Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar

An bayyana tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da ya yiwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP kome, cewar shi ne kadai mutumin da zai iya samun galaba kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari idan aka shiga zaben 2019.

“Gazawar wannan Gwamnatin ta Shugaba Buhari wajen cika alkawuran da ta daukarwa ‘yan Najeriya, ya sanya mutane da yawa suka dawo daga rakiyar ta. Dan haka, wannan ne ke kara tabbatar da damar da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar yake da ita ta samun nasara”

“Idan Atiku ABubakar ya tsaya yayi shiri sosai akan wannan zaben, ba ni da wata shakkar cewar zai kayar da Shugaba Buhari a zaben 2019 dake tafe. Babu wani mutum a PDP da zai iya karawa da Buhari kuma yayi nasara in ba Atiku Abubakar ba” Inji Abbati Bako.

Abbati Bako, ya kara da cewar, irin wannan yunkuri da mutane irinsu Atiku Abubakar suke yi na kalubalantar jam’iyya mai mulki a zaben 2019,shi ne zai sanya su farga domin su an cewar Annabi ya faku.

Da yake maida jawabi kan kalaman Gwamnan jihar kaduna, Malam Nasiru el-Rufai, Abbati Bako ya bayyana cewar abinda gwamnan yayi mummunar katobara ce da bai kamata mutum irinsa yayi ba.

“Ba zai taba yuwuwa ba, ka kalli mutum kamar Atiku Abubakar kace ya tafi Allah ya raka taki gona. Abin kaico ne Gwamna ya bayyana hakan. Siyasa batu ne na tattaunawa da sahalewa juna, a lokacin da aka tattauna, aka barwa Atiku Abubakar, a wannan lokacin kuma su el-Rufai zasu ji bakar kunya sosai”

Abbati Bako kwararren dan sisaya ne, da yake fashin bakin kan siyasar najeriya da ma sauran duniya baki daya.