Home Labarai Da alama ECOWAS za ta janye takunkumin da ta sanya wa Nijar, Mali da Burkina Faso

Da alama ECOWAS za ta janye takunkumin da ta sanya wa Nijar, Mali da Burkina Faso

0
Da alama ECOWAS za ta janye takunkumin da ta sanya wa Nijar, Mali da Burkina Faso

Alamu masu karfi na nuni da cewa kungiyar raya ƙasashen Afirka ta yamma, ECOWAS za ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba wa Burkina Faso, Mali da Nijar biyo bayan juyin mulki da aka yi a kasashen uku.

Wasu majiyoyi da dama sun shaida wa Daily Trust a jiya Alhamis cewa, an dauki wannan matakin ne domin daƙile kasashen uku daga cimma burinsu na ficewa daga ECOWAS.

A tuna cewa ministocin kasashen Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar a ranar Alhamis 15 ga watan Fabrairu su ka bayyana shirin kafa tasu kungiyar tarayyar bayan da suka sanar da ficewarsu daga kungiyar ECOWAS- kungiyar da shugaba Bola Tinubu ke jagoranta.

A ranar Laraba kuma, sai tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, ya yi kira ga kungiyar ECOWAS da ta ɗage dukkan takunkumin da ta ƙaƙaba wa kasashen uku.

Daily Trust ta tattaro cewa, kiran da Gowon ya yi ga gwamnatin Najeriya ne ya jawo ECOWAS ta ɗauki matakin janye takunkumin a yunkurinta na dawo da kasashen uku cikin kungiyar.

Majiyar ta ce za a dage takunkumin ne a babban taron kasashen yankin da za a yi a gove Asabar, a wani bangare na kokarin dawo da ƙasashen uku cikin ECOWAS.