500 da suka yi ragowa.

SalihuTakai shine ya rike commissioner na local Government bisa Amana ta wajen baiwa dukkan local Government 44 hakkokinsu ba tare da ya dauki ko kuma a bashi ko sisin kwabo ba. Wannan abu sananne ne.

Salihu Takai kamar Buhari yake, yayi takara har sau 3 amma Allah bai bashi dama ba. Gashi yanzu Allah ya kaddara fitowa ta hudu a karkashin jamiyyar PRP. Jamiyyar Mallam Aminu Kano. Jagoran talakawa.

Buhari da Aminu Kano suna yaki akan danne talaka da yakar yan tamore masu zukar jinanai ba marasa galihu da raunana. Salihu Takai takalminsa yayi daidai da irin wadannan gwarazan mutane bayin Allah. Muna fata Allah ya bashi wannan kujera ta jihar Kano kuma ya kasance tare dashi. Ya fishsheshi zamewa. Amin”

Categories
Raayi

2019 kujerar Gwamnan Kano allura ce a cikin ruwa – Adam Muhammad

 

By Adam Muhammad

Hakika zaben Gwamnan Kano a 2019 zabe ne da zai zo na rashin tabbas gurin waye zai iya lashe zaben ba tare da wata tangarda ba, sakamakon yan takara da ake da su a jam’iyyu mabamban ta kamar haka:

APC: Ita ce jam’iyya mai mulki tun daga kan shugaban kasa har zuwa gwamnan Kano mai ci a yanzu wato Dr. Abdullahi Umar Ganduje, kasancewar jam’iyyar tana da dimbin magoya baya da farin jinin al’umma a shekarar 2015 inda ta lashe zabe da mafi yawan rinjaye a mafi yawancin jihohin arewacin Najeriya, ciki har da nan Kano, sai dai kuma jam’iyyar ita ma a yanzu tana fama da rikicin cikin gida a inda tun daga farko ta fara rasa manayan yan siyasa irin su Engr. Rabiu Kwankwaso da sauran su.

Babban Nakasun da jam’iyyar za ta samu shine na faifan bidiyon da yake zagawa a yanzu inda ake nuna wani mutum yana karbar daloli yana zubawa a aljihu a matsayin karbar na goro wanda ake alakanta wannan mutumin da Dr. Abdullahi Umar Ganduje wato Dan takarar Gwamna a karkashin tutar jam’iyyar APC, wannan abu zaiyi tasiri sosai a wurin jama’a masu kada kuri’a, ta yadda idan har Wannan Dan Takara baiyi saurin wanke kansa daga wannan zargi da ake masa ba to wannan bidiyon zaiyi tasiri a wurin jama’ar jihar Kano.

PDP: Jam’iyya ce da ta mulki kasar Najeriya tsawon Shekarau 16, kuma jam’iyya ce mai karfi a wannan kasa inda suka tsaida Dan takarar su wato Abba Kabir Yusif surikin Rabiu Kwankwaso, wanda shine yayi mashi kwamishina na Ayyuka a lokacin mulkin Kwankwason karo na biyu. Kwankwason wanda yayi gwamna har sau biyu a Kano kuma yana da dimbin magoya baya a Kano masu bin Darikar Kwankwasiyya.

Babban Nakasun da jam’iyyar za ta samu shine na bakin jinin da jam’iyyar ta dauko tun daga lokacin mulkin Goodluck Ebele inda mafi yawancin jama’ar Arewacin Najeriya suke mata Kallon jam’iyyar da tayi sake wajen yakar yan Boko Haram, Sannan Babban nakasun da zai sami jam’iyyar shine na ganin manufar wannan Dan takara shine cewa ba zai ci Amanar Kwankwaso ba.

Haka zalika wajen zaben fidda gwani na Dan takarar Gwamna jam’iyyar tayi karfa karfa inda ta bawa Kwankwason kai da fata na ya fitar da duk Dan takarar da yake so, bayan ya dawo jam’iyyar ya tarar da mutane sama da mutum 100 sun sayi foma fomai na yin takara daban daban, amma jam’iyyar tayi fatali da su ta kawo wadanda Kwankwason yake so, wannan ta sa jam’iyyar ta rasa magoya baya da yawa a jihar Kano ciki har da manyan yan takarar Gwamna mutum shida.

PRP: Jam’iyya ce wadda Mallam Aminu Kano ya kafa ta domin ceton Talakawa, jam’iyyar ta samu karbuwa tun a wancan lokacin inda ta kafa Gwamna a wannan jihar ta Kano, anyi yunkurin dawo da ita a lokuta daban daban amma hakan su bai cimma ruwa ba.

