Categories
Labarai

An rantsar da Buhari karo na biyu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki a matayin Shugaban kasa karo na biyu.

Categories
Labarai

Ganduje ya wuce gona da iri kan Sarkin Kano – Sarkin Ningi

Daga Yaseer Kallah

Mai Martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, ya bayyana cewa kowanne irin kuskure Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya aikata, bai kyautu gwamnatin jihar ta tsaurara hukunci a kanshi haka ba.

Sarki Ningi ya shawarci ‘yan siyasa da gwamnatoci da su dinga yin juriya da hakuri a gurin hukunta sarakunan da suka aikata wani kuskure.

Yake cewa: “Abin da ya fi muhimmanci a gurinmu shi ne mu bai wa dukkan bangarorin da abin ya shafa hakuri. Da farko, a gaskiya ba ma farin ciki da abin da ya faru a Kano. Na yarda na yi magana a kan wannan batun kawai saboda matsayina na daya daga cikin tsoffin sarakuna a Arewa; a kan karagar mulki da kuma shekaru.

“Ba ma musu a kan cewa mai yiwuwa sarkin ya aikata wani abu da ba daidai ba. Mutum ne shi, amma shawararmu ita ce, in akwai wata ketare iyaka a bangaren sarkin, bai kyautu matakin da za a dauka ya yi tsananin da har ya ketare shi ya shafi gaba dayan masarautar da mutanenta ba.

“Dole ‘yan siyasa da gwamnatoci su zamo masu juriya da hakuri a kan hukumomin gargajiya. Ya kuma kyautu su zamo masu sassauta hukunci tare da afuwa ga sarakunan da suka aikata wani abu da ba daidai ba. Kada su zamo masu matukar tsanani a kan hukumomin gargajiya kamar yadda muka gani a jihar Kano. A gurina, abin takaici ne abin da ya faru a Kano, kuma karshen abin tsammani.

“Tun zamanin mulkin mallaka, bayan samun ‘yancin kai da lokacin Sardauna, ba a taba cin zarafin hukumomin gargajiya ba kai-tsaye kamar a wadannan lokutan. Hukumar gargajiya na hade da tarihi da al’adar mutane. Daga lokacin da aka lalata hukumar gargajiya, gaba dayan tarihi da al’adar mutane za su baci.

“Ya Kamata Gwamnatin jihar Kano, Masarautar Kano da Majalisar Dokokin jihar Kano su hada kai; su aje ra’ayi a gefe domin tseratar da tarihinmu da al’adarmu mai matukar muhimmanci.”

