Categories
Labarai

Zaben Kano: Zamu karbi zabenmu a kotu – Abba K. Yusuf

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar PDP Abba K. Yusuf ya bayyana cewar zasu karbi zabensu a kotu, kamar yadda mai magana da yawun Dan takarar Gwamnan Sanusi Bature ya bayar da sanarwa.

Abu ne a bayyane cewar “an yiwa al’ummar jihar Kano fashin zabensu ta hanyar amfani da jami’an tsaro da ‘yan daba” Sanusi Bature.

Categories
Labarai

Kotu ta rushe dukkan zabukan fidda gwani na APC a Zamfara

Babbar kotun daukaka kara dake jihar Sakkwato ta soke dukkan zabukan fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Zamfara, a cewarta zaben da ya fidda Gwamna da mataimakinsa da ‘yan majalisun dokoki na tarayya da na jiha haramtacce ne.

Categories
Labarai

INEC ta ce Ganduje ne ya lashe zaben Gwamnan Kano

Hukumar zabe ta kasa reshen jihar Kano ta bayar da sanarwa a hukumance cewar Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya lashe zaven Gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris din nan.

Ganduje ya fadi a zaven farko da aka yi a ranar9 ga watan Maris, inda Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar PDP ya kayar da shi da sama da kuri’u 26,000′ sai dai kuma Gwamnan ya lashe zaven zagaye na biyu da aka kuma yi a wasu mazabu da aka soke a zaben farko.

Gwamnan Ganduje ya samu kuri’u 45,876 a zagaye na biyu da aka yi na zaben Gwamnan Kano, inda Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar PDP samu 10,239.

Categories
Labarai

Kotu ta dakatar da tattara sakamakon Bauchi

Babbar kotun tarayya dake babban birnin tarayya Abuja, ta dakatar da cigaba da tattara sakamakon Gwamnan Bauchi na karamar hukumar Tafawa Balewa.

Shugaban hukumarzabe ta kasa, farfesa Mahmud Yakubu
Categories
Labarai

Majalisar dattawa ta amince da 30,000 mafi karancin albashi

Majalisar dattawa ta kasa ta amince da Naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.

Mahalisar ta bayyana hakan nea zaman da ta yi a ranar Talata. Majalisar ta sanar da hakan ne bayan da kwamitin da aka dorawa alhakin tattaunawa kan batun karin albashi ya mika rahotonsa.

Categories
Labarai

Yaushe takaka zai san kansa?

Daga Ado AbdullahiA lokacin da al’umma ta shashance ta zama TALAUCI da JAHILCI sun yi mata katutu.

Lokacin da suke wulaƙanta kansu wajen kyale mutumin kirki, nagartacce, ƙwararre da amana a gefe. Suka gwammace a ba su kuɗi su zaɓi mutanen banza.

Lokacin da suke rigengeniyar karɓar kuɗi don zaɓen waɗanda za su damƙawa amanar rayuwarsu. Waɗanda sun sani sarai ana tuhumarsu da al’mundahana da satar kuɗin al’umma ko kuma sun yaudaresu a baya sun sace kuɗaɗen Jihohinsu.

Duk lokacin da al’umma ta zama haka toh dole wannan al’umma ta shiga ruɗani, firgici da rashin tabbas a duk al’amuranta.

Wai yaushe ne al’ummarmu za ta waye ta fita daga ƙangin bautar masu mulki, mayaudaran ƴan siyasa, maha’inta, ƴan babakere. Masu siyasar sayen ƴancin talaka da tursasashi da barazana da firgita al’umma da ƴan sara-suka, alhali ƴaƴansu suna kulle a gida ko sun tura su karatu ƙasashen ƙetare?

Sai wane lokaci ne talaka zai farka ya san cewar waɗannan ƴan siyasar da ake ɓata dare da rana wajen kare muradunsu, ba su damu da rayuwar al’umma ba, basu damu da makomar matasansu ba. Basu damu da ilmin waɗanda suka zaɓe su ba.

