Mataimakin gwamnan Kano, farfesa Hafizu Abubakar

Mataimakin Gwamnan Kano Farfesa Hafizu Abubakar ya tabbatar da cewar ba zai shiga takarar Gwamna tare da Abdullahi Umar Ganduje ba a matsayin mataimakin Gwamna a zaben 2019 da ke tafe.

Farfesa Hafizu Abubakar ya bayyana hakan ne yau a Kano ta gidan Radiyon Rahama, inda aka sanya muryar Farfesan yana nesanta kansa da duk wani yunkuri na sake yin takara tare da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kakar zabe ta 2019.

Za a iya cewar, Farfesan mataimakin Gwamnan ya yi yankan shakku dangane da rade radin da ake yi a kansa, inda wasu mutane daga bangaren Kwankwasiyya ke gani ya yiwa ubangidansa Kwamkwaso butulci yabi Ganduje, yayin da wasu mutanan Ganduje kuma basu yadda da shi ba, suna masa kallon mai biyayya ga bangaren tsohon Gwamnan Rabiu Musa Kwankwaso.

Malam Bello Muhammad Sharada, wani mai sharhi kan al’amuran siyasar jihar Kano, yace abinda Hafizu Abubakar yayi, ya kara tabbatar da gagarumar baraka a tafiyar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a zaben 2019.

Ko kuna ganin hakan da Farfesa Hafizu Abubakar yayi ya dace?

2 COMMENTS

  1. Babu shakka abin da mataimakin gwamnan kano farfesa Hafizu Abubakar yayi, yayi dai dai, hakan kuwa shi ne zai tabbatarwa da duniya cewar farfesan da akeyimasa lakani. ba farfesan karya bane a makaranta ya samo , yayi tunani me kyau idansa bai rufe da neman mulki ba, irinsu da banne a cikin al’umma, kuma magoya bayan tsohon gwamnan jihar kano zasu tabbatar cewar farfesan yana tare da madugun tafiyar kwankwasiyya.