Home Labarai Ma’aikatan jinya sama da dubu 42 ne su ka bar Nijeriya a shekara uku — Gwamnati

Ma’aikatan jinya sama da dubu 42 ne su ka bar Nijeriya a shekara uku — Gwamnati

0
Ma’aikatan jinya sama da dubu 42 ne su ka bar Nijeriya a shekara uku — Gwamnati

Farfesa Faruk Abubakar, Rijistaran kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, ya ce sama da ma’aikatan jinya dubu 42 ne suka bar kasar a cikin shekaru uku da suka gabata.

Abubakar ya nuna damuwarsa kan wannan lamari, inda ya jaddada muhimmiyar rawar da ma’aikatan jinya ke takawa a fannin kiwon lafiya.

Da ya ke zantawa da gidan Talabijin na Channels TV a yau Talata, Abubakar ya ce, “Bari in bayyana a yau, a cikin shekaru uku da suka gabata, sama da ma’aikatan jinya 42,000 ne suka bar kasar nan kuma kasar na bukatar su.

“Manufofin gwamnati musamman ajandar Renew Hope na yanzu, tsare-tsare da yawa suna tafe, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta fito da tsare-tsare masu yawa inda za a inganta tsarin kiwon lafiyar Najeriya.

“Yanzu idan muka kyale kowane dan Najeriya ya tafi a matsayinsa na wadanda suka kammala karatun digiri, su waye za su gudanar da ayyukanmu na kiwon lafiya? Wanene zai ba da waɗannan ayyuka? Mu ’yan Najeriya ne kuma alhakinmu ne ga waɗannan ayyuka.

“Don haka ba ma adawa da kowa mai tafiya amma dole ne a yi wa ‘yan Najeriya hidima kuma dole ne a samar musu da wadannan ingantattun aiyuka na kiwon lafiya tunda muna samar da kwararrun ma’aikatan jinya da ke aiki a ko’ina a duniya.

“A bara kadai sama da 15,000 suka rage, adadin yana karuwa kowace shekara,” in ji shi