
Jam’iyyar APC, reshen jihar Kaduna, ta dakatar da shugabar matan jam’iyyar ta jihar saboda goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai kan sabon rikicin da ya ɓarke bisa ikirarin tarin bashi da ake bin jihar.
DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Gwamna Uba Sani a ranar Juma’a ya koka da dimbin bashin da ya gada daga magabacin sa, Nasir El-Rufai.
Da yake jawabi a wani taro na masu ruwa da tsaki a jiya Asabar, Sani ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin dala miliyan 587, da Naira biliyan 85, da kuma bashin kwangila guda 115 daga gwamnatin El-Rufai.
Sai dai shugabar matan jam’iyyar APC a jihar ba ta ji dadin kalaman gwamnan ba, inda ta ce gwamnan yayi butulci duba da cewa El-Rufai ne ya tsaya tsayin daka don tabbatar da nasarar sa a lokacin zabe.
“Idan ka ce babu kudi a jihar Kaduna me ya sa ba za ka yi murabus ba? Duk da dimbin bashin da ake bin sa, haka ya tsaya tsayin daka yana kokarin tabbatar da tikitin takarar ka ta gwamna na jam’iyyar daga hannun Mallam [El-Rufai].
“Wannan lamari ne a fili na cin amana. Mallam yayi komai domin Uba ya zama sanata kuma daga baya gwamna,” in ji ta
Sai dai jam’iyyar APC a wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na jihar Ali Maishago da kuma Zakka Bassahuwa, jam’iyyar ta dakatar da shugabar matar ne saboda zargin ɓata sunan gwamnan.
Wasikar na cewa: “Kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na yankin Badarawa/Malali bayan nazari da duba kan faifan bidiyo na da aka fitar a ranar 30 ga Maris, 2024 ta shafukan sada zumunta; Facebook, Whatsapp, da Tiktok wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar mu ta APC kamar yadda ya zo a cikin sashe na 21.2 (v).
“Saboda abubuwan da ke sama, wannan babban laifi ne da hukuncin sa shi ne dakatar wa,”