Categories
Taska

An bawa karuwai mako biyu da su tattara komatsansu su fice daga Abuja

Majalisar Mulki Ta Birnin Tarayya, Abuja (FCTA), ta umarci kafanin mata masu zaman kansu da ke kasa kawunansu akan titunan birnin da su tattara ya nasu ya nasu su fice daga cikin garin na Abuja cikin makonni biyu ko kuma su gamu da fushin hukuma

Umar Shu’aibu, wanda shi ne kodinata na alkinta birnin Abuja ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau a ofishinsa a nan Abujan.

Ya ce hukumar da ya ke jagoranta da taimakon hukumar ci gaban garin Abuja (SDS) da kuma taimakon jami’an tsaro ne za su aiki kafada da kafada wajen ganin sun kori karuwai daga cikin garin Abuja cikin makonni biyu masu zuwa.

Umar Shu’aibu ya koka kan yadda karuwai ke nema su mamaye titinan birnin Abuja musamman da yamma zuwa cikin dare, inda ya bayyana cewa za su fara aikinsu da wayar da kai, kuma wannan zai dauki makonni biyu suna yi, inda daga bisani kuma za a shiga kame a kowane layi da sakon Abuja.

Har ila yau, Umar Shu’aibu ya ce, hukumarsa za ta farwa mutanen da suka kafa tamfurare na katako ko na karfe, inda hukumar za ta rushe duk wani gini ko tamfurare da aka kafa ko gina a kwaryar birnin Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *