
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya sanar da bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 ga ƴan kasuwar Kantin Kwari da ke jihar Kano, wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.
Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa kaya da darajarsu ta kai na miliyoyin naira sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa kasuwar a makon jiya.
Abubakar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne a wani gagarumin liyafar da Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a jam’iyyar, Ibrahim Shekarau ya yi a Kano ranar Litinin.
A cikin gajeren jawabinsa, Atiku ya jajanta wa ‘yan kasuwar da abin ya shafa kafin ya bayyana tallafin.
“Tunani da addu’o’i na tare da ƴan kasuwar Kantin Kwari, mun ji irin bala’in da ya afka wa kasuwar ku. Ba wai gangamin neman zaɓe ne ya kawo ni Kano ba, na zo ne tarbi ɗan uwa na Shekarau zuwa PDP
“A gaskiya mun tausaya muku, don haka nake sanar da tallafin Naira miliyan 50 a gare ku,” in ji Abubakar.