
A jiya Laraba ne dai Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kaduna, Salisu Abubakar Tureta, ya yi tayin biyan sadaki Naira dubu 100 don taimaka wa wani matashi, Salisu Salele ya auri rabin ransa, Bilkisu Lawal.
Alƙalin ha ce wa Salele ya je ya yi tunani a kan tayin da aka yi masa, ya kuma shaida wa kotu shawarar da ya yanke a ranar 6 ga Satumba, ranar da aka dage ci gaba da sauraron kararsa.
Tun da fari, mahaifiyar Bilikisu, Rayila Lawal ce ta maka Salele a gaban kotu, inda ta bukaci ta tilasta masa ya auri ƴarta idan da gaske yana sonta ko kuma ya rabu da ita idan bai shirya yin aure ba.
“Muna zaune a unguwa ɗaya kuma yana zuwa zance wajen ƴa ta ba tare da izinin mu a matsayin iyayenta ba.
“Na shaida wa mahaifiyarsa halin da ake ciki kuma ta ce ɗanta bai shirya yin aure ba.
“Daga nan sai Salele ya canza dabara kuma ya daina zuwa gida zance, sai dai ya canja dabara, inda ya ci gaba da kiran ta a waya, sai su haɗu a wani waje su yi zance.
“Ba na son ya ɓata tarbiyyar da na yi wa ƴa ta tsawon shekaru, don haka na yanke shawarar kawo shi kotu,” in ji Rayla.
Ta nanata cewa a shirye ta ke ta aurar da ‘yarta ga Salele idan har ya shirya.
Da yake kare kansa, Salele ya ce yana son yarinyar amma bai shirya yin aure ba sai bayan shekara biyu.
“Ni dalibi ne da nake karatu a daya daga cikin jami’o’in tarayya kuma ba zan so aure ya dauke min hankali ba.
“Bayan haka, ba ni da sadaki kuma har yanzu a gaban iyayena na ke,” Salele ya shaida wa kotu.