Categories
Labarai

Raba Masarautar Kano: Akwai lauje cikin nadi


Daga Huzaifa Dokaji


Tarihi shine jigon dukkan wata al’umma. Babban burin dukkan al’ummar da ta san knata shine gina tare da kare tarihinta. Kasashe da dauloli da dama, kamar Kasar Sin da Daular Farisa sun yi shura kwarai wajen riko tare da dabbaka al’adunsu.
Kasar Kano kasace da ta shahara a fadin duniya. Kano ta yi fice saboda dimbin tarihin da masarautarta ta kafu a kai. Kusan ma iya cewa babu wani gari a kasar Hausa ko ma a Afirka ta Yamma da ya ja hankalin ko da Turawan Mulkin Mallaka irin Kano. Ra’ayin irin wadannan Turawa da daman na kara nuni da hakan. Misali, Lugard ya taba fadar cewa tunda yake, bai taba tunanin a Afrika za a samu wani abu da zai hankalinsa ya burgeshi ba irin badalar Kano. Robinson ya siffanta Kano a matsayin Landan din kasasehen bakar fata. Babban abinda ya kai Kano wannan matsayi shine tsari da fasalin masarautar da ke mulkin ta.
Tarihin Kano ya kafu ne akan Sarauta. An fara sarauta a Kano kimanin shekaru dubu da suka shude. Tsahon wannan Shekaru, zuri’ar mutum biyu ne kawai suka mulki Kano in ban da dan takin da Sarki Sulaimanu dan Aba Hamma (1807-1819) yayi mulki bayan Fulanin Jihadi sun ci Kano da yake. Duk da sauya-sauyen da Jihadi ya kawo a tsarin rayuwar mazauna kasar Hausa, Jihadin bai samu damar sauya tsarin sarautar Kano ba. Ma iya cewa, maimakon ma Jihadi ya ci sarautar Kano da yaki, Sarauatr Kano ce ta ci masu Jihadin da yakin al’ada.
Zuwan Turawan mulkin mallaka ba chanja wannan tsari na kusan karni 8 ba. Turawa sun bar al’ada yanda suka tarar da ita. Ko da yake an kirkiri gundumomi guda 24 a shekarar 1906 saboda gyara harkar karbar haraji, sai dai fasalin gundumomin bai saba da ainihin tsarin mulki na kasar Hausa ba. Wannan tsari, ko da gwamnatin Alhaji Abubakar Rimi da ta zo, duk da ta raba masarautar ta hanyar daga darajar sarakunan yanka zuwa daraja daya da Sarkin Kano, sai dai ba ta ci zarafin tsarin gunduma ba. Kowanne sarki an bashi iya abinda tarihin kasarsa ya mallaka masa ne. Rimi bai kirkiri wata sabuwar masarauta da babu ita a jiyan Kano ba.
Matakin da Sardauna ya dauka ne tsige Sarakunan da aikinsu ya saba da abinda gwamnatinsa take sa rai, ya nuna cewa bakar fata ma na da karfi da dama cire rigar Sarakunan a sabuwar tafiar yancin kai da aka dauko. Bugu da kari, cire Sarkin Musulmi da Janar Babangida da Janar Abacha su ka yi, ya nuna cewa babu wani Sarki da zai tsira daga siyasar mulkin zamani. Matakin da Rimi ya dauka na sauya fasalin matsayin wasu daga cikin sarakunan yanka da ke cikin yankin tsohuwar Jihar Kano ya kara bude wata kofa a tarihin Kano wadda ko Sardauna bai bude ta ba. Matakin na Rimi ya daga martabar Sarakunan Gaya, Rano dss zuwa daraja daya da ta Sarkin Kano. Hakan ya nuna cewa ba wai iya Sarkin Kano ba, a’a, masu mulki na da damar yiwa al’adar Kano hawan kawara matukar hakan zai biya bukatarsu ta siyasa. Hakan ya jawo rudu kwarai musamman ganin cewa ko da Turawan mulkin mallaka na taka tsantsan wajen aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi harkar gargajiyar Kano.
Wannan yunkuri na Gwamna Rimi ya fuskanci tawaye daga mutane da dama a ciki harda malaminsa na siyasa wato Malam Aminu Kano. Kamar yadda Alan Feinstein ya rawaito a littafinsa na African Revolutionary, Malam ya siffanta aikin na Rimi da ‘tabin hankali’ ko kuma “zauta”. Duk da akan tarbiyar Malam din Rimi ya tashi tare da kuma gina hujjarsa ta yiwa masarautar ta Kano fyadar ‘ya’yan kadanya, Malam din ne ya bada shawara mafi girma ta yanda za a bata wannan yunkuri na Limamin Chanji.
Tashin hankalin da ya biyo bayan wannan abu da Rimi yayi, ya dakushe yunkurin yan siyasa da suka biyo baya na daukan matakai tsaurara akan sarakunan gargajiya ko da akwai bukatar hakan. A bangaren Sarakunan kuma, hakan ya zama izna na su kame bakunansu daga al’amuran siyasa. Wannan ka iya zama dalilin da yasa mutane da dama a Arewa ke kallon Sarakunan a matsayin mutanen da ba sa kishin al’ummarsu. An dinga nunen yatsa akan cewa Sarakuna jemagu ne, masu goyawa mai mulkin da ke da dama, wanda hakan ya saba da tarbiyyar magabatnsu da su kai ta fama da Turawa akan abinda ya kamata da wanda bai kamata ba. Idan mu ka dawo Kano, kame kai daga tsoma baki a harkar yan siyasa bata hana tangarda tsakanin Sarki Ado da gwamnonin da suka biyo bayan Rimi ba. Wasu an sani, wasu kuma a boye suka faru. Kame bakin da Sarkin ya yi na tsahon lokaci ya zama al’adar Sarakuna da dama har wasu na ganin hakan shi ne abinda ya kamaci masu mulkin gargajiya.
