34.1 C
Abuja
Saturday, April 1, 2023

Ƴansanda sun cafke masu rajin samar da ƙasar yarabawa a Legas

Must read

Rundunar ƴansanda a jihar Legas ta cafke wasu ƴan kungiyar da ke rajin samar da ƙasar Yarabawa da ke shirin gudanar da zanga-zanga a yankin Alausa na jihar.

Kakakin rundunar ƴansandan, SP Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi a sahihin shafin sa na Twitter.

Ya ce, “Da safiyar yau ne wasu masu rajin samar da kasar Yarbawa su ka fara kafa sansani a Alausa, inda su ka shirya yin amfani da su a matsayin sansanin kaddamar da gagarumar zanga-zanga.

“Ba tare da bata lokaci ba aka kori sansanin yayin da aka kama wasu da ga cikin su. Ana ci gaba da bincike a Sashen Binciken Laifukan Jiha (SCID).”

A cewar sa, ba za lamunci rashin bin doka da oda ba a jihar.

“ Zanga-zangar da ta fara da wannan tsari, a Legas, a ko da yaushe kan yi girma zuwa take hakkin wasu, lalata dukiyoyi da jefa al’umma a cikin mawuyacin hali.

“A rundunar ƴansandan jihar Legas, mun sanya kididdigar laifuka don amfani da su,” in ji Hundeyin.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article

- Website Designed By DEBORIAN.COM, a Nigerian Web Designer and Web Developer -