21.1 C
Abuja
Tuesday, February 7, 2023

ASUU ta umarci malaman jami’a da su gaggauta dawo wa aiki

Must read

 

 

 

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU, ta umarci mambobinta da su ci gaba da duk ayyukan da su ka tsagaita yi sakamakon yajin aiki daga karfe 12:01 na ranar yau Juma’a.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a karshen taron gaggawa na kungiyar ta kasa, NEC, a yau Juma’a a Abuja.

Osodeke ya ce an kira taron ne domin a duba abubuwan da ke faruwa tun bayan da kungiyar ta ayyana yajin aiki na sai-baba-ta-gani a ranar 29 ga watan Agusta.

Ya kuma ce, domin kauce wa shakku, batutuwan sun hada da bayar da kudade don inganta ilimin jami’o’in gwamnati, biyan alawus-alawus na ilimi, ƙara yawan Jami’o’in gwamnati, kafa kwamitin malaman wucin-gadi da kuma tabbatar da takardar yarjejeniya .

Ya kara da cewa sauran su ne tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta UTAS a matsayin babbar manhaja don dakatar da almundahana da samar da wata hanyar biyan kudi a tsarin jami’a da kuma sake yin shawarwari na yarjejeniyar 2009.

A cewar shugaban ASUU, NEC ta lura da takaicin cewa har yanzu ba a magance matsalolin da ake tafkawa ba.

“Duk da haka, a matsayin kungiyar masu bin doka da oda da kuma yin biyayya ga kararrakin da shugaban kasa ya yi da kuma amincewa da kokarin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa.

“ASUU NEC ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin da ta fara a ranar 14 ga watan Fabrairu.

“Saboda haka, an umurci dukkan mambobin kungiyar ASUU da su ci gaba da duk ayyukan da aka janye daga karfe 12:01 na ranar Juma’a, 14 ga Oktoba,” inji shi.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article

- Website Designed By DEBORIAN.COM, a Nigerian Web Designer and Web Developer -