Sai dai shirun na Mai Garin Birni ya kuma samun sauyi a lokacin da Malam Ibrahim Shekarau ya hau mulki. Tsananin biyayyar da Shekarau ya nuna masa, ta kai ga har marigayin ya yi masa sarautar Sardaunan Kano, kuma ya nada shi dan majalisarsa. Kalaman Sarkin ga dan takarar da Sardaunan ya tsayar, wato Mal Salihu Sagir Takai, sa’ilin da ya kai masa ziyarar neman albarka, sun kara kafa tushen fadada rashin fahimta tsakanin marigayin da Kwankwaso. An buga tataburza ainun wanda ba dan shiga tsakani da manyan mutane irinsu Marigayi Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim su ka yi ba, da ba a san iya abinda rikicin zai zama ba.
Yau ma dai, ga mu cikn wani rikicin tsakanin sabon sarki da gwamnatin Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Shin wannan takaddama ta Sarki da gwamnan ta na da kamanceceniya da waanda suka gabaceta? Ma iya cewa akwai alaka saboda abu biyu. Da farko dai, dukkan gwamnonin da suka samu tsattsamar alaka da masarautar ta Kano almajiran Malam Aminu Kano ne. Na biyu, dukkansu ‘ya’yan dagatai ne. Watakila hakan ne ma ta su wasu ke ganin rigimar ba wani abu bace face tsohuwar rigimar nan ta tsakanin ‘ya’yan dagatai da ‘ya’yan hakimai ko Sarakuna.
Shin yunkurin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na raba masarautar ta Kano shi ma tasiri ne na wadannan abubuwa guda biyu da aka fada a baya? Ko kuma da gaske ya yi hakan ne domin ci gaban al’umman yankunan da abin ya shafa? Amsar wadannan tambayoyi na da alaka kwarai da juna. Lallai akwai raba hanya tsakanin manufar Gwamnatin Rimi, Kwankwaso da ta Ganduje. Sa’ilin da ya zama gwamnatin Rimi ta nuna damuwarta kwarai da bukatar ‘ya’yan talakawa, wannan gwamnati ba ta da alaka mai karfi da irin wannan manufa. Idan kuwa haka ne, akwai alamar tambaya kwarai akan kyawun niyyarta a wannan yunkuri musamman duba da hangar da ta bi domin cimma manufar ta ta raba masarautar ta Kano. Idan muka dora rikicin a mizanin na Kwankwaso da Sarki Ado, za mu ga cewa suna kama da juna ta fuskar dalili. Duka rikicin guda biyu sun faru ne akan zargin gwamnonin na cewa Sarakunan basu basu goyon baya ba a wajenmatasa. Idan kuwa har hakane, akwai bukatar mu duba dalilan sarakunan.
Kididdigar masana a fadin Najeriya ta nuna cewa babu jihar da ta kai Kano yawan almajirai da matasa marasa ilimi da aikin yi. Sanin kanmu ne cewa kaso mafi tsoka na wadannan matasa sun fito ne daga bangare da Mai Girma Gwamna yake kokarin kafa sabbin masarautu. Akwai bukatar a duba cewa wadannan yankuna sun fi bukatar ilimi, aikin yi da tsaro akan masarautu. A wannan yanayi na tsitsistsi da kowacce kasa ke kokarin rage kudaden da take kashewa na gudanarwa, babu hikima gwamanatin da ba ta iya rike masarauta daya da kyau ba, tace zata kara har wasu guda hudu. Akwai siyasa kwarai idan aka duba cewa gwamnnati ba ta yi la’akari da wadannan abubuwa ba kafin ta kara masarautun. Domin kudaden da za a kashe wajen gina gidajen sarautun da sarakunan da hakimansu za su zauna, da albashin da za a dinga biyansu da motocin hawan da za a siyawa kowannensu sun isa a kaddamar da ayyukan ci gaban al’umman wadannan yankunan.
Akwai bukatar jama’a su yiwa wannan abu karatun ta nutsu ta hanyar neman gamsassun bayanai daga wakilan da suka zartar da wannan ta’asa. Misali, me yasa zartar da wannan doka ya yi daidai da zartar da dokar albashin dindin ga shugabancin majalisar ta Kano? Shin akwai alaka tsakanin burin shugaban majalisar na Kano na zama ‘kingmaker’a masarautarsa ta Rano da yake rike da sarautar Turakin Rano musamman duba da cewa dokar ta shigar da mai rike da wanan sarauta, kamar yadda wata jarida ta rawaitar a rahotonta na musamman akan rikicin? Shin akwai alfanu gwamnatin da bata iya samar da kudin shiga na a zo a gani ta kara sabautar da asusun jihar Kano saboda bukatarta ta kirkirar masarautu da kuma biyan kudin kwalliya ga wadanda suka tayata tabbatar da wannan kudiri? Yanzu shikenan an yi amfani da karfin mulki an murde zabin mutanen Kano, amman duk bai isa ba, kuma sai an kara bin tarihi da al’adarsu an musu dukan kawo wuka? Shin ina laifin sarki idan yace mutane su zabi shugabanni na gari, wadanda za su kare mutuncin Kano da mutanenta? Ko dai biri ya yi kama da mutun ne, shi ya sa mai suna ya amsa sunansa?

