Categories
Raayi

Shehun Shagari, Shagarin Shehu – Mansur Isa Buhari

 

Shugaban ƙasa Shehu Aliyu Usman Shagari ya bar duniya da shekara 93. Ya yi rayuwa mai tsawo mai albarka. Ya bar zuri’a mai yawa mai albarkar da kowa ƙasar nan da ma wajenta ya na son alaƙanta kan shi da ita. Daga ƙarshe ya rabu da duniya lafiya kuma cikin aminci wanda ya sa al’umma ta ji zafin rabuwa da shi.

Shehu Shagari bai yi zurfi a karatun zamani ba, amma ya bar ilmi da hikimar da jami’o’i za su kamfata su sha kuma su shayar da wasu har su bar saura. Ta rayuwar Shehu Shagari ne na ƙara tabbatar da cewa tarin karatu daban, ilmi daban.

A raye ko a mace, sunan “Shagari” ya taimaki mutane da yawa. Na san mutanen da sunan Shagari a matsayin gari, da ke maƙale da sunansu, ya sa sun samu girmamawa a kudanci da ma wajen ƙasar nan. Wani ya bani labarin yadda ya samu girmamawa da kulawa ta musamman a NYSC camp saboda sunan Shagari da ya ke a maƙale da sunanshi, alhali shi ɗan talakawa ne a garin na Shagari. Wasu da yawa sun samu kulawa ta musamman a wuraren ɗaukar aikin gwamnati da na ɗamara daban-daban saboda sunan Shagari da ke maƙale a sunayensu. Wannan abu kuma zai ci gaba har abada matsawar akwai tarihi a ƙasar nan.

Hakan shi ya nuna cewa Alhaji Shehu Shagari ya samu sheda da karɓuwa da girmamawar da babu wani tsohon shugaban ƙasar nan ya samu a idon ƙabilu dabandaban a ƙasar nan da ma duniya baki ɗaya. Duk faaɗin ƙasar nan, duk da irin bambanci da rikicin addini da ƙabilancinta, babu inda za ka ambaci cewa Shehu Shagari mutumin kirki ne a ce maka “anya?”.

Babu wani lokaci da zan iya tuna Shugaba Shagari ya yi katsalandan ko nuna ɓangaranci a fili akan sha’anin mulki ko wani sha’anin siyasa na ƙasar nan da ma na jiharsa ta Sakkwato. Ya riƙe girman shi ya kuma kama mutuncin shi da har waɗansu su zata ya daɗe da mutuwa.

Rayuwa da mutuwar Shugaba Shagari sun zama wani babban darasi ga shuwagabbani kuma abin alfahari ga talakawan ƙasar nan. Kuma bai mutu ya bar ma zuri’a ko jihar shi abin kunyar da za a dinga jifar mu da shi ba.

Allah ya kai dausayin aljannah a makwancin Shehu Usman Aliyu Shagari.

Categories
Raayi

Tsakanin Buhari da ‘Yan Arewa: Kura da shan bugu. . .

Daga Mansur Ahmed

Da ya ke in ka yi magana a kan Buhari, yanzun nan za ka ga mahaukatan cikin masoyan sa sun fara zagin ka da cin zarafi sai ka d’auka Buharin ba shi ne wanda ya kasa yi wa Arewa komai ba ne. Yarabawa su na ta sharb’ar romon dimokaradiyya a kudanci, kai ka ce d’an su ne ke mulkin. Su kuwa mutanen Kano an bar su da ginin gidan yari, wanda shi ma ana yi ne saboda mummunar manufar Buhari ta tozarta ‘yan Arewa.

Ko da ya ke muna cikin jimamin karb’ar yankunan Baga da wasu manyan garuruwa da ‘yan Boko Haram su ka yi a cikin ‘yan kwanakin nan, da kuma rasuwar sojoji 126 da aka kashe kwanakin baya, ga shi kuma cikin satin da ya wuce an kashe sojoji 13 da d’an sanda d’aya ranar Talatar da ta gabata. ‘Yan agajin mu da aka yi garkuwa da su har yanzu babu labarin su, balle a samu shugaban k’asa ya jajanta wa kungiyar Izala ko ya yi magana domin a nemo su ruwa a jallo.

Kullum labarin irin na k’anzon kurege dai kawai a key i wa ‘yan Arewa farfaganda da shi – yau a ce Boko-haram ta k’are, gobe a ce sun tsere, jibi kuma a ce kad’an suka rage. Sai ka rasa labarin wanne ne na gaskiya? Abin da Buhari ya fi so shi ne a kawo malamai da ’yan wasan fim din Hausa da na yankin kudanci, a ci, a sha sannan ya fad’a musu ya na neman goyon bayan su game da komawar sa mulki.

