
Bayan kusan kwanaki 5 a na ta faman nema, a ƙarshe dai an gano ragowar gawwaki sha uku na mutanen da su ka rasu a haɗarin kwale-kwale da ya faru a garin Badau, Ƙaramar Hukumar Ɓagwai, Jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa dukkan mutum sha ukun sun rasu, inda adadin waɗanda su ka rasa rayuka a haɗarin ya kai mutane 42.
A halin yanzu dai gwamnatin Kano ta kafa kwamiti domin bincikar yadda lamarin ya faru, inda ta bayar da motoci 2 a riƙa safarar mutane bayan ta hana yin fito a garin.
Sannan gwamnatin ta bada tallafin abinci da na kuɗi ga iyalan waɗanda abin ya shafa.