
Wani matashi dan shekara 11, Nelson George, ya shigar da kara ta Naira miliyan 100m a kan asibitin Limi Children’s Hospital Limited bisa zargin rashin ƙwarewa da ya kai ga lalacewar ɗan marainan sa.
Nelson, wanda ya shigar da karar ta hannun mahaifinsa, Bankole George, ya kuma roki mai shari’a Akanbi Yusuf na babbar kotun tarayya da ke Kubwa, da ya ba da umarnin cewa asibitin ya biya shi kudi naira miliyan 5 a matsayin kudin shigar da karar.
A cikin karar mai lamba: FCT/HC/CV/7356/2023 mai kwanan 28 ga watan Agusta ta hannun lauyansa, Emmanuel Ekpenyong na Fred-Young & Evans LP, Nelson ya kara da rokon kotun da ta baiwa asibitin umarnin su bashi hakuri a rubuce a bisa ta’asar da aka yi masa.
Mai shigar da ƙarar ya kuma hada da wasu ƙungiyoyin kiwon lafiya guda hudu a matsayin waɗanda ake kara na 2 zuwa 4 a shari’ar.
Haka kuma ya bukaci kotun da ta bayyana cewa ya kamata wadanda ake kara na 2 zuwa na 4 su kara kaimi wajen ganin sun gudanar da ayyukansu a karkashin ikonsu kamar yadda dokokin da suka kafa su ke ba da kariya da inganta muradunsa da jin dadinsa, ciki har da na ‘yan uwa al’ummar Najeriya.
A cikin sanarwar da ya bayar ta hadin gwiwa, Nelson ya ce yana da shekaru 11 a halin yanzu “a karamar Sakandare aji 3 kuma yana zaune a karkashin iyayensa, Bankole George wanda shine mai kula da shi.”
Har yanzu wadanda ake tuhumar ba su amsa kiran kotun ba har zuwa lokacin wannan rahoton.
Mai shari’a Yusuf ya sanya ranar 20 ga watan Disamba domin sauraron karar.