Home Labarai Ƙanin Kwankwaso, Inuwa ya rasu

Ƙanin Kwankwaso, Inuwa ya rasu

0
Ƙanin Kwankwaso, Inuwa ya rasu

 

Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso, ƙani ga tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya rasu.

Marigayi Inuwa ya rasu a yau Litinin a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano.

Rahotanni sun baiyana cewa marigayin ya rasu ya na da shekaru 64 bayan ya sha fama da doguwar jinya.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa za a yi jana’izar marigayin, wanda shi yanke bin Sanata Kwankwaso a gidan su da ke Ƙaramar Hukumar Madobi da misalin 4:00 na yamma.