A Jihar Zamfara rayukan mutane sun zama kamar rayuwar gandun dabbobi, ka je ka kama wanda ka ke so ka hallaka. A k’one inda ake so ko a yi garkuwa da wadanda ake so a nemi kudi mai tsoka da su. Idan ba’a biya ba a kashe ka kisan wulak’anci. Idan mace ce a yi ta fasik’anci da ita sai k’arfin ya k’are. Takaici da damuwa su saka ta kashe kanta ko su kashe ta bayan sun illatar da rayuwar ta. Wannan wacce irin masifa ce?

Abin d’aukar hankali da rainin wayon shi ne, gwamnan jihar Zamfara shi ne shugaban gwamnonin k’asar nan kullum yana tafe kamar an d’aura wa kare aure. Malaman mu da manyan Arewa sun kasa tsawatar masa ko shugaban k’asar ma ya kasa d’aukar mataki a kan sa, saboda ya na tsoron sa.

Wani abin takaici wai sai ka ji an ce Buhari ya kira Sarki wane a waya ya jajanta masa bisa abin da ya ke faruwa. Wannan ai ba ma abin fad’a ba ne domin nuna gazawa ce da halin ko in kula a kan rayuwar mutane. A banza Buhari ya ke zuwa taron murnar zagayowar haihuwar wani (birthday) ko k’addamar da littafi, amma ba zai iya zuwa ya nuna damuwa a kan talakan Arewa ba.

Garkuwa da mutane a Arewa ta zama kamar cin kasuwa. Ka na jimamin an kama wancan sai ka ji wancan ma ya shiga hannu. Abin da zai ba ka mamaki shi ne har yanzu ba’a d’auki wani babban mataki da zai bawa ‘yan k’asa k’warin gwiwar an kusa kawowa k’arshen matsalar ba. Nan aka kama wasu ’yan mata su biyu a Kebbi har da yayarsu da ’yan biyun suka fito shi kenan an wuce wajen. ’Yar uwar ta su ko a wanr yanayi ta ke? Oho!

Shi Buhari hankalin sa ya na kan yadda za’a yi ya koma mulki shi ya sa ba shi da lokacin da zai je Zamfara ja je, ko ya yi wuni biyu a can domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan yadda za’a kawo k’arshen abin da ya ke faruwa. Amma zai iya zuwa taron wani aikin banza ko shan shayi a kan yanayi ko noman rani ko saka hannu a wata yarjejeniya a k’asashen k’etare. Tunda ya zama shugaban k’asa bai je Zamfara sau uku ba. Na tabbata an kashe ‘yan Nigeria sama da 500 a Zamfara amma yaje Ingila sau 8. Tsakanin Akwa Ibom da Zamfara wacce ta fi nisa? Buhari ya fi ganin zuwa Akwa Ibom saboda can kuri’a za’a samu Zamfara kuma rayukan mutane za’a kare. In a yankin Yarabawa a ke wannan abin da yanzu ka gan shi tunda su can ya fi tsoron su.

Nan wani d’an majalisa ya tashi a idon duniya ya bayyana wa duniya zahirin halin da ake ciki a jihohin Borno da Yobe game da abin da ke k’asa a kan Boko-haram. Amma mutane suka yi biris saboda ba’a son gaskiya, kuma hankalin shugabannin k’asar ya bar kan kare rayuka ya koma kan neman kuri’a.

Saura na ji wani shawaraki, dibgagge, gargajiga, salgoriyo ko makahon dan jagaliya ya fito ya zage ni. Wannan shine sak’o na na k’arshen shekara zuwa ga Muhammadu Buhari.

 

Categories
Labarai

Duk wanda muka samu da laifin karbar cin hanci zai dandana kudarsa – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar dukkan wanda aka kama yana karbar cin hanci da rashawa zai dandana kudarsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da gidan Radiyon muryar Amurka, inda ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa ta kakkabe cin hanci da rashawa daga Bajeriya.

Shugaban ya Kara da cewar ana samun cigaba sosai a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Shin yaya kuke kallon wadannan Kalamai na Shugaban kasa?

Categories
Labarai

Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya ziyarci Sakkwato don ta’aziyar Shagari

Daga Nura Aminu Dalhati

Gwamnan jihar sokoto Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal tareda tsohon Gwamnan jihar sokoto Alh Attahiru Bafarawa garkuwan sokoto, da mataimakin gwamnan jihar sokoto Hon Manir Dan’iya da tawagar gwamnati sun tarbo tsohon shugaban kasar Nigeria Dr Good Luck Ebele Jonathan, wanda yazo Sokoto ne domin gabatarda taaziyar rasuwar tsohon shugaban kasar Nigeria Alh Shehu Usman Aliyu Shagari a mafaifarsa dake Shagari a Sakkwato.

