
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya barranta kansa da wata fatar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027 mai ɗauke da hoton sa da na Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna da ke yawo a ƙasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Eseme Eyiboh ya fitar a yau Laraba, Akpabio ya ce magauta ne suka fitar da fastar din domin su ɓatawa masoya shigavan ƙasa suna.
Akpabio ya ce bashi da wata niyyar tsaya wa takarar shugabancin kasa, ballantana ma ya tsaya tare da El-Rufai.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta fara bincike don bankaɗo waɗanda su ka kitsa wannan yarfen.