Duk lokacin da rashin lafiya ta kama wasunsu, kai wasu ko sayen kayan lefen bikin ƴaƴansu za a yi, sai sun dangana da ƙasar waje. Amma sun bar al’umma babu ilmi ingantacce, babu ruwan sha mai tsafta, babu asibiti nagartacce babu wani aikin yi na azo a gani. Babu……babu….. babun ba za ta lissafu ba.

Shi kuwa bawan Allah talakan sai ana daf da shiga zaɓe, sai a riƙa ribatarsa da ɗan kayan masarufin da ba zai kai shi kwana biyu ba. Ana raba musu ledar taliya guda ɗaya. Ko a basu kwalin sabulu ko biredi leda ɗaya, wasu ma da kwalin ashana ake sayensu. Ƙiri-ƙiri mun gani ana sayen ƙuri’ar talaka a kan naira 200 kacal.

Baya ga wannan yaudarar da zaluncin kuma fa, ƴaƴan wannan talakan ne ƴan siyasa suke amfani dasu wajen maguɗin zaɓe domin su ci gaba da mulkin kama karya da danne haƙƙin iyayensa, yayyensa da ƙannensa. Da shi dai ake amfani su riƙa kashe junansu alhalin mai yiwuwa wanda ya haddasa rikicin ma yana kwance a kan gadonsa zagaye da jami’an tsaro cikin kwanciyar hankali.

Wajibi ne al’umma ta farka daga ɗimuwa da rashin wayewa da rashin kwaɗayi domin neman ƴancin kanta daga azzaluman ƴan siyasa waɗanda kansu kaɗai suka sani.

Wajibi ne a dawo a sake tunani a zaɓo mutanen kirki a duk matakin da suka tsaya zaɓe. Ba tare da la’akari da sun fito a ƙaramar jam’iyya ba, ko kuma basu da kuɗin da zasu raba don a zaɓesu.

Lokaci ya yi da talakan ƙasar nan zai fara zaƙulo mutanen kirki masu son cigaban yankunansu domin su tsayar dasu takara a kowace jam’iyya ce domin samun shugabanci nagari da bijirewa tsarin kama-karya na mugaye ƴan siyasa marasa kishin ƙasa.

Ado Abdullahi
19-03-2019


Categories
Labarai

‘Yan bindiga sun sace Sheikh Ahmad Sulaiman Kano

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace fitaccen makarancin Al-qurani Sheikh Ahmad Sulaiman Kano, akan hanyarsa ta zuwa Katsina.

An sace malamin ne a akan hanyar sheme zuwa Kankara shi da wasu mutum biyar, inda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne suka sace su.

Categories
Labarai

Akuyoyi sun addabi birnin Landan


Wani garken Awaki da ya bazama a cikin unguwar Llandudno dake tsakiyar birnin Landan ya hasala jama’a, inda suke kawo tsaikon ababen hawa akan tituna da kuma yin kashi ko ina.

Awakin wadan da suka baro makiyayarsu sakamakon mamakon ruwan sama tare da iska mai karfin gaske da kuma tsananin sanyi ya sanya suka bazamo cikin gari.

Mai magana da yawun mazauna unguwar, ya bayyana cewar bazamowar awakin a wannan lokacin ba sabon abu bane, saboda a cewarsa a kowace shekara a irin wannan lokaci awakin kan nemi mafaka.

Categories
Labarai

Rubzawar gini kan ‘yan makaranta a Legas

Wata mata ta rasa yaranta guda biyar a sanadiyar rusau da wani gini yayi a kan daliban wata makaranta a jihar Legas.

Matar ta bayyana cewar yaran nata biyar ne suka rasu a sanadiyar wannan gini da ya rufto kan ‘yan makaranta.

Matar tace yaran nata sun dawo gida sakamakon rashin biyan kudin makaranta, suna zaune mako guda a gida, kwana days bayan sun koma makarantar wannan lamari ya auku.