Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP ya nemi Tsohon Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da ya taimaka ya janye masa takara a wannan zaben na 2019.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a Sakatariyar jam’iyyar PDP dake birnin Dutse lokacin da ya kai ziyarar neman goyon bayan wakilan jam’iyyar da zasu yi zaben fidda gwani.

”Na girmi Sule Lamido dan haka ya dace ya janye takararsa ya kyale ni domin na gwada sa’ata a wannan karon” A cewar Atiku Abubakar