Home Kasuwanci Air Peace ya dakatar da jigila zuwa UAE don ramuwa kan dakatar da biza da Dubai ta yi wa ƴan Nijeriya

Air Peace ya dakatar da jigila zuwa UAE don ramuwa kan dakatar da biza da Dubai ta yi wa ƴan Nijeriya

0
Air Peace ya dakatar da jigila zuwa UAE don ramuwa kan dakatar da biza da Dubai ta yi wa ƴan Nijeriya

Sakamakon dena baiwa ƴan Nijeriya bizar da gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi, kamfanin jirgin sama na Air Peace ya bayyana cewa zai dakatar da ayyukansa zuwa Dubai daga ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba har sai baba-ta-gani.

A cikin sanarwar, Air Peace ya ce: “Hakan ya biyo bayan ci gaba da rashin ba matafiya na Nijeriya bizar da gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ke yi da kuma matsalolin da ke biyo baya”.

Kamfanin jirgin ya yi alkawarin samar da karin bayanai nan gaba.

A cewar kamfanin jirgin, “Air Peace ya kasance yana aiki a cikin Hadaddiyar Daular Larabawa duk da dokar hana tafiye-tafiye a kasar a baya-bayan nan, amma idan aka yi la’akari da matsalolin da matafiya Najeriya ke fuskanta wajen shiga kasar, ya zama wajibi mu dakatar da ayyukanmu zuwa wannan kasar”.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Air Peace ta bukaci fasinjojin da wannan ci gaban ya shafa da su tuntuɓe ta.