Home Labarai A yi adalci a shari’ar zaɓen gwamnan Kano, Sheikh Dahiru Bauchi ya shawarci Kotun Ƙoli

A yi adalci a shari’ar zaɓen gwamnan Kano, Sheikh Dahiru Bauchi ya shawarci Kotun Ƙoli

0
A yi adalci a shari’ar zaɓen gwamnan Kano, Sheikh Dahiru Bauchi ya shawarci Kotun Ƙoli

Jagoran ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi, ya nemi Kotun Ƙolin ƙasar ta yi adalci a hukuncin da za ta yanke game da shari’ar zaɓen gwamnan jihar Kano da ke arewacin ƙasar.

Cikin wata wasiƙa da ya rubuta wa Alƙalin Alƙalai Olukayode Ariwoola, shehin malamin ya bayyana Kano a matsayin “cibiyar kasuwanci da addini ta arewacin Najeriya”, abin da ya sa ya kamata “a ci gaba da ririta zaman lafiya da haɗin kan Najeriya ke nan”.

Ya rubuta wasiƙar ce tun a farkon watan Disamba amma sai ranar Juma’a ta ɓulla, kamar yadda wani daga cikin ‘ya’yan malamin ya shaida wa BBC Hausa.

“Na rubuto maka wasiƙa ne saboda na jaddada cewa ya kamata a yi adalci a wannan shari’a ba tare da tsoro ko nuna ɓangaranci game da ra’ayin ‘yan ƙasa ba, wanda suka bayyana kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada,” in ji shi.

A ranar Alhamis ne kotun ta fara zaman sauraron ƙarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗaukaka a gabanta bayan kotun ƙararrakin zaɓe da ta ɗaukaka ƙara sun soke nasarar da ya samu a zaɓen watan Maris tare da bai wa Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC nasara.

Daga cikin ƙorafe-ƙorafen da Abba da jam’iyyarsa ta NNPP suka shigar gaban kotu ƙolin har da batun takardun bayanan shari’a na kotun ɗaukaka ƙara, waɗanda suka dinga yin tifka da warwara game da wanda ya yi nasara a kotun.

Kotun ta ajiye ranar da za ta faɗi hukuncin nata amma ba ta faɗi rana ba tukunna.

BBC Hausa