
Ƙasa ta ruftawa mutum 2 sun rasu a Kano
Mutum biyu ne suka mutu sakamakon ruftawar da kasa ta yi a kansu, a garin Bichi da ke Jihar Kano a arewacin Najeriya.
Rahotonni sun ce mutanen suna cikin wani rami ne inda suke tonon dutse lokacin da kasar da rufta kansu.
BBC ta rawaito cewa Jami’an ‘yan sanda sun dauki gawarwakin zuwa babban asibitin Bichi.
A watan Maris din da ya gabata, an samu makamancin wannan lamari inda abokai hudu suka mutu lokacin da suke tonon kasar da za su yi wa abokinsu da zai yi aure daki.