Categories
Labarai

A shirye nake na tafka muhawara da Buhari – Atiku Abubakar

Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewar a shirye yake da ya tafka muhawara da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shirye shirye zaben Shugaban kasa na 2019.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da Baban kwamitin yakin neman zabensa a matsayin dan takarar Shigaban kasa.

A wajen taron, Atiku ya kalubalanci Shugaba Buhari da ya fito suyi muhawara a gabanin zaben Shugaban masa da za ai a nan da shekarar 2019.

Categories
Kanun Labarai

Shugaba Buhari ya halarci taron tsaro kan tafkin Chadi a Njammena

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci taron tsaro kan yankin tafkin Chadi a birnin Njammena na kasar Chadi.

Mana wannan taro ne sakamakon hare haren Boko Haram da ‘yan kungiyar suke kaiwa a yankin na tafkin Chadi da ya hada da Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru.

 

Categories
Labarai

Muna bincikar bidiyon Ganduje a Landan – Magu

Shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC Ibrahim Magu ya bayyana cewar suna buncikar bidiyon Ganduje a Landan.

Shugaban hukumar ya bayyana haka ne a lokacin da wani dan fafutikar Yaki da cin hanci da rashawa Bulama Bukarti yayi masa tambaya lokacin da aka yi wata ganawa tsakanin Shugaban hukumar EFCC da ‘yan Najeriya mazauna kasar Burtaniya.

Magu ya bayyana cewar yanzu haka sun baiwa kwararru dama domin yin binciken kwakwaf akan wannan faifan bidiyo da aka nuno Gwamnan Kano Ganduje na sanya daloli a cikin babbar riga.

Categories
Raayi

Raddi ga Farfesa Labdo kan maganganunsa game da Sarkin Kano

 

Daga Magaji Galadima Abdullahi

Yanzun nan dan-uwana Malam Ibrahim Ado Kurawa ya aiko min wani rubutu da wani waishi Professor Umar Labdo Muhammad na Jami;ar Bayero tamu ta Kano yayi kuma aka watsa a kafafen sadarwa.

A rubutun shi Umar Labdo ya fake da guzuma yayi ta rabkawa karsana harbi, inda yayi hasashen cewa al’ummar kasa Nijeria suna cikin wani matsanancin hali, a bisa hakan sai ya kalubalanci mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na 2 da ya fito ya baiyanawa shi Ummarun wai wadanne matakai da yunkuri sarkin yayi domin taimakawa talakawa su fita daga cikin wannan hali?

Bayan ya wassafo kalubalen sa ga mai martaba sarki, sai Umar Labdo yayi kidansa kuma ya rausaya, inda yace shi baiga wata hobbasa da mai martaba sarki yayi ba wajen yayewa al’umma wannan bakin talauci da yayi masu katutu, duk kuwa da dimbin dukiyar da ya taskace, hasali ma yace kullum ya wuce ta Kofar Kudu yaga matan talakawa na holi don karbar sadakar taliya leda daya kacal da Sarki Sanusi yake basu sai yaji duk ransa ya baci domin a cewar sa yasan mai mataba sarki yana da arzikin da ya kamata ace katan guda-guda ake rabawa matan maimakon wannan dille dan-uwa.

A wannan rubutu dai Umar Labdo ya kalubalanci mai martaba sarki da ya fito ya fadi gidauniya nawa ya kafa ko wane asusu ya tanada domin magance wa al’umma talauci dindindin? Anan ma Umar Labdo ya bawa kansa amsa cewa babu ko daya, duk kuwa da dimbin arziki da hanyoyi fiye da na chali da Sarki Sanusi yake dasu.

Maganganu irin wadannan lashakka basa bukatar amsa, domin dama mai rubutun ba amsa yake nema ba, bukatarsa shine ya tayar da kura domin aga cewa karansa ya isa tsaiko har yana kalubalantar sarkin Kano. Shi a ganinsa hakan ne zai sa yayi suna kuma jama’a su sanshi. Ba zan so na kara masa ajawali ta hanyar kula shi ba, toh amma wannan barababiya da yay[, lallai akwai bukatar a sauke shi daga kan keken-beran da ya hau, kana kuma masu karatu da sauran wadanda ke bibiyarsa suma a haska musu turba kuma a yaye musu maboyarsa a burumburum din da yake nema yayi musu.

