0

An yi garkuwa da Haj. Halima Adamu, mahaifiyar fitaccen mawakin Hausan nan, Dauda Adamu, wanda aka fi sani da Rarara.

An sace ta ne a gidanta da ke kauyen Kahutu a karamar hukumar Danja a jihar Katsina, kamar yadda wata majiya ta bayyana.

Majiyar ta ruwaito cewa ƴan bindigar sun shiga kauyen ne da misalin karfe 1 na daren yau Juma’a inda suka yi garkuwa da tsohuwar.

Majiyar ta ƙara da cewa ƴan ta’addan sun shigo garin ne da kafarsu ba tare da wata hayaniya ba l, kuka ko yin habi ba su yi ba a lokacin aikin, wanda ya dauki tsawon mintuna kadan. Matar ba ta yi turjiya ba lokacin da suka nemi ta taho tare da su,” majiyar ta bayyana.

“Duk da cewa akwai wasu mutane a gidan, yan bindigar sun tafi da mahaifiyar Rarara ne kawai, suka bar sauran. Babu wani yunkuri na tunkarar ‘yan bindigar da ke dauke da makamai.”

“Wataƙila sun ajiye baburansu daga nesa suka yi tattaki zuwa ƙauyen. Muna addu’ar Allah ya dawo da ita lafiya domin tana da mahimmanci a gare mu. Ɗanta mai suna Rarara yana kyautata mana sosai, ya kawo ci gaba da yawa a ƙauyenmu,” in ji majiyar.”

Kokarin jin ta bakin fitaccen mawakin Hausa ta wayar tarho ya ci tura, saboda an kasa samun sa a kiran da aka yi masa.

Daily Trust