
Rundunar Ƴansanda a jihar Katsina ta tabbatar da sakin yara 30 da ƴan bindiga suka sace a jihar.
An sace yaran ne a jiya litinin a lokacin da su ka je yin itace a kauyen Kasai da ke karamar hukumar Batsari a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadiq, ya tabbatar wa wakilinmu DAILY NIGERIAN sakin yaran.
Sai dai ya ce an kubutar da dukkan wadanda harin ya rutsa da su tare da mika su ga iyayen su.
“ Gaskiya ne. Yaran sun je yin itace ne a lokacin da ‘yan bindigar suka kama su.
“Amma da jin labarin, sai muka shiga aikin ceto, kuma alhamdulilah, an kubutar da su kuma an mika su ga iyayen su,” in ji Mista Abubakar.