Categories
Kanun Labarai

Zamu samar da cibiyar tunawa da Shehu Shagari – Buhari

Yayin da ya isa jihar Sakkwato domin yiwa Gwamnati da iyalan Tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari ta’aziyar rasuwarsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhinin sa na rasuwar Shagari. Ya Kara da cewar dole ne Gwamnati ta samar da cibiyar tunawa da tsohon Shugaban kasar akan irin gudunmawar dabya bayar don ciyar da Najeriya gaba.

Shugaban kuma yayi bayanin cewar babu wata tsattsamar dangantaka tsakaninsa da marigayi Shehu Shagari kamar yadda wasu ke tunani.

Categories
Labarai

Shugaban kasa Buhari ya isa Sakkwato don ta’aziyar Shagari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Sakkwato domin yin ta’aziyar rasuwar tsohon Shugaban kasa Shehu Usman Aliyu Shagari.

Allah ya yiwa tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari rasuwa a ranar Juma’a, wanda aka yi jana’izarsa ranar Asabar da safe a karamar hukumar Shagari dake jihar Sakkwato.

Categories
Labarai

Zamfara: Tarihi Zai Hukunta Shugaba Buhari

 

Daga Mahmud Isa Yola

Masu ta’addanci, da masu taimakawa ‘yan ta’adda, da shugabannin da suke sakaci har ta’addanci yayi tasiri akan al’umman su suna samun kwarin guiwa ne daga abubuwa guda hudu: rashin sanin illan abunda suke yi, sanin abunda suke yi amma ba tare da kulawa da musibar da zai janyo ba, sanin illan abunda suke yi yayin da suke tunanin cewa zasu iya kaucewa musiban idan ya tashi shafan su, ko kuma kin yadda cewa abunda suke yi yana da illa.

Ba sabon labari bane a wurin mu cewa jihar Zamfara a Nijeriya ta zama cibiyar aiwatar da ta’addanci ta yanda yanzu ana lissafin kusan kowani rana ana asaran rai a Zamfara ko kuma ayi garkuwa da masu rai. Ta’ddancin kashe-kashen ba ya tsaya akan wani sashi na al’umma day aba, ana kamawa kuma a kashe matasa, ana kamawa, kashewa ko fyade ga mata, ana kamawa ko kashe tsofoffi, kai hatta kanan yara ba’a barsu cikin wannan fitinar ba.

Idan mukayi nazarin tarihin ta’addanci a Zamfara zamu fahimci cewa wannan ba shine karo na farko da fitinan ke addaban jihar ba. Asali ma, lokacin da dan takaran shugaban kasa Muhammadu Buhari yake yakin neman zaben 2015, gwamna Abdul’aziz Yari yayi alkawarin cewa ta’addancin zai zo karshe idan mutane suka bashi hadinkai wajen zaben Muhammadu Buhari.

An zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari sama da kowani dan takara a jihar Zamfara, kuri’ar da shugaba Buhari ya samu a Zamfara ko Abdul’aziz Yari, gwamnan jihar bai samu ba. Yanzu muna neman shekaru hudu kenan karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari, amma ta’addanci da sace mutane a Zamfara bai tsaya ba, asali ma, a karkashin shugaba Buhari ne aka samu kashe kashe-kashe da sace-sace irin wanda jihar Zamfara bata taba samu ba. Ba wani Buhari muke magana ba, muna magana akan mai bada umurni na kololuwa ga dukkan jami’an tsaro Nijeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tarihi zai hukunta shugaban kasa Buhari, cewa a karkashin mulkin sa ne aka samu wannan ta’addanci irin wanda jihar Zamfara bata taba gani ba. Marayu baza su ta ba mantawa da cewa an kashe iyayen su ne a karkashin mulkin sa ba, mata da suka rasa mazajen su baza su taba mantawa da cewa karkashin shugabancin Buhari aka kashe mazajen su ba, iyalai da ‘yan uwan wadanda akayi garkuwa da su, magidanta da aka kone gidajen su, fasinjoji da aka tare aka kashe a kan hanya… duka wadannan idan wani zai manta to tarihi bazai manta ba. wannan bakin fanti ne da bazai sharu ba a jikin shugaba Buhari.

Tabbas ba shugaba Buhari kadai ba, gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, shugaban rundunar ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris da dukkan wadanda Allah ya dorawa alhakin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar Zamfara tarihi bazai manta da abunda ya faru karkashin kulawar ku ba.

Duk wanda yake rike da mukami, matukar yana da kuzarin amsawa idan an ambaci mukamin sa, to ya sani, ko yana so ko baya so shine yake da alhakin wannan mukami. Idan wani abu ya faru, to babu wanda za’a kalubalanta sama da shi. Kuma ya tanadi hujjan da zai baiwa Ubangijin sa.