Yanzu in banda tsagwaron kitifi da kinibibi mutum yace wai baiga abinda mai martaba sarki yayi , yake kuma kan yi wajen taimakawa talakawa ba? Ba zan bata lokacin mai karatu wajen zaiyano abubuwan alheri da mai mataba sarki yayi ba da rawar da yake takawa wajen inganta rayuwar alumma kamar yadda ya wassafa wa gwamnatin taraiya kadarkon da za a hau a fita daga cikin matsanancin hali a lokacin da tattalin arzikin Nijeriya ya shiga halin mutumutu-rairai. Har ila yau bazan so na gundure ku da bayanin cewa mai martaba sarki shine shugaban katafariyar gidauniyar nan ta duniya wato Black Rhino wacce ke tallafawa kasashe masu tasowa a Afrika da Amerika ta kudu da kuma tsibiran Wiskindiya.

Sarkin Kano yayi amfani da damarsa wajen kawo wannan gidauniya ta taimaka a Kano, yanzu haka suna nan suna aiki domin kafa tashar samar da wutar lantarki a madatsar ruwa ta Tiga kuma an kusa kammalawa. Sannan ba sai na fada ba, kowa yasan cewa Sarkin na Kano shine Amara-kirjin-biki a Dangote Foundation kuma ya kalmaso ayyuka da dama zuwa Kano domin taimakawa talakawa.

In aka ce za a tsaya lissafa ayyukan taimako da inganta rayuwar talakawa da mai martaba sarki yake toh sai a tabo kwal uwar daka amma ba akai magaryar tukewa ba. Ai kunga ban ma yi maganar zabari da safa da marwa kullum kasashen duniya yau ya kai gwauro China gobe ya kai mari kasar Afrika ta kudu duk domin neman yadda zasu zo su bude masana’antu a Kano domin talakawa su sami aikin yi da kuma yadda za a inganta harkar noma na zamani. Wannan fa duk kada ayi maganar wadanda sarki yake taimakawa a daidaiku, domin daga hawan sarki karaga zuwa yau, wa yasan iya wadanda ya taimakawa kama daga masu lalura ta asibiti da masu neman taimakon makaranta da masu neman aiki. Yanzu duk bankuna da sauran manyan cibiyoyin hada-hadar kudi ina ne jihar Kano bata da dan-makwayo mai rike da babban matsayi dalilin alfarmar sarki ? Lallai makiyinka baka burge shi ko ka saka giwa a kata.

Toh duk ma a jingine wannan, a magana ta zube ban kwarya ta, don Allah ta yaya alhakin magance wa talakawa talauci ya rataya a wuyan sarkin Kano kacokam ? mai yasa Umar Labdo bai tuhumi shugaban kasa ba ? mai yasa bai tambayi gwamnan Kano ba? mai yasa bai tambayi sauran shugabannin siyasa wadanda duk shekara ake kasaftawa kuma a ware kudi makudai domin yiwa talakawa aiki ba ? lallai ashe ana tsoron inna inji ‘ya’yan maiya. Ina dalili ina dan mafari da ya tsame mai martaba sarkin Kano duk cikin gungun sarakuna ? lallai ashe amabuwa sai karme.

Shi sarkin Kano bashi da ma’aikatan watsa labarai masu shafawa labari shuni da maishe da allura garma. Shi duk aiyukan taimakon da yake yi toh sabili da Allah yake yi ba don a gani a fada ba, wannan shi yasa su Umar Labdon duniyar nan ba zasu ga irin aiyukan ba. Su dai talakawa suna tare da sarkin su, shi kuwa mai sarki ba fadi yake ba, sai dai kawai a ganshi da riguna tafka tafka.

