Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar

Wasu tabbatattun majiyoyi sun tabbatar da kammala dukkan wasu shirye shirye na sauya shekar tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar daga jam’iyyar APC zuwa PDP a ranar asabar din nan mai zuwa.

Ana sa ran, Atiku Abubakar zai yanki katin jam’iyyar PDP a mazabarsa dake Jada a jihar Adamawa, lamarin da zai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki. Ana kuma sa ran tsohon mataimaakin shugabankasar zai halarci babban taaron PDP da za’a zabi sabbin shugabanni.

Ba wannan ne karon farko da Atiku zai sauya sheka zuwa PDP ba, ko a baya ma, Atiku ya taba ficewa daga PDP inda ya kafa jam’iyyar AC, kuma yayi mata takarar Shugaban kasa, yayin da daga bisani ya sake komawa jam’iyyar PDP a lokacin.

Bayan haka kuma, Atiku Abubakar ya jagoranci wasu Gwamnoni da suka tayar da kayar baya a PDP, inda suka kafa sabuwar PDP, kafin daga bisani su tsunduma hadakar da ta samar da sabuwar jam’iyyar APC wadda Atikun yayi mata takarar Shugaban kasa.

Tuni damanake ta rade radin cewar Atiku zai sallama jam’iyyarsa ta APC dan komawa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP, wadda ake ganin yana iya zamar mata dan takarar Shugaban kasa a zaben 2019 mai zuwa.

Ana saran Atiku Abubakar zai isa birnin Yola a ranar Asabar, domin bayyana komawarsa jam’iyyar PDP, wadda yayi mata mataimakin Shugabana kasa daga 1999 har zuwa 2007, inda suka samu sabani da tsohon maigidansa, Olushegun Obasanjo.

Ko me zaku ce kan wannan batu?