Home Labarai YANZU-YANZU: Gwamnatin Taraiya ta rufe Sahad Store da ke Abuja

YANZU-YANZU: Gwamnatin Taraiya ta rufe Sahad Store da ke Abuja

0
YANZU-YANZU: Gwamnatin Taraiya ta rufe Sahad Store da ke Abuja

YANZU-YANZU: Gwamnatin Taraiya ta rufe Sahad Store da ke Abuja

Sa’o’i 24 bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shirin sa na magance matsalolin dake haifar da matsalar abinci, hukumar kula da hakkin mai saye ta ƙasa, FCCPC, ta rufe Sahad Store Supermarket da ke Garki a Abuja.

An dai zargi Sahad da yaudarar kwastomomi ta hanyar cajin su farashi sama da yadda ya ke a manne a jikin kaya.

Shugaban FCCPC na riko, Adamu Ahmed Abdullahi ne ya jagoranci samamen.

Da yake zantawa da manema labarai bayan rufe kantin, Abdullahi ya ce binciken farko da hukumar ta gudanar ya tabbatar da cewa masu manyan kantunan na zaluntar kwastomomi.

Ya ce kantin zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai an kammala bincike.

“Abin da muka gano cewa wadannan mutane suna yi shi ne yaudarar kwastomomi da farashi na rashin gaskiya, wanda ya saɓa da sashe 115 (3) na dokar da ta ce dole.a sayarwa da kwastoma kaya kan farashin da aka manna a jikin kaya.”

“Za kuma a ci tarar kantin Naira miliyan 100 sannan daraktocin sa za su biya tarar miliyan goma-goma a kulle su watanni shida ko a haɗa musu duka biyun idan aka sake su da lefi.,”

“Dole ne kuma su tabbatar da cewa sun cika ka’idoji kafin a buɗe musu supermarket din,”