Home Kanun Labarai Akpabio na iya komawa APC kowanne lokaci daga yanzu

Akpabio na iya komawa APC kowanne lokaci daga yanzu

0
Akpabio na iya komawa APC kowanne lokaci daga yanzu

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa na jam’iyyar PDP Sanata Godswill Akpaabio tsohon Gwamnan jihar Akwa Ibom na iya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a kwanne lokaci daga yanzu a cewar wata majiya mai karfi daga jam’iyyar APC.

Jam’iyyar ta APC ce dai ta fara zawarcin Akpabio a lokacin da ake ta sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Ko a makon da ya gabata jam’iyyar PDP ta shirya wata liyafar cin abinci ga wadan da suka tsallako daga jam’iyyar APC zuwa PDP din, amma ba’a ga Sanata Akpabio ba a wajen taron, abinda yake kara nuna cewar yana shirin komawa APC ne.