A wannan lokacin ma jam’iyyar tana nan da ranta inda ta dauko Dan takarar Gwamna wanda yayi takara 2011 da 2015 wato Mallam Salihu Sagir Takai, Takai dai yayi Shugaban Karamar hukumar Takai a shekarar 1999 inda jama’ar garin suka shaida ba a taba shugaban da suka mora kamar sa ba, sannan yayi kwamishina a lokacin Mulkin Shekarau har guda biyu yayi Kwamishinan ruwa, sannan yayi na kananan hukumomi, a inda nan ma, aka yaba da irin rikon amanar sa, ta yadda Kananan Hukumomi suke karbar kasan su ba tare da fincen ko sisi ba.

Haka zalika babban abin da ya kara fito da shi kuma yake yawo a zukatan Kanawa shine Matatar ruwa da ya gina ta tamburawa wadda babu kamar ta a fadin yammacin Afirika, kuma sannan aka sami rarar kudi har Naira Miliyan dari biyar, amma ya mayar da su asusun gwamnati ba tare da ya zuba a aljihun shi ba.

A gefe guda wannan Dan takara sananne ne a jihar Kano, yayi takara har sau biyu, kuma sannan zai samu tausayin jama’ar kano saboda shine ya lashe zaben fidda gwani a jam’iyyar PDP amma daga baya labari ya canja sakamakon waccen dama da aka bawa Kwankwaso.

Babban nakasun da wannan jam’iyyar za ta samu shine sabuwar jam’iyya ce, sai an tallata sosai kafin jama’a su san ta, sannan kuma jam’iyyar bata da wasu manya a cikin ta.

Categories
Kanun Labarai

Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Kaduna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Kaduna a wata ziyara ta bazata, domin tattaunawa da Shugabanni da kuma jagororin addini a jihar domin gano bakin zaren matsalolin da jihar ke fuskanta.

Categories
Raayi

Kafin ka zargi Sheikh Daurawa akan hudubarsa ka san abinda yace

 

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

1. Daga cikin Hanyoyi mafi muni na cin dukiyar Haram mafi muni shine karbar cin hanci da rashawa. Wanda Aka Tsinewa Mai Bayarwa Aka Kuma Tsinewa Mai Karba. Abdullahi bn Amr (Allah Ya kara yarda da shi) ya ruwaito daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam cewa, ” Allah Ya la’anci mai bayar da cin hanci da kuma mai karba.

2. Juya gaskiya ta koma karya ko kuma juya karya ta gaskiya kamar yadda alkali da lauyoyi ke yi na daga rashawa mai muni. Alkali a ba shi rashawa ya kwace gaskiya daga wajen mai gaskiya ya ba wa makaryaci. Ko Jami’an tsaro a ba su rashawa su juya laifi daga mai laifi su mayar kan mara laifi.

3. Kamar yadda wani ya kira ni a waya yana Tambaya ta ya taba aikata wani laifi da yake damunsa. Sun taba kama ‘yan fashi guda biyar wadanda aka yankewa hukuncin kisa, sai daya daga cikinsu ya ce yana da kudi masu yawa a boye idan suka sake shi zai ba su. Suka tafi hanyar kauye suka samu wani bawan Allah da bai san hawa ba bai san sauka ba suka yi masa duka sannan suka sa shi a cikin barayin aka je aka kashe shi.

Daya daga cikin wadannan Jami’an tsaro ya bar aiki shekaru da dama, amma duk sanda ya kwanta barci sai ya rika hango wannan mutumin.

4. Kowa ya san halin da ake ciki a Kano wanda duniya gabadaya kallo ya dawo kan Kano. Sakamakon tuhuma da ake yi wa mai girma Gwamna na karbar cin hanci da rashawa daga hannun ‘yan kwangila. Wanda wasu bidiyo ke ta yawo a kafafen yada Labarai, kuma majalisar dokokin jihar Kano tana bincike domin gano gaskiya ko karyar wannan bidiyon.

5. Wannan abu da Majalisar ta yi abu ne mai kyau domin tabbatar da gaskiya da kuma yin aiki da ita. Domin mutane ne guda biyu, daya dan jarida daya dan siyasa.

6. Dan jaridar nan daga yada bidiyon nan ya saba Alkur’ani ya zo Majalisar ya tabbatar da cewa wadannan bidiyon gaskiya ne. Sannan a bangaren gwamnatin sun ce wadannan bidiyon karya ne, kage ne, sharri ake wa mai girma Gwamna.

7. To yanzu ina gaskiya ta ke? Idan ka ce karya da kage da sharri aka yi wa maigirma Gwamna da wanne dalili? Idan ka ce gaskiya ne mai girma Gwamna yayi haka da wanne dalili? Wa za ka gasgata a cikin wadannan bangarori guda biyu?

8. Wannan ne ya sa Kasashen duniya suka zuba ido ga majalisar domin tabbatar da gaskiyar dan jarida ko karyar sa. Ko kuma tabbatar da gaskiyar Gwamna ko karyar sa.
Wanda a karshe kowanne ne ya faru darasi ne a garemu Al’umma gabadaya.

