Home Labarai Akwai makamai sama da miliyan uku a hannun masu laifi a Nijeriya — Ribadu

Akwai makamai sama da miliyan uku a hannun masu laifi a Nijeriya — Ribadu

0
Akwai makamai sama da miliyan uku a hannun masu laifi a Nijeriya — Ribadu

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Nuhu Ribadu ya ce akwai sama da makamai miliyan uku a hannun mutanen da ba su dace su mallaka ba a Nijeriya.

Ribadu ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a yayin taro a kan yaki da ta’addanci a kasashen Afrika, wanda aka bude a yau Litinin a Abuja.

Sai dai kuma Ribadu ya ce gwamnati ta dade tana toshe hanyoyin samun makamai, wanda hakan ya sa su ke yin wahalar samu a gurin masu aikata ta’addanci.

“Muna aiki kuma ina ganin mu na kokari,” in ji shi.

Ya bayyana cewa mace-macen da ke da alaka da ta’addanci ya ragu matuka a Najeriya daga kusan 2,600 a kowane wata zuwa kasa da 200 a halin yanzu.

Taron na da taken: ‘Karfafa hadin gwiwar yanki da gina cibiyoyi don magance ƙaruwar barazanar ta’addanci a Afirka.

Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro, ONSA, da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya na Yaki da Ta’addanci ne suka shirya taron.

NSA ta ce, ya zuwa yanzu, kokarin yaki da ta’addanci da gwamnati mai ci ke yi na samun sakamako mai kyau, inda aka samu karancin mutuwar ta’addanci a sassan kasar.