Home Labarai Addu’a ce kaɗai maganin rashin tsaro a ƙasar nan, in ji Yari

Addu’a ce kaɗai maganin rashin tsaro a ƙasar nan, in ji Yari

0
Addu’a ce kaɗai maganin rashin tsaro a ƙasar nan, in ji Yari

Sanata Abdul’aziz Yari (APC-Zamfara) a jiya Talata ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da addu’o’in kawo karshen ƴan fashin jeji da masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a kasar nan.

Yari, wanda ke wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, ya yi wannan roko ne a lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki na ‘yan siyasa 147 na Zamfara a gidansa da ke Talata-Mafara.

A cewarsa, addu’a ce kadai za ta iya magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta da sauran sassan kasar.

“Kalubalen tsaron da ake fama da shi a kasar nan na kara ta’azzara duk da matakan da gwamnati ta dauka na magance shi.

“Abin takaici ne, ayyukan rashin tsaro sun kara zama ruwan dare a kullum a cikin al’ummominmu.

“Saboda haka, dole ne mu dage da addu’o’in neman taimakon Allah don kawo mafita mai dorewa a kan matsalar,” in ji shi.