Babban abin ta’ajibi a wannan lamari shine yadda Umar Labdo wanda aka ce wai professor ne kuma yana da’awqr malanta irin tamu ta gida amma hassada da kitiko suka rufe masa ido har yake magana irin ta ‘yan magaru ko mazowwa teburin maishayi. Shi ilmi yana da shu’umanci da waibuwa ta yadda in mutum baiyi taka tsan-tsan ba sai ya kaishi ga hallaka kamar yadda ya faru ga Bil’ama dan Ba’ura. Kuma duk tarin karatun mutum in bai iya sarrafa shi ba toh sai kaga tamkar daga jami’ar Jatau na albarkawa aka yaye shi. Wannan shi yasa in kaji ance Professor Sheikh Umar Labdo Sai ka zata wani hamshakin masani ne amma kash ! kwamfa tamkar doki ne ingarma akawali mai doshiyar goshi da torami hudu amma kofatan na sakaina.

 

Categories
Labarai

Gwamnan Nassarawa Almakura ya baiwa EFCC kyautar fili mai fadin hekta 50

Gwamnan jihar Nassarawa Umar Tanko Amakura ya baiwa hukumar Yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC kyautar fili mai fadin hekta 50 a lafiya babban birnin jihar.

Sai dai kuma tsohon Antoni janar kuma kwamishinan Shariah na jihar ya bayyana cewar wannan kyautar fili ta sabawa doka da kundin tsarin mulkin Najeriya.

 

Categories
Labarai

Sanata Lidani ya koma APC daga jam’iyyar PDP

Sanata Joshua Lidani dan majalisar dattawa nai wakiltar jihar Gombe ta kudu ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Sanata Lidani ya bayyana sauya shekarsa ne a zauren majalisar dattawa a ranar Laraba.

Categories
Kanun Labarai

Shugaba Buhari ya isa Maiduguri don duba sojojin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya Isa Maiduhuri babban birnin jihar Borno domin duba sojojin Najeriya da suka jikkata da kuma jajanta musu kan harin da ‘yan Boko Haram suka kai a garin Metele inda suka kashe sojoji sama da dari.

Wannan harin da Boko Haram suka kai a garin na Metele ya tayar da Kura sosai a Najeriya. Indai akai ta dora laifin alhakin wannan harin akan shugabannin sojojin Najeriya dake jihar Borno.

Categories
Kanun Labarai

Osinbajo ya kaddamar da bayar da kayan tallafi a Jigawa

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kaddamar da bayar da kayan tallafin kayan Noma da sana’o’i a jihar Jigawa.

Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar shi ne ya samar da kayayyakin aikin tallafin domin rarrabawa fa manoma da kuma sana’o’i.

Categories
Taska

Wani Kare ya mutu bayan da wasu mutum hudu sukai masa fyade

Wani kare da aka bayyana sunansa da Courage ya mutu bayan da wasu karti su hudu sukai masa fyade a kasar Indiya.

Jaridar Sun ta kasar Indiya ta ruwaito labarin wannan kare nai nan tausayi. Inda ta ruwaito cewar an garzaya da kare asibiti domin ceton rayuwarsa amma yace ga garinku nan.

Har ya zuwa lokacin da aka hada rahoton ba a kai ya gano wadannan matasa da suka yiwa wannan Namijin kare fyade ba.

Categories
Labarai

Magu yaki karbar kyautar Ganduje ta miliyan goma ga hukumar EFCC

Shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Ibrahim Magu ya mayar da hannun Kyauta baya, inda Yaki karbar kyautar Naira miliyan goma da Ganduje ya baiwa hukumar domin shirya gasar gudun yada kanin wani.

Magu ya bayyana cewar hukumar bata karbar tallafi na kudi daga hannun Gwamnoni. A ranar Litinin ne dai mai magana da yawun Gwamnan Kano Aminu Yassar ya bayyana cewar Gwamnan ya baiwa hukumar tallafin Naira miliyan goma dan ta shirya wata gasar tsere.

Sai dai a lokacin da yake mayar da martani kan batun, kakakin hukumar Tony Orilade ya bayyana cewar hukumar ya nesanta kanta daga karbar wadancan kudade da aka ce Ganduje ya bayar.

“Kokarin karya lagon hukumar ne na yaki da cin hanci da rashawa, wani Gwamna ya dauki kudi ya baiwa hukumar “ A cewar Orilade.