Ta kowani bangare akwai matsaloli. Bincike na ya nuna min cewa ba shugabanni ne kadai sukayi sakaci ba. Yanzu haka gwamnatin jihar Zamfara na kokarin gurfanar da masu rike da mukaman gargajiya na yankunan da ake gudanar da ta’addanci guda bakwai a gaban kotu, bayan an tube su daga sarauta bisa zargin su da hannu a ta’addanci. Wannan yana nuna mana ba kawai shugabannin hukumomi ba, shugabanni mafi kusa da talaka (masarautun gargajiya) suma sun taka rawar gani a tasirin ta’addanci a jihar Zamfara.

Jaridar Punch ta ranar 17/02/2018 ta ruwaito gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari yana cewa sun sunar da jami’an tsaro akwai yunkurin da ‘yan ta’adda suke yi na kai hari a wani kauye. Yari yace sun sanar da jami’an tsaro awa 24 kafin ‘yan ta’addan su kawo harin, amma hakan bai saka jami’an tsaro daukan matakin dakile wannan harin ba. ikon Allah!

Mai martaba sarkin Zurmi shima a wannan rahoton an ruwaito shi yana cewa sun san inda ‘yan ta’addan suke fakewa inda nanne dukkanin su suke zama. Ya ambaci kauyen Kagara dake iyaka da Bafarawa na jihar Sokoto, kilomita kadan daga Shinkafi na jihar Zamfara. Wannan yana nuna kenan dukkan abunda ya kamata na hadinkai gwamnan jihar da Sarkin Zurmi sun bayar ga jami’an tsaro na samar da bayanai masu inganci.

Wannan rahoto anyi shi ne tun watan biyu, yau muna watan goma sha biyu. Watanni goma bayan da aka bayyana wa jami’an tsaro inda ‘yan ta’adda suke, amma abun mamaki, shekaran jiya a jihar Zamfara sai da ‘yan ta’addan nan suka kawo hari yanda suka saba.

Menene jami’an tsaro suke yi? Idan har akwai abunda suke yi, to na kusa da su su gaya musu cewa sun gaza a wurin gudanar da aikin su saboda ana kashe rayuka kullum a jihar Zamfara.

Wannan yasa daukan matakin gaggawa ya wajaba akan shugaban kasa Muhammadu Buhari da duk wani wanda ke da alhakin shugabantan wadanda ake kashewa. Idan har jami’an ‘yan sanda sun gagara, to ayi gaggawan sake tura sojoji wadannan wurare. Idan kuma kayan aiki ne babu to ayi gaggawan wadata su da kayan aiki, saboda ‘yan ta’addan nan bayanai sun nuna suna da makamai masu karfi. Jami’an tsaro su shiga wadannan kauyuka da dajin da ‘yan ta’addan suke samun mafaka su tarwatsa su. A tabbatar an ga bayan su gabadaya. Talakawa su bada hadinkai ta hanyar samar da isassun bayanai ga jami’an tsaro kuma gwamnati ta tsaya wajen tabbatar da an hukunta wadanda suke da hannu a wannan ta’addancin.

Allah ya bamu lafiya da zama lafiya a kasar mu Nijeriya, Amin.

 

Categories
Labarai

Hukumar Hisba ta rusa dubunnan kwalaben giya a Kano

Hukumar Hisbah ya jihar Kano ta rusa dubunnan Kwalaben giyar da aka yi sumuga dinsu zuwa jihar Kano.

Tun bayan kaddamar da Shariar Musulunci a jihar Kano aka yi dokar da ya haramta shigo da giya ko shan giya a fadin jihar Kano.

Hukumar Hisba dai na bibiya tare da kake dukkan giyar da aka shigo da ita jihar ta Barauniyar hanya.

Categories
Labarai

Buhari zai kaddamar da kamfen ran Juma’a a Akwa Ibom

Shugaban masa Muhammadu Buhari zai kaddamar da yakin neman zabensa karo na biyu a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Sanata Ita Enag mai taimakawa Shugaban kasa na musamman akan harkokin majalisar dattawa ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a lokacin da yake ganawa da manema labarai a jihar ta Akwa Ibom.

Shugaba Buhari tare da Shugaban jam’iyyar APC ta kasa Adams Oshiomhole da sauran dukkan shugabannin jam’iyyar domin bikin kaddamar da takarar a ranar Juma’a.

Categories
Labarai

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da kashe kashe a Zamfara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da halin da ake ciki na kashe kashe a jihar Zamfara. Shugaban yaji takaicin hare haren da aka kai a kauyen Birnin magaji dake yankin karamar hukumar Tsafe da kuma wanda aka kai a Magami a yankin masarautar Maradun.

Shugaba Buhari yayi wannan tir ne ta bakin kakakinsa Malam Garba Shehu Wanda ya zanta da manema labarai a fadar Gwamnati dake Aso Villa yana mai yin tir da kashe kashen.