
Wasu ƙungiyoyin jihohin Arewacin Najeriya 19 sun barranta kansu daga shiga zanga-zangar da aka tsara farawa daga gobe Alhamis, 1 ga watan Agusta.
Yahaya Usman( Siyasar Yanci) (Politics of Freedom), Aliyu Abdulmalik, Agaie Emirate Consultative Forum, Saidu Alfa, National Coordinator, Yan-Almajiri Endowment, Mohammed Saidu Etsu, National Coordinator, Youth Lead Nigeria, and Abubakar M. B. Kutigi, National Coordinator, Niger Progressive Forum ne sunka sanya hannu a takardar jawabin taron.
Da suke jawabi ga manema labarai a garin Minna a yau Laraba, kungiyoyin sun ce sun janye zanga zangar ne bayan gwamnatin tarayya tayi tayin tattaunawa.
Da yake jawabi a madadin shugabannin kungiyoyin, Yahya Usman na kungiyar siyasar Yanci ya ce alamu sun nuna zanga zanga-zangar da aka shirya ba ta lumana bace.
Acewarsa, gwamnati na aiwatar da wasu daga cikin bukatun masu zanga-zangar zangar ta hanyar shirye shiryenta.
“Matakan da gwamnati ta dauka sun yi nisa wadanda suka hada da bai wa kananan hukumomi yanci da bashin karatu dalibai da sanya hannu kan dokar mafi karancin albashi da siyar da shinkafa kan Naira dubu 40 kowanne buhu da sauransu”.
Kungiyoyin sun yi kira ga kungiyoyi da daidaikun mutane da su amshi tayin gwamnati na tattaunawa.
“Mun ga yadda daga karshen yakin Basasa aka zo aka tattauna. Mun ga yadda zanga zangar mata ta Aba ta kasance. Haka ma abinda ya faru a June 12. Don haka wannan ma tattaunawa ce mafita”.
Yahaya Usman ya kuma baiyana cewa za su aika wa gwamnatin taraiya takardar amsa kiran ta na sasantawa da ƙungiyoyin da su ka shirya zanga-zangar.