Home Labarai Majalisar dokoki ta Zamfara ta zartas da kudirori 40 cikin shekaru 3

Majalisar dokoki ta Zamfara ta zartas da kudirori 40 cikin shekaru 3

0
Majalisar dokoki ta Zamfara ta zartas da kudirori 40 cikin shekaru 3

 

 

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta ce ts zartar da kudirori 40 cikin shekaru uku, kamar yadda kakakin majalisar, Nasiru Magarya ya bayyana.

Magarya ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Gusau a yau Laraba.

“A cikin shekaru uku da suka gabata, majalisa ta shida a jihar nan, karkashin jagorancina ta samu nasarori masu tarin yawa.

“Daga cikin nasarorin da aka samu shi ne zartar da ƙudirori sama da 40 kuma mafi yawansu Gwamna Bello Matawalle ne ya amince da su.

“Dukkan ƙudirorin sun shafi al’umma ne kai tsaye kuma babu wani ƙudiri da aka zartar domin buƙatar kan mu.

“An zartar da dukkan ƙudirorin ne ta hanyar amfani da ƙa’idojin majalisa, musamman sauraron ra’ayoyin al’umma” inji shi.

Shugaban majalisar ya danganta nasarorin da aka samu da alaƙa mai kyau tsakanin ɓangaren zartaswa da na majalisar dokoki a jihar.