Categories
Labarai

Babu Rigima Tsakanin Izala Da Darika — Sheikh Bala Lau

Daga Mahmud Isa Yola

Shugaban kungiyar Izala ta kasa Ash-Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau ya gargadi masu yada jita jita a kafafen yada labarai wai cewa kungiyar Izala na takun saka da ‘yan Dariku.

Sheikh Bala Lau yana magana ne akan wasu rahotanni da cikin kwanaki biyun nan suke yawo a jaridu cewa wasu ‘yan Darika sun far wa Sakataren Kungiyar na kasa Sheikh Dr. Muhammadu Kabiru Gombe a Kaduna inda ya sha da kyar.

Bala Lau ya muzanta labarin ne a yau jumma’a a majalisin Tafsirin sa da ke Yola, inda yace babu kanshin gaskiya a cikin wannan rahoton, kuma wadanda suke yada rahoton suna yi ne don bibiyar kungiyar da sharri da makircin su.

“Tsakanin wurin tafsirin Sheikh Kabir Gombe da inda Sheikh Dahiru Bauchi yake akwai nisa sosai, babu wani abu da ya faru. Kungiyar Izala bata rigima da ‘yan darikar Tijjaniya ko wasu, sun san matsayin su, mun san matsayin mu” inji Sheikh Bala Lau.

Shehin malamin yace suna sane da wadansu sun sha alwashin farraka kungiyar Izala saboda matsayar da kungiyar ta yi a zaben 2019 da ya gabata. Yace babu shakka wadannan sune suke bibiyar kungiyar da sharri don su ga sun zubar da kiman shugabannin ta a idon al’umma.

Sheikh Bala Lau yayi kira ga masu yada rahotannin su ji tsoron Allah, su kasance masu yada gaskiya ba sharri ba. Yace babu amfanin yada abunda bai faru ba a cikin al’umma, kuma Qur’ani yayi gargadi akan hakan a wurare da dama.

Categories
Labarai

GUZURIN RAMADAAN: Zamantakewa Tsakanin Musulmi Da Wanda Ba Musulmi Ba

Daga Mahmud Isa Yola

Shiga Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama Na Hilf al-fudul Da Manzon Allah SAW Yayi

A lokacin jahiliyya, a cikin garin Makka kuma a karkashin mulkin jahiliyya, Manzon Allah SAW ya shiga wata kungiya da ake kira da Hilf al-fudul. Kungiyar tana fafutukar kawo zaman lafiya da kuma bi wa duk wanda aka tauye wa hakki hakkin sa a cikin garin Makka.

Har lokacin da musulunci ya kafu a garin Madina da Makka, Manzon Allah SAW bai bar kungiyar ba. Talha dan Abdallah yake cewa “idan da an sake gayyatan Manzon Allah zuwa makamancin kungiyar a lokacin da Musulunci ya mamaye garuruwan Makka da Madina da zai amsa gayyata kuma ya shiga kungiyar.” (Sunanul Kubura 12114, Aldala’il Gharib 243).

Ibn Hashim yace su ‘yan kungiyar na Hilf al-fudul sun yaddan wa kansu cewa babu wani wanda za’a tauye wa hakki cikin mutanen su ko kuma duk wanda ya shiga garin Makka ba tare da sun bi masa hakkin shi ba.(Musnad Ahmad 2904).

Saboda haka ne malamai suka cewa musulmai, ko da a wuraren da basu ne ke rike da gwamnati ba, yakamata su kasance suna kwatanta gaskiya kuma suna kin duk wani abu da bai dace ba a gwamnatance iya gwargwado. Wannan yana nuna mana yin amfani da addini wajen tozarta wasu ko da ba musulmai bane babban kuskure ne kuma sabawa Allah ne da Manzon Sa.