9. Idan ya tabbata karya da kage da sharri aka yi wa maigirma Gwamna wannan zai Kara masa kima, zai kara masa mutunci zai kuma kara masa daraja.
Sannan kuma zai zama hukunci mai tsanani akan Dan jaridan da ya yi yunkurin bata masa suna.

10. Idan kuma ya tabbata wannan kudi na rashawa ne mai girma Gwamna ya karba wannan zai zama babban kamu a jihar Kano wanda ba a taba yin irin sa ba. Shine kama dan siyasa mafi girma a jihar Kano, kuma idan an hukunta shi wannan zai zama babban darasi a kasa baki daya.

11. Musamman Gwamnantin da shugaba Buhari yake jagoranta wacce ya shelantawa duniya zai yaki cin hanci da rashawa da tabbatar da tsaro. Wadannan sune Abubuwan da ya yi kamfen da su a shekara ta 2003 da shekara ta 2007 da shekara ta 2011 da shekara ta 2015 da kuma shekara ta 2019 da yanzu za a shiga zabe.

Abin dai bai canja ba shine yaki da cin hanci da rashawa da farfado da tattalin arziki da kuma tsaro.

12. Idan wannan abu ya tabbata aka yi kokarin canja shi ko aka yi kokarin murde shi wannan zai zubar da mutuncin jihar Kano dama kasa baki daya. Sannan zai nuna cewa yaki da cin hanci da rashawa da ake cewa ana yi ba gaskiya ba ne.

13. Akan wannan an daure manyan ‘yansanda. Akan irin wannan tuhuma an cire babban jami’in DSS. Akan Irin wannan tuhumar an kama Malam Ibrahim Shekarau wanda yayi Gwamnan jihar Kano shekara takwas, yayi Minista kuma Basarake ne. Duk da mutuncinsa da darajarsa da kimarsa da ake gani a jihar Kano an kama shi an kai shi kotu ana tuhumar sa da cin kudi na rashin gaskiya.

14. Ka ga wannan idan Gwamnati ta dauki mataki na tabbatarwa ko kuma korewa wannan zai zama babban darasi ga ‘yan siyasa. Nan gaba za a ce da Dan siyasa ga mulki ya ce ba ya so saboda ya ga ana hukunta manya. Sannan rigima da zubar da jini gami da shaye-shaye za su ragu akan son mulki. Saboda mutane za su ga ko ina ka je ba za ka sha ba idan aka same ka da cin dukiyar Al’umma.

Categories
Kanun Labarai

Aisha Buhari ta karrama fitaccen dan sanda Abba Kyari

A yayin da take bikin cika shekara uku da kirkiro kungiyar Future Assued, uwar gidan Shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ta karrama fitaccen dan sanda Abba Kyari bisa yadda yake nuna kwazo wajen Yaki da miyagun mutane batagari.

A yayin bikin Aisha Buhari ta bayyana cewar an karrama Abba Kyari sabida kwarewa Danjuma jajircewa da nuna bajinta da yake yi wajen yaki da miyagun mutane batagari.

Abba Kyari shi ne ya jagoranci kama fitaccen mai yin garkuwa da mutane wato Evans. Wannan muhimmin aikin ya janyowa Abba Kyari kima da martaba a Najeriya inda akai ta karrama shi tare da yaba masa.

Categories
Labarai

Ganduje ya aika wa Sheikh Daurawa sammaci saboda yayi huduba akan bidiyon badakalarsa

A daren jiya Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sa aka cikumo Kwamandan Hisba na jihar wanda yayi Hudubar juma’a akan faifan bidiyon Gwamna da aka nuno shi yana karbar dalar Amurka.

Rahotanni sun tabbatar da cewar Gwamnan ya sa an kamo dukkan Malaman da suka yi huduba akan bidiyon zuwa gidansa dake titin Miyangu a daren jiya dan jin dalilinsu na yin huduba kan badakalar tasa.

Bayanai sun nuna cewar Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana a cikin hudubarsa da yayi a Masallacin Ansarus Sunnah dake unguwar Fagge cewar wannan video ya Isa shaida idan idan mutum yana neman hujja.

Categories
Labarai

Dalibi dan JSS 3 ya dirkawa wata ‘yar bauta kasa cikin shege

Wani dalibi a wata karamar makarantar sakandire da aka sakaya sunanta a jihar Abiya ya dirkawa wata budurwa mai yiwa kasa hidama karkashin NYSC cikin shege.

Lamarin dai ya janyo cece kuce a makarantar ta yadda akai mai yiwa kasa hidamar har ya bari dan aji uku na karamar sakandire yayi kwance kwance ya dirka mata ciki.

Wasu da dama na ganin duba da yadda ‘yar yiwa kasa hidimar ta baiwa dalibin tazarar shekaru bai kamata ace ya bari hakan ya auku tsakaninsu ba, yayin da wasu ke tunanin ko barazana dalibin ya yiwa budurwa.

Ana dai cigaba da gudanar da bincike domin gano bakin zaren matsalar da yadda za a warware ta.