Home Labarai Ma’aikatan Hukumar kula da Ƴan Sanda za su tafi yajin aiki

Ma’aikatan Hukumar kula da Ƴan Sanda za su tafi yajin aiki

0
Ma’aikatan Hukumar kula da Ƴan Sanda za su tafi yajin aiki

 

 

Majalisar hadin guiwa ta hukumar ‘yan sanda ta fitar da sanarwar yajin aiki na sai-baba-ta-gani ga mahukuntan hukumar saboda saɓa yarjejeniyar da aka cimma.

Ƙungiyar ta bayyana cewa yajin aikin zai fara aiki ne daga ranar Litinin 29 ga watan Agusta, 2022.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan hadin gwiwar, PSC, Adoyi Adoyi, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da wakilin jaridar Punch a yau Alhamis.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun saɓani tsakanin ma’aikatan hukumar da shugaban hukumar, Musiliu Smith da babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Baba, kan hukumar da ya kamata ta ɗauki nauyin ɗaukar ma’aikatan ƴan sanda, karin girma da kuma naɗa ƴan sanda da jami’ai.

Ya yi nuni da cewa, IGP da sauran shugabannin ‘yan sanda tare da shugaban hukumar ta PSC, sun yi watsi da aikin da tsarin mulki ya ba hukumar.

Adoyi ya kara da cewa IGP ya dauki alhakin gudanar da ayyukan hukumar ta PSC ba tare da mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya ba, hukuncin kotun daukaka kara da kuma mahukuntan hukumar ta PSC.

Adoyi ya ce, “za mu fara yajin aikin ne na sai-baba-ta-gani daga ranar Litinin, 29 ga watan Agusta, domin nuna rashin gamsuwa da yadda PSC ke tafiyar da shugabancin hukumar, da kuma rashin mutunta kundin tsarin mulki, kotun shari’a. da PSC na IGP, Usman Baba.

“Ayyukan PSC sun bayyana a cikin kundin tsarin mulki, amma IGP ya yi watsi da duk wadannan, kuma ya karbi aikin hukumar. Yana nadawa da kuma daukaka kara yadda ya ga dama sabanin abin da kundin tsarin mulki ya bayyana.

“Kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, nadi, karin girma, da daukar jami’an ‘yan sanda da ‘yan sanda aiki ne na PSC, ba IGP ba.”