Home Labarai Ɗan ƙasar Syria da ya je Umrah a keke ya rasu a Makkah

Ɗan ƙasar Syria da ya je Umrah a keke ya rasu a Makkah

0
Ɗan ƙasar Syria da ya je Umrah a keke ya rasu a Makkah

Wani Alhaji ɗan ƙasar Syria mai suna Ghazi Shehadeh wanda yaje ƙasar Saudi Arabia a kan Keke daga kasar Jamus domin ya yi ibadar Umrah ya rasu.

Shafin kasar Saudia na Facebook mai suba Life in Saudi ya rawaito cewa Shehadeh ya rasu ne a garin Makkah.

An yi jana’izarsa a Masallacin Harami kuma an binne shi a makabartar Mualla kamar yadda shafin ya rawaito.

Mamacin ya wallafa duk abin da ya shafi tafiyar tasa a shafukan sada zumunta kafin rasuwar tasa.

“Wani Alhaji ɗan kasar Syria, Ghazi Shehadeh wanda ya tawo daga ƙasar Jamus a Keke zuwa Masallacin Ka’aba kuma ya wallafa duk abinda ya shafi tafiyar tasa a shafukan sada zumunta.

Ya rasu a wajen Makkah. An yi jana’izarsa a Masallacin Harami kuma an binne shi a makabartar Muallah”.