Mu hadu a fitowa na gaba.

(ABUN LURA: wannan rubutu na guzurin Ramadan zai rika zuwa muku a shafukan jaridun Hausa tareda marubuci Mahmud Isa Yola)

Categories
Labarai

Tilas Buhari yayi bayanin nawa ne a Bital mali – Aminu Beli

Wani tsohon dan siyasa a jihar Kano Comr. Aminu Sa’ad Beli, yace akwai bukatar gwamnatin tarayyar Najeriya ta yiwa ‘yan kasa cikakken bayanin adadin kudin da gwamnatin Buhari ta tara izuwa yanzu a asusun bai-daya (TSA).

Aminu, ya wallafa wannan magana ne yau Talata a shafin sa na Facebook cewa “An fara tafikar da asusun ajiya na bai-daya (TSA) tun a shekarar 2012 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Jonathan, inda a wancan lokaci aka tara kudi zambar N30tr.”

“A don haka nauyi ne akan gwamnatin Muhammadu Buhari ta fito ta yiwa ‘yan Najeriya bayanin nawa ne aka tara izuwa yanzu a cikin asusun ajiya na bai-daaya, kamar yadda gwamnatin Jonathan ta yi.” Cewar Comr. Beli.

www.muryaryanci.com

Categories
Labarai

Mutanan Gama sun koka kan ayyukan da aka fara lokacin zabe ba’a gama ba

Mazauna unguwar Gama daka Kano sun koka kan ayyukan da Gwamnan Kano ya fara kuma bai kammala ba yayin zaben cike gurbi a mazabar da akai a yayin zaben 2019 da ya gabata.

Auwal Danlarabawa daya daga cikin mazauna unguwar Gama ya bayyana kokensu kamar haka:

“Burtsatsen Masallacin Yara layin Makarantar adfalu tunda aka haka aka barta ba tare da an saka solar ba Ballantana Batir zuwa karasa ta yadda Za’a anfana da ita kuma mun san yadda akayi kokarin wannan aikin Dan a Tallafawa Al’umma musanman akan Matsalar ruwan Sha da ake fama dashi a Mazabar Gama.

Dama wasu kuma muna Kara Kira da a duba solar din da aka Sakawa Burtsatsen Dan akwai bukatar ya zama kowacce tana da Batir kamar yadda ka umarci Ayi ingantaccen aiki wanda Za’a Dade ana anfani da tagomashin da ka kawo wannan Mazaba.

Muna Fatan Za’a duba wannnan koke tare da share mana Hawaye Dan kar a cigaba da cewa Rijiya ta bayar guga Ya Hana.”

Categories
Labarai

GUZURIN WATAN RAMADAN: Addu’ar Ganin Jinjirin Wata

Daga Mahmud Isa Yola

Bismillahirrahmanirrahim. Dukkan godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, mai kowa mai komai, mamallakin kowa da komai, cikin rahamarSa yau muna kwanan wata 29 ga watan Sha’abaan. Hakan na nuna cewa idan dai an ga jinjirin wata, to gobe Insha Allahu zai kasance daya ga watan Ramadaan. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah Annabi Muhammad SAW.

Bayan haka, yaku ‘yan uwa kamar dai yanda muka saba kawo muku rubutu a watan ramadaan mai taken GUZURIN WATAN RAMADAAN, a wannan shekarar ma mun shirya tsaf don cigaba da kawo muku Ayoyi da hadisai cikin bayanan manyan malamai akan hukunce hukuncen da suka shafi Azumi.

Yaku ‘yan uwa, mu sani cewa watan Ramadaana wata ne mai falala da yawa, rubutun mu na gaba zai kawo mana su Insha Allah. Saboda haka, mu lizimci dukkan wani aiki na alkahairi don neman rahamar Ubangiji, kuma mu nesanci dukkan wani zunubi don gujewa fushin Ubangiji SWT a wannan wata mai dumbin falala.

Yazo a cikin Hadisi wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito, Manzon Allah SAW yana cewa: “ku dau azumi da kallon jinjirin wata (Ramadaan), kuma ku ajiye azumi da kallon wata (Shawwaal)”. Wannan yasa babban sharadi na azumin Ramadaan shine ganin wata.

