Wani katafaren allon Shugba Buhari da aka yayyage a jihar Kano

Wasu fusatattun matasa a jihar Kano sun farwa allunan tallan Shugaba Buhari da Gwamnatin Kanon ta sassaka a waje da dama a cikin birnin Kano a fuskantar barazanar cirewa sakamakon kin zuwa kano da Shugaba Buhari yayi a yau litinin.

Kusan Mako biyu da suka gabata akai ta yayata sanarwa a gidajen Radiyo a jihar Kano cewar mutane su fito su yi turururwa domin yin adabo da Shugaba Muhammadu Buhari a yau litinin, sakamakon wata ziyarar aiki da ake jin cewar zai kawo Kano.

Ana zaton zuwan na Shugaba Buhari zai kaddamar da wasu asibitoci guda biyu wanda aka gina su tun zamanin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau kuma Gwamna Ganduje yayi musu fenti tare da sanya gadaje, da kuma aikin titin Panshekara.

Wadannan na daga cikin ayyukan da ake tunanin Shugaba Buhari zai kaddamar in ya zo Kano din. Amma dai tun a jiya Lahadi sanarwa ta fara bazuwa a jihar ta Kano cewar Shugaba Buhari ya soke zuwansa jihar Kano.

Daman dai akwai jikakkiya tsakanin tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso wanda Sanata ne a yanzu mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa ta kasa, da kuma Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje, wanda aka jima da sanya zare tsakanin juna.

Masu fashin baki na ganin rashin samun wannan halartar ziyara da Buhari yayi a jihar Kanon na da nasaba da rikicin da ke tsakanin Kwankwaso da Ganduje a cewar wani mai sharhi kan siyasa a jihar Kano Malam Bello Muhammad Sharada,

1 COMMENT

  1. Comment: BUHARI KANO YAKE MULKA KO NAJERIYA BAKI DAYA?

    Ai ni dan Buhari baije Kano banga laifin shi ba, Nijeriyar nan fa nada fadi, kuma ba Nijeriya yake mulka ba to me yasa za’ace dole sai Buhari yaje da kanshi Kano bayan zai iya tura wakilai ammafa idan za’ayi mashi adalci, zuwan shi Kano a wannan yanayi zai iya kawo tarzoma da kuma cece kuce a Gwamnatin jihar Kano, kuma wadanda suka cire wadannan hotuna sun cire sune da wata manufa bawai dan kawai rashin zuwansa Kano ba.

    Mu muna bayan Buhari kuma muna tare dashi