Home Labarai Ƴan ta’adda sun kashe kansila a Adamawa

Ƴan ta’adda sun kashe kansila a Adamawa

0
Ƴan ta’adda sun kashe kansila a Adamawa

 

Ƴan bindiga sun afka gidan wani kansila a Jihar Adamawa kuma su ka kashe shi.

BBC Hausa ta rawaito cewa Ƴan bindigan sun shiga gidan Honarabul Ishaya Bakano ne da daren Juma’a wayewar garin Asabar a Ƙaramar Hukumar Song inda suka harbe shi.

Mai magana da yawun ƴan sanda reshen Jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce bayan an harbi kansilan an garzaya da shi asibiti amma rai ya yi halinsa.

DSP Yahaya ya kuma tabbatar da cewa ƴan bindigar sun harɓi ɗaya daga cikin ƴaƴan kansilan wanda yanzu haka yake jinya a asibiti.

Kafin rasuwarsa, Honarabul Ishaya ya kasance kansila mai wakiltar mazaɓar Gudu Mboi da ke Ƙaramar Hukumar Song ta Jihar Adamawa.