
Jam’iyyar APC reshen jihar Rivers ta bukaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike da ya koma jam’iyyar a jihar.
Shugaban kwamitin riko, Tony Okocha ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fatakwal, dangane da ficewar ƴan majalisar 27 da suka koma jam’iyyar daga PDP.
Okocha, wanda kuma shi ne wakilin jihar a hukumar raya Neja-Delta, NDDC, ya bayyana farin cikinsa kan matakin da masu sauya shekar suka dauka.
Ya ce wadanda suka sauya shekar ne suka sanar da jam’iyyar a hukumance, lamarin da ya sa suka sauya sheka, kuma gaskiya ne ba jita-jita ba.
Mista Okocha ya yabawa ƴan majalisar kan matakin da suka dauka na sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, inda ya ce ba za a iya kwatanta sauran ‘yan majalisar guda hudu da ‘yan majalisar 27 ba.
A kan ko dalilin sauya shekar an yi shi ne don sharewa Wike hanya zuwa APC, Okocha ya ce, “Bana jin haka.
‘’Wike dan siyasa ne da sunansa ya yi amo a cikin al’umma; don haka babu wanda zai iya tunani ko ya ce masa idan zai koma APC ko a’a.’’