To a nan, menene musulmi yakamata yayi idan ya ga wata?

Ya tabbata a sunnah cewa idan aka ga wata akwai addu’a da ake yi. Wannan addu’ar kuwa ita ce “Allahumma ahillahu alaina bil Amni, wal Iman, wal Salaama, wal Islam, Wat Taufiq Lima tuhibbu wa tarda, Rabbuna wa Rabbuka-Llah”. [At-Tirmidhi]

Ma’anar sa, “Ya Allah Ka Sa (wannan wata ya kasance) na samun tsaro, da Imani, da zaman lafiya, da musulunci da dacewa ga abunda Kake So, Mahaliccin mu kuma Ubangijinka Allah.”

Daga karshe yaku ‘yan uwa mu daura damara sosai na ibadaa sosai tare da ikhlasi. Mu shirya karanta Al-Qur’ani, Tarawi, Sadaka, ciyarwa, da sauran ayyuka na neman yaddan Allah.

Allah Nuna mana watan Ramadaan Lafiya, Allah Sanya mu cikin bayin Sa ‘yantattu.

(GUZURIN WATAN RAMADAAN RUBUTU NE NA MUSAMMAN AKAN AZUMI, TARE DA MARUBUCI MAHMUD ISA YOLA. ZAI DINGA ZUWA MUKU A JARIDUN HAUSA)

+2348106792663 (Text only)

Categories
Labarai

‘Yan bindiga sun kai hari gidan Bafarawa

Daga Nura Aminu Dalhatu

A jiya da dare kusan karfe 9:00 na dare wasu yan bindiga suka kai farmaki a gidan tsohon gwamnan jahar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa (Garkuwan Sokoto) dake garinsu na Bafarawa.

Lokacin harin yan bindiga sun kashe mai gadin gidan Malam Abdullahi Jijji tare da sace wani yaro a gidan mai suna Abdulrasheed Sa’idu daga cikin yaran dake a gidan.

Haka ma yan bindigar inji bayanin daga kauyen sun yi alkawalin kakkabe kauyukan guda biyu na Bafarawa da Kamarawa daga kasa baki daya.

Allah Ya kawo sauki!

Nura Aminu Dalhatu
Bafarawa Media Aide
4th May 2019.

Categories
Labarai

Ya kamata Gwamnoni su yi koyi da Buhari -Ribadu

Nuhu Ribadu

Tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu ya yai kira ga gwamnonin kasar nan na su yi koyi da irin halayyar Buhari a wajen mulkin mutanen jihohin su.

Ribadu yayi wannan kira a wajen taron wanke sabbin gwamnoni da ma tsoffi da kayi a Abuja.

” Ku duba ku gani, irin halayyara shugaba Muhammadu Buhari, bashi da wasu abokanai wai ‘yan kasuwa da za ace wai kullum suna tare dashi a ana shirya harkalla. Sannan yadda ya soma a 2015 haka yake har yanzu, bai siya ba kuma bai gina ba.

” Kun gani yanzu lokacin zama attajiri farad daya ya wuci a dalilin salon mulkin Buhari. Aiki dabam, wasa da bam.”

A tsokaci da yayi game da dalilan da ya sa hukumomin binciken ta kasa ke bibiyar gwamnoni, Ribadu ya ce “Ku ne ke da hakkin tafiyar da gwamnatin ku. Ku ne kuma ke rike da komai na dukiya, albarkatu da makudan kudaden jiha, har ma da na kananan hukumomi.” Cewar Ribadu.

Ya yi wannan tsinkaye ne a lokacin da ya ke jawabi wurin taron sanin makamar aiki da aka shirya wa zababbun gwamnoni, jiya Talata, a Abuja.
Daga nan sai Ribadu ya nanata cewa babu yadda za a yi a ce gwamnoni ba a bincike su ba.

Ya ce kai hatta ma wanda suka zabo da kan su domin ya gaje su, zai iya binciken su, kamar yadda tarihi ya nuna ba da dadewa ba a baya.

Daga nan sai Ribadu ya ce jami’an tsaro na duniya su na bibiyar duk lunguna da sako-sakon da kudade ke shiga, saboda yawaitar safarar muggan kwayoyi, ta’addanci da ya buwayi duniya da kuma shugabanni masu wawurar kudade.

Daga

Premium Times